Saturday, 27 January 2018

TARIHIN ZUWAN TURAWA ZARIA 1

ZUWAN TURAWA ZARIA

Kashi na ɗaya

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Tun gabannin mamayar turawa ga daular Zazzau, an samu cewa karfin daular ya ragu nesa da yadda ta kasance a baya sabili da wasu dalilai
   Da fari dai, akwai rikicin cikin gida daya mamaye kabilun fulani da suka jagoranci karɓe ikon Zazzau a zamanin Jihadi saboda neman mukami.
  Ance tun zamanin Sarki na farko aka soma wannan saɓanin  tsakanin Jagora kuma sarkin Zazzau na farko Mallam Musa da wani Ja'e shugaban kabilar fulani Yesgwamawa, amma sai aka bashi sarautar Kajuru aka zauna lafiya.
   Daga baya sai rikicin ya sake kamari bayan rasuwar Sarkin Zazzau Usman Yero, a wajajen shekara ta 1897 kenan.
  Hakan ya samu ne ta yadda kabilu huɗu na fulani da aka sani da mulkin zazzau suka nuna bukatarsu ga mulkin, kabilun sune Mallawa, Katsinawa da Barnawa.
   A cikin masu neman mulkin akwai ɗan marigayi Sarki Yero mai suna Madaki Kwasau, sai Mallam Lawan ɗan tsohon Madaki da kuma wani daga cikin 'ya'yan tsohon sarkin zazzau Mallam Sambo.
   Babban abinda kuma ya samar da saɓani a lokacin shine yadda Galadima ya tsaya kai da fata cewar wani kurma kuma Makaho mainsuna Mallam Muhammd ya kamata a baiwa sarauta. Mutane sunce hakan nada nasaba da kokarinsa na ɗora wanda ba zai iya kataɓus ba a mulki ta yadda zai rinka juya shi.
  Ganin karfin ikonsa yasa waɗancan kabilu na fulani suka dunkule tare da goyawa Madaki kwasau baya domin ya zama sarki. Akan haka suka nemi gudunmuwar Sarkin Kano Aliyu Babba, da kuma rundunar 'yan bindiga da mahaifin Madaki Kwasau ya kafa a zamanin rayuwarsa, shikuwa Galadima sai ya nemi goyon baya daga Sokoto.
   Ana cikin wannan kiki-kaka, sai wazirin sokoto Buhari yazo zazzau da niyyar masalaha. Ya lura da haɗarin dake ciki ainun idan aka ɗora wani ba Kwasau ba akan gadon mulki, tunda yasan yadda Basasa ta kaya a kano, sai kurum ya ɗora Madaki Kwasau sarautar Zazzau.
  Yin haka keda wuya sai wasu daga mabiya da garuruwa suka fara yin bore.
  Sarki Kwasau ya shirya yaki ya tafi Gwari, da Kataf da Kadara tare da tilasta musu yin biyayya a gareshi.
   Abu na biyu kuma da ya sake raunana zazzau shine hare-haren da take samu daga wasu sarakunan hausa misalin Maraɗawa da Ningawa.
  Idan dai ba'a manta ba, a lokacin Maraɗawa na tsaka da kai hare-hare kasar hausa. Bayan sarkin su Dan baskore ya mutu, sai wanda ya gajeshi mai suna Baratiya ya ɗora akan inda ya tsaya.
  Baya danan sai Mutanen Ningi, waɗanda akai-akai suke kawo hari ga birnin Zazzau. Shine har akace sun taba yiwa zazzau ɗin ruwan kibiyoyi a lokacin da suka kawo faɗa zazzagawa suka shige cikin ganuwa suka kulle kansu. Kuma har sun kwace ikon wasu garuruwa irinsu Soba, Dutsen Wai da Kubau daga Zazzau.
  Kari akan haka shine Sarkin Kwantagora Nagwamutse, shima a lokacin ya addabi zazzagawa da hari.
  Duk kuma a wannan lokaci turawa fakare sukai suna kallon zazzau. Saboda ance sun gama lissafa cewar itace cibiyar da zata fi a garesu wajen kafa sansani kafin kaiwa Kano da Sokoto hari.
   Kuma kasancewar akwai turawan mishan dake al'amuransu a Zaria sai ya zamana turawa basu da burki gareta, suna shigowa suyi hurɗoɗinsu babu tsangwama.
  Ana haka sai labari yazowa Sarkin Zazzau Kwasau cewa turawan mishan sun nemi wurin zama a Kano amma sarki Alu ya koresu, sannan rundunar dakarun turawa mai suna 'West African Frontier Force' (WAFF) ta kone garuruwan Remo da Kaje dake karkashin zazzau, kuma da raɗe raɗen zasu kawowa zaria yaki don hana cinikin bayi. Sai kawai sarki Kwasau shima ya kori turawan mishan daga kasar sa suka koma Girku da zama.
   Yin wannan keda wuya sai shugaban waccan runduna ta turawa mai suna Kaftin Kambell ya kawo ziyara ga sarki Kwasau, yace yazo kulla abota ne dashi tare da samar da yarjejiniyar zaman lafiya a tsakaninsu.
  Abinda ya kara kwantar wa da Sarki Kwasau hankali a game da turawa shine yadda suka kame kwantagora tare da korar sarkin su abokin hamayyarsa Sarki Ibrahim Nagwamutse a  shekarar 1901, sannan kuma suka kame sarkin a wani faɗa da sukayi a Maska suka aike dashi garin Lokoja aka tsare.
   Wannan yasa hankalinsa ya kwanta dasu domin sunyi masa maganin abokin hamayyarsa, suka rinka kwararowa cikin zaria suna lamurorinsu.
   Sai dai kwatsam babu aune, sai sarkin Zazzau Kwasau yaji turawa Sun ayyana Zaria a matsayin garin da suke iko dashi tare da kawo wani bature mai suna Kaptin Abadie da akafi sani da suna Mai jimina a matsayin Rasdan na garin, wannan yasa sarkin cikin damuwa da ɓacin rai.
   Ya shiga tunanin mafita a wannan lamari, gashi yana da rauni wajen faɗa da turawa, sannan sarkin Bidda ya aiko masa da gargaɗin kada ya kuskura yace zai buga dasu, gashi kuma yana jin kaskancine ya cigaba da zama a kasansu.
  Don haka mafitarsa biyu ce, kodai ya hakura ya zauna cikin kaskanci, ko kuma ya nemi taimakon sarkin Kano Alu yayi yaki dasu.
  Da tunani yayi zurfi, sai kurum ya zaɓi shawara ta biyu..

No comments:

Post a Comment