Saturday, 27 January 2018

TARIHIN DAULAR ZAZZAU 2

TARIHIN KAFUWAR DAULAR ZAZZAU

Kashi na biyu

  DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

KUFENA
   Kufena wani tsohon kauye ne dake yammacin birnin zaria na yanzu, kuma ance ya taɓa zamowa cibiyar masarautar zazzau mai cike da wayewa acan baya.
   Ance wasu maharba karkashin shugabancin wani mai suna 'Dan zau ne suka kafa shi tun wajajen karni na ɗaya. Kuma sun fara zama ne akan tsaunikan dake wurin, daga baya wasunsu suka koma kan tsaunikan yankin Madarkachi.
   Shi kanshi sunan Madarkachi, ance daga kufena ya samo asali.
  Wasu na ganin wani mai suna Madara shine babba cikin masu zama a Madarkachi, don haka idan yazo kufena sai a tambayeshi 'Madara, kachi abu kaza?'
  Wasu kuma suka ce da yake ba lallai hausawa ne kabilar madarkaci ba, don haka idan suka zo kufena sai suke cewa 'Madara kachi' mai makon 'madara kasha'.
  Shi kuwa sunan Kufena, ana ganin ya samo asali ne daga 'Kafe A Nan'.
   Watau waɗannan maharban da suka sauka a wurin nada inda sukayi nufin zuwa amma sai suka ɓige da zaman nan, don haka suke kiran kansu/ ko ake kiransu da 'waɗanda suka kafe anan', daga baya sunan ya sauya zuwa kufena.
MADARKACHI
  Kauye ne dake arewa maso gabashin birnin zaria.
  Binciken kimiyya ya tabbatar da wanzuwar mutane a wannan waje shekaru sama da dubu da suka gabata.
  Haka kuma ana kallon wani  dutse a wurin a matsain wurin bautar Iskokai ga mazauna Madarkachi, har kuma wasu ke tsammanin tana iya kascewa wannan mahsrbin mai suna 'Dala' daga nan yake ya taso zuwa dutsen dala na kano tare da bijirar da irin bautar Iskokai da akeyi a wurin.
  KARGI
 Kauye ne a gabashin Madarkachi, kuma ɗaya ne daga ɗaɗaɗɗun wajen zama a zazzau.
  Mutanen Kargi sun faɗa cewar asalin mazauna Kawuri, waɗanda suka dawo Rikochi, da mazauna wuchichchiri, Turunku, da Kufena, da Zaria ne suka haɗu tare da kafa hamshakiyar daular Zazzau. Kuma wani mai suna 'Madaki Gunguma' shine sarkin daular na farko.
WUCHICHIRI
  Kauye ne dake arewacin garin zaria wanda binciken kimiyya ya tabbatar da alamun daɗaɗɗiyar rayuwa a wurin.
   Ance sunan wurin ya samo asali ne a lokacin da wasu jama'a sukayi nufin cire wasu busassun ciyayi a wurin don yin bukkoki sai abin ya basu wuya, shine wai suke cewa "ciyayin nada wuyan chich chirew.." Har kuma ake kiran wajen wuchichchiri.
  Ance madaki Gunguma da jama'ar sa sun taɓa zama a wurin kimanin shekara ɗaya a wajajen karni na goma sha huɗu. Anan suka kera kwari da baka ta farauta saboda makera da suka zauna a wurin bisa albarkar tama da karafan wurin, sannu a hankali kuma sai manoma, makiyaya da sauran mutane suka rinka kwarara.
  Sauran wuraren da aka tabbatar da cewar shekaru da yawa da suka gabata mutane sun zauna a cikinsu sune:- Tukur-Tukur, Hange-Hangawa, Fara-Kwai, Dutsen wai, Tsauni da Dutsen Pampuri.
  

No comments:

Post a Comment