Sunday, 7 January 2018

AMFANIN TURAKAR YANAR GIZO (BLOGGING)

Amfanin Turakar yanar Gizo (Blog)
Sadiqtukur Gwarzo
 - 5/16/12 to leadershiphausa
 Assalamu alaikum. Turakar yanar gizo mai suna web-log, ana kiranta da blog a taqaice, kamar ma'ajiya ce da ake taskance bayanai a yanar gizo, sai dai kuma tasha bambam da dandali dake yanar gizo wato website, haka kuma tasha bambam da zaurukan dake yanar gizo wadanda ake kira (discussion group/forum). Wannan turakar ta blog tana da matuqar amfani ga al'umma dake ta faman bincike a yanar gizo dare da rana, asalima blog shine sirrin bunqasuwar yanar gizo a yanzu. Mafiya yawan mutanen da suke samun kudi a yanar gizo zaka same su suna da blog, wato suna qirqirar turaka da suke sanar da jama'a ko koyawa jama'a wani ilimi wanda mutane ke qaruwa da turakar, don haka yawan qaruwar mutane da wannan ilimin a wannan turakar, yawan kudin shigar da mai turakar yake samu, kamar dai yadda nasha fadawa mutane masu son samun kudi a yanar gizo cewa ba'a samun kudi a yanar gizo da jahilci, ko da ragwanci! AMFANIN TURAKAR YANAR GIZ 1. Yada ilimi Mutane da yawa suna yin mamakin yadda duk wata tambaya da kayi a harshen turanci ko larabci a shafin search engine kamar google dake yanar gizo zaka samu cikakkiyar amsarta ko kuma kwatan-kwacin amsar tata. Wannan duk yana faruwa ne ta dalilin blog. Mutane iri na irin ku masu karatu ke rubuta irin wadancan abubuwan ta sigar blog suna liqawa a yanar gizo, wannan ne dalilin da yasa a cikin matsalolin yanar gizo (internet disadvantages) ake saka rashin ingancin bayanai a yanar gizo. Don haka turakar yanar gizo waje ne da ake yada ilimi, waje ne da masana tarihi ke taskance tarihi don masu nema. 2. HASKAR KASUWANCI Yan kusuwa na amfani da turakar yanar gizo don sauraren ra'ayoyin abokan huddar su tare da sanar dasu manyan labarai da suka shafi kayayyaki da aiyukan yan kasuwar. Haka kuma ta hanyar blog, yan kasuwa da dama ke tallata hajarsu ta hanyar bayar da bayani daya shafi kayan da suke sayarwa tare da bayar da adireshin website da za'a iya samun cikakken bayani. 3. SAMUN KUDI Mutane masu himmar yada ilimi ga al'umma sunfi kowa qirqirar turaka a yanar gizo, don haka mutane da yawa sukan so ziyartar turakar wadannan mutane don qaruwa da ilimi,wannan kesa masu blog ke amso tallace-tallace irin ta adsence, wadda duk wanda ya ziyarci shafin turakar indai ya latsa (click) akan tallar zai samu lada, wato dai abinda ake kira (pay-par click). Wani abin ban sha'awa kuma ga turaka shine, akwai wajen sauraron ra'ayoyin masu karatu (comments), ta hanyar nan mai turakar zai gane amfanin rubutunsa ga jama'a domin wasu zasuyi masa godiya, wasu kuma zasu iya nuna kuskuren da akayi a rubutun ko kuma rashin jin dadinsu game da rubutun. YADDA AKE QIRQIRAR BLOG. Qirqirar blog hanya ce mafi sauqi ba kamar website ba. Domin blog kyauta ne, website kuwa kowa ya sani akwai caji da akeyi kafin a kafa da bayan an kafa. Kawai dai abu mai wahalarwa wajen kafa blog bazasu wuce 3 ba, na daya mutum ya mallaki abinda zai rubutawa jama'a mai inganci kuma wanda zai amfanawa jama'a, na biyu mutum ya mallaki email addres, na uku kuma mutum ya zabawa turakar sa suna mafi dacewa wanda kuma babu wata turaka mai irin sunan. ga adiresoshin shafukan da za'a iya bude turaka a kyauta sune: www.wordpress.com da www.blogger.com (blogger.com basa amsar kowanne email addres illa gmail wanda za'a iya budewa ta wannan adireshin www.gmail.com). Da zarar mutum ya ziyarci daya daga wadannan adiresoshi, zai ga inda atja sa 'sign up' ko 'create blog', sai a latsa tare da cike fam din da zasu bayar. QALUBALEN HAUSAWA A GAME DA KAFA TURAKAR YANAR GIZO. A zahiri, ya kamata yan uwa hausawa su maida hankali wajen kafa turakar yanar gizo da harshen hausa, amfanin hakan bazai misaltu. wajen kafawar kuwa, duk abinda mutum yasan yanatda ilimi akansa koda labarai ne, wataqila anan gaba lokaci zaizo wanda mutanen lokacin zasu so jin yadda muka gudanar da rayuwar mu, kamar yadda wasun mu ke takaicin rashin ingantattun bayanai akan yadda hausawan da suka gabace mu suka kasance. Wannan zaisa nan gaba hausawan mu zasu rinqa binciken ilimi a yanar gizo cikin hausa ya zamo mai sauqi ba tare da wahalarwa ba, wataqila ma nan gaba marubutan mu zasu huta da kai littattafan su kasuwanni, maimakon haka sai dai marubuci ya rubuta littafi, ya sanya shi a yanar gizo hausawa su siya. Daga Sadiq Tukur Gwarz 08060869978.

1 comment:

  1. Mun gode da waxannan bayanai domin sun taiamaka wajen ankarar da mu muhimmancin blogs.

    ReplyDelete