Saturday, 6 January 2018

TARIHIN AUDU BAKO

9. TARIHIN AUDU BAKO

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
   08060869978

An haifi tsohon gwamnan kano marigayi Audo Bako a barikin 'yan sanda na kaduna cikin shekarar 1924.
  Mahaifinsa ɗan sanda ne, kuma shine sarkin sabon garin kaduna.
  Audu Bako yayi karatun elemantare a Kaduna, sannan ya tafi Zaria yayi kwaleji acan, daga nan ya samu shiga rundunar 'yan sandan Nigeria a shekarar 1942.
 Da fari, Audu Bako ya soma zama malami a kwalejin horas da 'yansanda ta kaduna, sannan a hankali ya rinka samun ɗaukaka ta yadda har saida ya zama mataimakin Kwamishina mai kula da yankin Arewa.

   An naɗa Audu Bako a matsayin Gwamnan Kano da kakinsa na ɗansanda a shekarar 1967 bayan anyi wannan mummunan juyin mulki na shekara ta 1966.
 Tun da hawansa sai ya dukufa wajen inganta kananun hukumomi, da kuma samar da kyakkyawar hurɗa tsakanin gwamnati da sarakuna da kuma talakawan nasa duk kuwa da kasancewarshi shugaba da kakin sarki.
Audu Bako ne gwamnan daya gina kusan ɗaukacin manyan gine-ginen birnin kano. Misali, shine ya gina sakatariyar Audu Bako baki ɗayanta wadda ko a yanzu, yana da wuya a samu wani mahaluki da zaiyi irin wannan gagarumin aiki.
  Baya da haka, ya gina kwalejin aikin Gona a Dambatta wadda aka sanyawa sunansa.
  Haka kuma, Audu Bako ne Gwamnan kano na farko daya soma yunkurin ɗaukaka darajar 'ya'ya mata ta hanyar tsara musu hanyoyin samun ilimin zamani dai-dai da koyarwar Shehu Usmanu ɗan fodio. Sannan a zamanin mulkinsa ne aka soma tsara hanyoyin samun kuɗin shiga daga baki masu yawon buɗe ido. A shekarar 1969 Audu Bako ya soma gina madatsar ruwa ta Bagauda domin samar da ruwan noman rani a Kadawa.
Daga shekarar 1970 zuwa 1973 gwamnatinsa ta gina babban madatsar ruwa ta Tiga bisa burin haɓaka noman rani da yawon buɗe ido.
Ana yiwa Audu Bako lakabi da 'Uban Noman Kano' saboda manyan madatsaai na ruwa daya gina a faɗin jihar kano.
 
Audu Bako yayi ritaya a shekarar 1975 bayan juyin mulkin daya kawo karshen Rasuwar Janar Murtala da aka shirya wanda bai samu nasara ba, sannan ya soma aikin noma a sokoto.
   A shekarar 190 Allah ya yiwa Audu Bako rasuwa. Kuma har gobe shi abin tunawa ne duba da manyan gine-ginen daya yi a kano.

No comments:

Post a Comment