Saturday, 6 January 2018

ALAKAR FIR'AUNA DA HAUSAWA 3

SHIN FIR'AUNAN DA YAYI ZAMANI DA ANNABI MUSA (A.S) BAHAUSHE NE?

Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
    08060869978

Kashi na Uku.

Ana iya bin diddigin alakar Misirawa da sauran kabilu ciki kuwa harda hausawa ta hanyar komawa tsoffin zantukan da masana tarihi suka faɗa game da wannan yanki na Afirka.
   Da fari dai, an samu cewa akwai masarauta a Misira shekaru sama da dubu shidda da suka gabata, daga nan aka sake ruwaito cewar an samu ɓullar wata masarauta mai suna 'Nubia' ko 'Kush' ta bakaken fata wadda take karkashin ikon misira, daga baya kuma ta ɓalle daga gareta a wani lokaci wanda karfin daular misira ya fara raunana, har kuma aka ruwaito cewar Waccan masarauta ta Kush ta karɓe iko da Misira a wani lokaci, inda aka samu jerin wasu fir'aunoni bakaken fata (sarakunan misira) waɗanda asalinsu daga Masarautar bakaken fata sukema fito.
   A wancan tsohon zamani, an samu wanzuwar hijira ta misirawa izuwa daular bakaken fata da akace tana wani gari mai suna Napata, saboda raunin daular tasu, bisa mararin samun kuɓuta da cigaban rayuwa, tun daga wuraren shekaru dubu biyu zuwa dubu da ɗari biyar kafin haihuwar Annabi Isa A.S, har zuwa zamanin da Fir'auna Thutmose III ya hau mulki, ya tafi da yaki kasar bakaken fata, ya juma cinye Nubia tare da kafa wani karamin gari mai suna 'Dukki gel' don kare misira daga harin ramuwar gayya a gaba.
  Daga nan sai daular bakake ta tashi izuwa baya daga misira, inda ta kafu a Meroe, wani birni dake kasar Sudan a yanzu.
  Tun daga lokacin kuma akace mutane suka rinka kwararowa yankunan yammaci da gabashi na Afirka domin samun rayuwa mai sauki, saboda azabar yake-yake da azabtarwar masu mulki.
   Marubucin littafin 'Races in Africa' C. G Seligman ya faɗi a shafi na 30 yadda mutane suka rinka kwararowa lokuna da sak'unan afirka da sunan farauta, har ma yace mutanen na rayuwa rukuni-rukuni akalla su 50 zuwa 100.
  Yace kuma Suna da karancin suturu, don haka da ganyaye suke rufe tsiraici, suna kuma da al'adu irin nasu.
  Sannu a hankali, daular Meroe tayi sanyi, daga baya ma wata daula mai suna Aksum ta kafu har kuma ta karɓe ikon ta.
   Ita daular Aksum, kamar gamin gambizar larabawa ne da bakaken fata. Tunda masana tarihi ciki harda Munro Hay marubucin littafin 'Aksum:  An african Civilization of Late Antiquity' sun faɗa cewar Sabiyawa da Kabilun Kudancin larabawa da kuma zaunannun mutanen kasar bakar fata ne suka haɗu a wannan daula suka gina ta.
  Zuriyar da suka haifa kuwa  aka sanyawa suna Abesha.
 Koda yake, littafin 'Book of Aksum' ya faɗa cewar wani mai suna Itiyopis ɗan Kush jikan Annabi Nuhu shine ya soma kafa birnin daular Aksum mai suna Mazaber, wanda ke tsakanin kasashen Ethiopia da Eritrea a halin yanzu. Don haka, tana iya yiwuwa daga bisani mutane suka cika garin har kuma suka haifar da zuriya mai suna Abeshawa.
  Daga nan, mun samu a littafin 'The History of Ethiopia' na A. H. M Jones da Elizabeth Monroe  cewar a zamanin Annabi Sulaiman (wuraren shekaru 900 kafin haihuwar Annabi Isah A.S) alaka ta auratayya ta auku da sarauniyar Sheba, ta daular Aksum har kuma sun samar da zuriya tsakani.
  Haka kuma, daga baya zamanin Annabi Musa A.S (wajajen shekaru 600 kafin haihuwar Annabi Isah A.S) sai akace shima ya auri bakar fata daga daular Aksum kamar yadda yazo a littafin 'History of churches and Monestries of egypt' na Abu Saleh, cewar sarakunan Habashawa jinin Annabi Musa A.S ne, yayinda wasu sukace ai mahaifiyar Annabi Musan ma bakar fata ce daga zuriyar Abesha.
   Ita kuwa waccan kalma ta 'Abesha', itace ta koma 'Habeshat', ta sake sauyawa zuwa 'Habeshi, sannan ta koma 'Habesh', daga baya kuma ta zama 'Habasa' har kuma wasu ke kallonta a matsayin wacce ta sake sauyawa izuwa 'Hausa'..
   Sauyawar Abesha ko Habasa izuwa Hausa na iya zama ta dalilin tasowar wasu daga cikin wancan kabila daga daular Aksum izuwa nan kasar hausa, ta yadda zasu rinka kiran kansu da Habasawa, daga baya kuma a kirasu da Hausawa.
   Don haka, idan har ta tabbata Hausa itace Habasa, babu mamaki idan har alaka ta samu tsakanin su da misirawan lokacin fir'aunan Annabi Musa.
   Dr. Edward Glasser dai shahararen masanin tarihi ne ɗan kasar Austria, ya kuma faɗa cewar Kalmar 'Habesha' ta fito ne daga yaren Mahri, kuma abinda take nufi shine 'Haɗuwa'.
   Daga Habesha ne kuma akace zuriyar Tigra, Agew, Beta Israel da Amhara na kasar ethiopia da Eritrea suka fito.
  Saboda haka, matsawar binciken kimiyya na kwayoyin halittu zai nuna alaka tsakanin kabilun Tigra, Agew, Beta da Amhara kamar yadda alakar harshe ta nuna akwai wani abu tsakaninsu, to tabbas zamu gamsu cewar Habasawa ne suka yo kaura izuwa kasar hausa har kuma suka canza  izuwa Hausawa, sannan kuma suna da alaka da misirawa bama fir'aunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S kaɗai ba.
  Ko kuma duk ba haka ba, kai tsaye Hausawa na iya samo alaka ta tale-tale da Alummar Khemites, waɗanda aka gamsu da cewar sune asalin tushen Misirawa kamar yadda Farfesa Yusuf Adamu ya bada sharshi a Zauren Binciken Tarihin Hausa. Kenan, da kakanni Hausawa, dana midirawa duk ɗaya ne.
  Karshe.
(NB Rashin fahimtane wani yaji aibu don ance Hausawa da Fir'auna nada alaka domin An samu Annabawa fiyayyun Mutane sunyi alaka da mutane masu girman saɓo, kuma da yawan masu amfani da harshen Hausa babu jinin Hausawa na asali a jinin jikinsu. Don haka sai akula da aikata wauta).

No comments:

Post a Comment