Wednesday, 10 January 2018

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 8

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na takwas.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.


SARAUTAR SARKIN MUSULMI ATTAHIRU DAN AHMADU DAN ABUBAKAR ATIKU

  Anyi masa mubaya'a mulki a wurno gidan waziri Buhari. Daga nan ya taso zuwa sokoto da zama. Acan ne Sarkin kano Alu Babba yazo gareshi yayi masa mubaya'a tare da jaddada tubansa bayan karewar Basasar kano da rasuwar sarkin kano Tukur.
   Sarkin Musulmi Attahiru ya yafe masa, ya kuma aura masa 'yarsa, sannan ya ɗauki hanyar komawa gida.
   Akan hanyarsa ne ya sauka a Gadi ta kasar zamfara. Da yammaci sai kuwa ga matarsa a sukwane tazo gareshi daga kano. Anan take sanar masa cewar turawa sun kwace kano. Don haka sai tsoro ya kamashi, ya sulale da dare ya gudu ba tare da jarumansa sun sani ba.
   Da gari ya waye jaruman Sarki Alu suka nemeshi baya nan, sai wazirinsa Ahmadu yayi musu jagora suka sukwano da nufin dawowa kano. Amma kafin su iso sai suka haɗu da turawa, suka gwabza yaki, waziri Ahmadu yayi shahada, saura suka tarwatse.
   Anan kuma sai Wambai Abbas yaja ragowar tawaga da suka tarwatse suka tafi kano tare da yiwa turawan cikinta mubaya'a, har kuma daga baya suka naɗa shi Sarkin kano.
   Sa'ar da labari yazo sokoto cewar turawa na zuwa daga kano, sai aka shiga shawarwarin abin yi. Wasu suka ce ayi tattalin yaki dasu. Wasu sukace a nemi sulhu dasu. Wasu kuwa sukace sai ayi hijira tun kafin su iso.
   Sarkin musulmi Abdurrahman kuwa sai ya karkata akan ayi hijira. Daga nan mutane suka shiga tattalin kayayyaki. Aka shiga siyen takalma, alfadarai, jakuna, rakuma da sauran kayayyaki domin yin hijira. Aka sanya ranar tashi.
  Ana cikin haka kwatsam sai ga labari cewar turawa na daf da sokoto. Sai kuwa niyyar hijira ta warware, aka shiga shirin yaki dasu.
   Sarkin musulmi ya fita bayan gari ranar wata jumu'a ya kafa sansani, ya aika da masu neman labari suje suyi Sharoro.
   A wannan yammaci masu sharoro suka gama hangawa suka dawo basu ga kowa ba. Wayewar garin asabar ma haka. Sai can da yammaci har nutane sun fara sakin jiki da zuwan turawa akaga kura ta turnuke, turawa suka harbo bindiga ta kashe mutane. Jama'ar sarkun musulmi ta kwana cikin shiri.
   Da wayewar garin Lahadi sai aka fita yaki. Aka soma fafatawa, amma cikin kankanin lokaci aka kashe mutanen sarkin musulmi masu yawa, wannan yasa yaja zuga ya gudu yabar sokoto, sannu a hankali har kasar Gombe inda Allah yayi masa rasuwa daga baya, bayan ya gwabza faɗa da turawa a wani wuri da ake kira 'Burmi.
  Dafatan Allah yajikamsa Amin.
   Bayan rasuwarsa, sai Sauran mutanen dake tare dashi suka rabu, wasu suka dawo sokoto, wasu kuma suka nausa izuwa gabas, suka sauka a wani wuri mai suna 'Shehu Talha', suka naɗa Muhammadu Bello ɗan marigayi sarkin da turawa suka kashe Attahiru a matsayin shugaba. Har yanzu kuma ɓurɓushin sa suna can garin.
   Amma da turawa da turawa suka tarwatsa tawagar yaki a sokoto, shima waziri Buhari sai yaja zuga yayi nasa wuri. Yaje wani kauye mai suna Dinawa kusa da wurno ya sauka.
   Babu jimawa sai turawa suka aiko masa da takarda cewar ya komo sokoto. Waziri Buhari yahau da mutanensa ya nufi sokoto. Ya iske turawa sunyi dandali a gabas da birnin sokoto. Ya aike musu gashi nan tafe, suka yi masa izinin shiga birni.
   Aikuwa koda mutane sukaji cewar waziri ya komo birni, sai waɗanda suka gudu sukayi ta dawowa.
   To daga nan sai turawa suka nemi shawarar wanda za'a naɗa sabon sarki..
  

No comments:

Post a Comment