TARIHIN KAFUWAR GARIN KANO
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
Shekaru sama da dubu biyu da suka gabata, sun tabbatar da cewa akwai mutane masu rayuwa a Afirka ta yamma. Wadannan mutane basu da wata sana'a sama da farauta. A wancan lokacin sana'ar noma bata shahara ba a duniya, don haka mutane suke dogaro da farautar namun daji a matsayin aikin yi. Lokaci yana tafiya, har labarin wani babban dutse ya fara zama shahararre a kunnuwan mafarauta. Dalili shine, akwai namun daji masu yawa a yankin da dutsen yake. Sannan ana iya haƙo Tama da ake sarrafa ƙarfe a wurin. Waɗannan abubuwan sunfi komai daraja a wancan lokaci. Domin akasarin kayayyakin farautar wadannan mutane da duwatsu aka sassaƙa su, don haka suke da matuƙar buƙatar kayayyakin ƙarfe saboda darajar su da sauƙin dasu ke dashi a wajen sarrafawa. Sunan wannan dutse DALA.
A bisa wata mahangar ta masana, wasu na ganin yankin Dala a matsayin wuri ne wanda k'abilu daban-daban (kazo-na-zo) ke taruwa domin shiga dajin dake jikinsa yin farauta. Shine har wasu ke ganin babu takamai_man k'abilar data fara zama a yankin., amma dai ana ganin yarukan da k'abilun ke amfani dashi sun had'ar da na ZULU, FULA, da SHONA. (Idan hakane, Hausa na iya fitowa daga had'akar wad'annan yaruka kenan, amma dai zamu saurara daga masana a bisa haka)
Babu takamaiman wanda ya fara zuwa bakin wannan dutsen, wasu sunce wata k'abila mai suna Dala ce ta fara zama, daga nan aka sanyawa dutsen suna Dala, wasu kuma sunce sunan wanda ya fara gina gida akan dutsen tare da fara rayuwa akai shine Dala. Don haka ake yiwa dutsen kachokan lak'abi da sunan sa.
Daga bisani dai, sai mutane suka fara zama kadan-kadan a gefen dutsen domin neman arziki. Makera na zuwa don hak'o tama da tare da sarrafa ƙarafa, mafarauta kuma na zuwa don siyen k'arafa tare da shiga farauta a dajin dake bayan Tsaunin Dala, kamar dai yadda yake a tarihi, za'a ga cewa mutanen da suka gabacemu sunfi rayuwa a wuri mafi daraja. Watau sa'ar da ruwa yake da tsada a wuri, sai kaga mutanen sun gina gari a wurin da ruwa yake, kamar yadda ya faru a garuruwan Makkah da sauransu.
Wad'anda suka ce Dala ne ya fara zama akan dutsen, sunce ya rayu tsawon shekaru masu yawa akan wannan dutse, tare dashi akwai matarsa da 'ya'yansu bakwai, hudu maza uku mata. Wani mai suna Garegaji aka bayyana a matsayin babban d'ansa, shine kuma akace uban wani k'ak'k'arfa mai suna Nuzamu, Nuzamu kuwa ance shine ya haifi Barbushe. Dala mutum ne k'ak'k'arfan gaske, wanda akace yakan iya kashe giwa ya sab'ota a kafada duk girmanta. Littafin tarihin kano 'Kano chronicle' ya faro tarihin kano ne daga lokacin Barbushe wanda akace shine yayi gadon wasu ɗabiu na kakan-kakan sa Dala. Shine ma har wata masaniyar tarihin Nigeria mai suna Elizabeth Isichei tayi hasashen cewa Dala tsatson k'abilar Sao ne saboda yadda akace girmansa da k'arfin sa yake yafi kamanceceniya da k'abilar ta sao. K'abilar sao kuwa itace tsohuwar k'abilar da tarihi ya nuna cewa al'ummar kanembou (Kanem) sun samo tsatso daga garesu.
Tarihi dai ya nuna cewa a lokacin Barbushe shine sarkin mutanen dake zaune a zagayen dutsen dala. Kuma suna da al'adar bautawa wani gunki mai suna 'Tsumburbura' wanda yake can kan saman dutsen dala, akan wata bishiya wadda take zagaye da katangu mai suna Shamus. Ance babu mai shiga wurin dodon tsafi tsumburbura sai barbushe. Duk kuwa wanda ya shiga sai ya mutu. Barbushe kuwa ance a saman dutsen yake rayuwa abinsa. Yana saukowa ga mutanen sa sau biyu a shekara domin gudanar da bikin bauta na al'ada. A lokacin mutane ke taruwa sosai a bakin dutsen na dala suna jiran saukowar sarkinsu barbushe. Wanda yake saukowa gabanin faduwar rana. Yana mai buga ganguna. Sai yayi kirari da yabo ga tsumburbura, mutane suna tayashi. Daga nan akace sai yahau sama mutanen na biye dashi a baya har izuwa saman dutsen na dala. Wanda akace daf da isarsu saman dutsen sai mutanen su yanka hadayar da suka kawowa tsumburar, abinda sukan yanka kuwa shine ; bakin kare, bak'ar kaza, ko bak'ar akuya. Idan suka isa bakin d'akin bauta kuwa, sai kowa ya tsaya. Barbushe ne kadai ke shiga. Kafin shigarsa ance sai yayi kirari da kuwwa. Yana cewa "Sai ni magajin dala. Mutane dole su bini, ko sunk'i ko sunso". Daga bisani idan ya fito, sai ya jagoranci bautar tsumburbura, wadda ake zagaya dakin bauta ana rawa da kida tsirara.
Idan an kammala kuma sai aci asha a wurin. Sannan sai barbushe ya fadi sak'on da tsumburbura ya bashi. Sak'on da mafi akasari akace labari ne na abubuwan da zasu faru a shekara mai zuwa. Duk wadannan abubuwa ana hasashen sun faru ne a shekaru k'asa da shekara ta 900AD (miladiyya) bayan wafatin Annabi Isa. Koda yake Marubucin littafin Kitab Al-buldan mai suna Al'yaqubi bayan yawace-yawacen sa dayayi a kusa da yankin, ya ruwaito a shekarar 872-873 cewa "akwai wata masarauta awani wuri dake tsakanin masarautar kanem da tafkin kwara (dai-dai da ko kuma kusa da inda kano take a yanzu), mai suna 'HBSH'. Sunan mai mulkinta 'MRH' sunan birnin ta 'ThBYR'. Rashin wasulla a wadannan kalmomi yasa shakku da jayayya a tsakankanin masana tarihi. Domin wasu na hasashen sunan masarautar shine Hausa, domin kuwa sunce HBshH na nufin Habasha ne, sunan da ake tsammanin daga cikinsa aka samo sunan Hausa. Wasu kuma na hasashen cewa masarautar ta auku ne a kusa da kano, amma daga baya kafuwa da k'arfin da kano tayi ya rusa ta, ya kuma yi sanadiyyar komawar mutanen ta zuwa kanon.
Koma ya abin yake, daga baya littattafan tarihi na kano misalin 'Kano chronicle' (har yanzu ana taba-bar wanda ya rubuta shi), Raudat al-akbar na Abdulqadir bn mustafa Almagili sun ruwaito cewa wani mai suna Bagauda ne ya zama sarkin kano na farko a tarihi. Shi kuwa bagauda wasu na cewa jikan bayajidda ne, kuma daga garin gaya suka taso shi da al'ummar sa, wai sunan su shine 'Abagayawa' (wadanda suka zo daga gaya) ko gaudawa, shiyasa kuma ake kiransa da 'Bagauda', ma'ana, mutumin gaudawa, kamar yadda mallam bahaushe ke yiwa d'aya daga cikin turawa lak'abi da Bature daga Baturke (Mutumin Turkiyya).
Wasu kuma suka ce sam, Bagauda ba jikan Bayajidda bane, yazo yankin dala ne tare da wata runduna mai yawa kamar yadda Barbushe ya taɓa bada labarin zuwan su, kuma ainihin sunan sa shine kano, don haka daga nan kano ta samo sunan ta. A lissafin da mukayi dai-dai da yadda littafin wak'ar bagauda 'kano chronicle' (duk da cewa an samu sab'anin shekarun mulkin wasu sarakunan) ya nuna, Bagauda ya rayu a matsayin Sarkin kano a wajajen shekara ta '950 zuwa 1031'. Amma da yake akwai saɓanin shekarun mulkin wasu sarakuna, wasu dayawa sun sanya somawar nulkin Bagauda a shekarar 999.TARIHIN KAFUWAR GARIN KANO
Daga SADIQ TUKUR GWARZO
08060869978
Shekaru sama da dubu biyu da suka gabata, sun tabbatar da cewa akwai mutane masu rayuwa a Afirka ta yamma. Wadannan mutane basu da wata sana'a sama da farauta. A wancan lokacin sana'ar noma bata shahara ba a duniya, don haka mutane suke dogaro da farautar namun daji a matsayin aikin yi. Lokaci yana tafiya, har labarin wani babban dutse ya fara zama shahararre a kunnuwan mafarauta. Dalili shine, akwai namun daji masu yawa a yankin da dutsen yake. Sannan ana iya haqo Tama da Qarfe a wurin. Wadannan abubuwan sunfi komai daraja a wancan lokaci. Domin akasarin kayayyakin farautar wadannan mutane da duwatsu aka sassaqa su, don haka suke da matuqar buqatar kayayyakin qarfe saboda darajar su da sauqin dasu ke dashi a wajen sarrafawa. Sunan wannan dutse DALA.
A bisa wata mahangar ta masana, wasu na ganin yankin dala a matsayin wuri ne wanda k'abilu daban-daban (kazo-na-zo) ke taruwa domin shiga dajin dake jikinsa yin farauta. Shine har wasu ke ganin babu takamai_man k'abilar data fara zama a yankin., amma dai ana ganin yarukan da k'abilun ke amfani dashi sun had'ar dana ZULU, FULA, da SHONA. (Idan hakane, hausa na iya fitowa daga had'akar wad'annan yaruka kenan, amma dai zamu saurara daga masana a bisa haka)

Daga bisani dai, sai mutane suka fara zama kadan-kadan a gefen dutsen domin neman arziki. Makera na zuwa don hak'o tama da k'arfe tare da sarragawa, mafarauta kuna na zuwa don siyen k'arafa tare da shiga farauta a dajin dake bayan dutsen dala, kamar dai yadda yake a tarihi, za'a ga cewa mutanen da suka gabacemu sunfi rayuwa a wuri mafi daraja. Watau sa'ar da ruwa yake da tsada a wuri, sai kaga mutanen sun gina gari a wurin da ruwa yake, kamar yadda ya faru a garuruwan Makkah da sauransu.
Wad'anda suka ce Dala ne ya fara zama akan dutsen, sunce ya rayu tsawon shekaru masu yawa akan wannan dutse, tare dashi akwai matarsa da 'ya'yansu bakwai, hudu maza uku mata. Wani mai suna Garegaji aka bayyana a matsayin babban d'ansa, shine kuma akace uban wani k'ak'k'arfa mai suna Nuzamu, Nuzamu kuwa ance shine ya haifi Barbushe. Barbushe mutum ne k'ak'k'arfan gaske, wanda akace yakan iya kashe giwa ya sab'ota a kafada duk girmanta. Littafin wak'ar bagauda 'Kano chronicle' ya faro tarihin kano ne daga lokacin Barbushe. Shine ma har wata masaniyar tarihin Nigeria mai suna Elizabeth Isichei tayi hasashen cewa Barbushe d'an k'abilar Sao ne saboda yadda akace girmansa da k'arfin sa yake yafi kamanceceniya da k'abilar ta sao. K'abilar sao kuwa itace tsohuwar k'abilar da tarihi ya nuna cewa al'ummar kanembou (Kanem) sun samo tsatso daga garesu.

Idan an kammala kuma sai aci asha a wurin. Sannan sai barbushe ya fadi sak'on da tsumburbura ya bashi. Sak'on da mafi akasari akace labari ne na abubuwan da zasu faru a shekara mai zuwa. Duk wadannan abubuwa ana hasashen sun faru ne a shekaru k'asa da shekara ta 900AD (miladiyya) bayan wafatin Annabi Isa. Koda yake Marubucin littafin Kitab Al-buldan mai suna Al'yaqubi bayan yawace-yawacen sa dayayi a kusa da yankin, ya ruwaito a shekarar 872-873 cewa "akwai wata masarauta awani wuri dake tsakanin masarautar kanem da tafkin kwara (dai-dai da ko kuma kusa da inda kano take a yanzu), mai suna 'HBSH'. Sunan mai mulkinta 'MRH' sunan birnin ta 'ThBYR'. Rashin wasulla a wadannan kalmomi yasa shakku da jayayya a tsakankanin masana tarihi. Domin wasu na hasashen sunan masarautar shine Hausa, domin kuwa sunce HBshH na nufin Habasha ne, sunan da ake tsammanin daga cikinsa aka samo sunan Hausa. Wasu kuma na hasashen cewa masarautar ta auku ne a kusa da kano, amma daga baya kafuwa da k'arfin da kano tayi ya rusa ta, ya kuma yi sanadiyyar komawar mutanen ta zuwa kanon. Koma ya abin yake, daga baya littattafan tarihi na kano misalin 'wak'ar bagauda' (har yanzu ana taba-bar wanda ya rubuta shi), Raudat al-akbar na Abdulqadir bn mustafa Almagili da Tayqidil Akbar na Mallam Muhammad zangi sun ruwaito cewa wani mai suna Bagauda ne ya zama sarkin kano na farko a tarihi. Shi kuwa bagauda wasu na cewa jikan bayajidda ne, kuma daga garin gaya suka taso shi da al'ummar sa, wai sunan su shine 'Abagayawa' (wadanda suka zo daga gaya) ko gaudawa, shiyasa kuma ake kiransa da 'Bagauda', ma'ana, mutumin gaudawa, kamar yadda mallam bahaushe ke yiwa d'aya daga cikin turawa lak'abi da Bature daga Baturke (Mutumin Turkiyya).
Wasu kuma suka ce sam, Bagauda ba jikan Bayajidda bane, yazo yankin dala daga Gaya ko wani gari dake yammacin Kano bayan Sheme ta Katsina tare da wata runduna mai yawa kamar yadda Barbushe ya tab'a bada labarin zuwan su.
A lissafin da mukayi dai-dai da yadda littafin wak'ar bagauda 'kano chronicle' (duk da cewa an samu sab'anin shekarun mulkin wasu sarakunan) ya nuna, Bagauda ya rayu a matsayin Sarkin kano a wajajen shekara ta '950 zuwa 1031'.
Daga nan kuma sai sarakunan jinsin sa suka cigaba da mulki a kano har na kusan tsawon shekaru 450, tunda ance Sarkin kano Ali Yaji ne Sarki musulmi na farko a tarihin sarakunan kano. Kuma ya amshi mulki ne a wajajen shekara ta 1350, wanda a lokacin sane wasu malamai masu fatauci da ake kira Wangarawa suka barokasar su Mali tare da kawo musulunci kano.
Game da inda sunan garin ga samo asali, wasu sunce 'kano', wani shahararren mak'eri ne da aka tabayi tun a wancan lokacin wanda ya taso daga garin Gaya ya sauka a yankin dutsen Dala...

Salamu allium,Akwai littafin tarihin masarautar gaya kuwa?
ReplyDelete