Wednesday, 10 January 2018

SARAUTAR SOKOTO DA GWAGWARMAYAR MULKI 9

TARIHI: SARAUTAR SARAKUNAN MUSULUNCI DA GWAGWARMAYAR RIKON SARAUTA.

Kashi na tara.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.

SARAUTAR SARKIN MUSULMI ATTAHIRU NA BIYU DAN SARKIN MUSULMI ALIYU DAN MUHAMMADU BELLO.

  Daga karshe shawara ta cimmu, aka yiwa Attahiru jikan Muhammdu Bello sarauta.
  A shekarar farko turawa basu fara komai ba, suna ta neman haɗin kai daga jama'a.
   A farkon shekara ta biyu sai suka sanya wa jama'a Jangali. A karshenta kuma suka sanya haraji.
   A shekara ta uku ne fitinar Satiru ta taso.
   Abinda kuwa ya faru shine:-
Akwai wasu unguwanni a kudancin sokoto masu sunaye Boɗinga da Dange, ance sai wani mutum mai suna Danmakaho gaurin Kauyawa da wasunsa suka shiga tara mutane a garin Satiru, har sai da suka tara jama'a da yawa da nufin ɓallewa daga turawa.
   Farkon abinda suka fara shine yanka wuyan wani mutum mai suna Yahaya saboda yayi sallar idi ba tare dasu ba.
  Daga nan sai kisan wasu mazaje 13 da mace ɗaya a kauyen Tsomau gami da kone garin.
   Labari sai ya iske baturen mulki Mai Farin Kai (Mr. Burdon) lokacin kuwa yana shirin tafiya Dungurun ne. Don haka sai ya aiko da takarda ga turawan sokoto domin suyi bincike kafin ya dawo.
  Ana haka sai turawa uku da likita ɗaya suka taso izuwa satiru don ganewa idonsu abinda ke faruwa. Ai kuwa zuwansu keda wuya bayan sun zauna, sai mutanen Satiru suka hausu da sara da suka, sukayi gunduwa-gunduwa dasu, suka ɗauke bindigoginsu.
  Daga nan fa sai mutanen satiru suka soma girman kai da buwaya, suna bin garuruwan makwabta suna kara magoya baya da kisan duk wanda yaki musu biyayya.
  Bayan jimawa kaɗan Mr Burdin ya komo sokoto. Sarkin musulmi yaje ya gaisheshi, sannan ya tura takardu duk manyan sarakuna suzo sokoto irinsu Sarkin Tambuwal, Sarkin Mafara, sarkin Danko, sarkin 'Burmin Bakura, sarkin Gobir Isa, da sarakunan Zamfara.
   Bayan kwanaki sai Marafa ya nemi izini aka bashi, ya taho da runduna don murkushe mutanen satiru, amma akayi rashin nasara akan sa, mutanen satiru suka kara girman kai.
   Daga nan sai askarawan Turawa suka iso sokoto daga Kano, kwantagora, Dungurum da Lokoja. Aka haɗa runduna aka nufi satiru.
   Da turawa suka isa, sai suka girke kayan faɗansu. Mutanen satiru ma suka fito garesu suka jeru. Turawan nan kallon su kurum suke yi. Babu jimawa mutanen satiru suka nufo askawan turawa a sukwane.
  Sai da mutanen Satiru suka zo kusa, sai masu Igwa suka durkusa kan guiwowinsu, suka fara harbawa. Nan take hayaki ya turnuke sama, kafin kace haka gawarwakin mutanen satiru kurum ake gani a kasa hululu cikin jini.
  Wani sahun ya kara tasowa ga turawa, nan ma akayi masa kamar yadda akayiwa sahu na farko. Aikuwa babu jimawa sai ragowar suka arce.
  Bature  Mai Farin kai ya shiga garinsu, ya huta, sannan ya bada umarni a kone shi. Karshen wannan fitina kenan wadda ta ɗauki tsawon shekara ɗaya da kwana ashirin.
  A shekara ta huɗu da zuwan turawa suka tursasa sarakunansu bada 'ya'yansu a koyar dasu ilimin boko, a lokacin ma babu makaranta a sokoto.
 A shekara ta takwas kuma suka gina Baitul Mali.
   A karshe dai, Allah ya karɓi ran sarki Attahiru na biyu bayan ya shafe shekaru 12 da watanni 2 a mulki a shekarar 1915.
  Da fatan Allah yajikansa Amin.
Sauran Sarakunan da suka mulki sokoto bayansa sune:
-Muhammadu dan Ahmadu 1915-1924
Muhammadu dan Muhammadu 1924-1931
Hasan dan Mu'azu Ahmadu
1931- 1938
Siddiq Abubakar III
 1938- 1923
Ibrahim Dasuki
1923-1988
Muhammadu Maccido
1988- 2006
Sa'adu Abubakar
 2006-

Alhamdullahi. Karshe kenan!


No comments:

Post a Comment