Thursday, 28 December 2017

TARIHIN MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO

MAITAMA SULE DAN MASANIN KANO

An haifi marigayi Yusuf Maitama Sule ɗan masanin kano a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 1929 a birnin kano.
   An sa masa suna Yusuf ne, saboda sunan Mahaifin Madakin Kano Mahmudu, dom haka Madaki yana kiran sa da suna Abbana. Sunan Maitama kuwa an sanya masa shine sabili da Galadiman Kano Yusuf, saboda an yi amfani da makamai sosai lokacin yakin basasar Kano, don haka ake kiran duk wani Yusufu da suna Maitama.
  Madakin Kano ya yi wa Mahaifin Maitama, Abba Sule Danmuri, mukamin mai kula da dukkan al'amuransa na gida da kula da Dawakai.
   Maitama Sule na ɗan shekaru 4 mahaifiyarsa Hauwa wacce ake kira 'Yarkayi ta rasu. Ita kuwa Allah yayi tane mace mai ban dariya, mai raha, ba ta fushi, shi ya sa duk bukin da ya tashi ita ake kira ta yi ta magana a gidan buki, halinta da iya maganarta Maitama ya gado.
  Madakin Kano ya saka Maitama Sule a makarantar Elemantare ta Shahuci a cikin watan Janairu, 1937, dama tun kafin akai sa makarantar boko, suna yin karatun alkur'ani a gida.
   A ka'ida shekaru huɗu ya kamata ayi a elemantare, amma saboda hazakar da Maitama Sule ya nuna shekaru biyu kacal yayi aka bashi damar ɗaukar jarabawar zuwa midil.
  A wancan lokacin ne kuma Maitama Sule ya fuskanci kalubalen da bai taba fuskanta ba a rayuwarsa kasancewar a lokacin ne mai ɗaukar ɗawainiyarsa a rayuwa ya rasu cikin shekarar 1939. Aka bar kujerar Madaki, tsawon shekaru biyu, ba'a naɗa kowa ba, har sai a shekarar 1941.
  Bayan haka ta faru, sai Gaba ɗaya ɗawainiyyar Maitama Sule ta koma kan Mahaifinsa Abba Sule, wanda a wancan lokacin kuma ba shi da karfin da zai iya ɗaukarta. Sai da ta-kai Abba Sule, ya saida duk wani abunda ya mallaka har da suturunsa na sawa dan ya ɗauki ɗawainiyar 'ya'yansa, a lokuta da yawa haka suke kwana da yunwa.
  Ranar da suka samu ɗan abin taɓawa, a daren gasasshehen rogo ne za su ci su kwanta. A karshe Maitama Sule ya shiga makarantar Middle, a wannan datsen an kai matsayin da Maitama ko suturar da zai sa ba shi da ita, kayan makaranta kawai sune kayan sanyawarsa.
  A shekarar 1943 Maitama ya shiga kwalejin Kaduna, yana ɗan shekaru 13. Maitama, ya kammala karatunsa na kwaleji cikin shekarar 1948, ya kuma kama aikin Malanta, a makarantar Middle ta Kano.
  Maitama Sule ya tsaya zaɓen majalisar wakilai, yana takara da  tsohon Malaminsa a makaranta, watau Malam Aminu Kano, wannan zaɓe ya gudane a Central Office, wannan abu ya faru ne a 1954.
  Lokacin da aka faɗi sakamakon zaben Malamin, zaɓen ya bada sanarwar cewa Maitama Sule ne ya lashe wannan zaɓen.
 Ana fadar haka kuwa sai Mallam Aminu Kano, ya juyo ya cewa Maitama Sule: ina tayaka murna, saura idan kaje kuma ka ba mu kunya.
   Maitama Sule ya cewa Aminu Kano, "Yallaɓai wallahi, ba zan ba ka kunya ba". Suka riko hannun juna suka fito tare, wanda suka fara gamuwa da shi shi ne Ado Bayero, inda ya rike hannun Maitama Sule, ya nufi inda magoya bayansa suke, ya ce sun ci zaɓe.
   Maeigayi Maitama Sule Ya zama ministan tama da karafa a janhuriya ta farko. Sannan Bayan faɗuwar jamhuriya ta farko, ya dawo gida Kano, inda ya rike mukamin kwamishinamai kula da kananan hukumomi a gwamnatin Audu Bako. Ya rike mukamin shugaban hukumar sauraren koke-koken, jama'a ta kasa a gwamnatin Msrigayi Janar Murtala.
Yayin da a shekarar 1979 ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar NPN, sai dai Shehu Shagari ne ya lashe zaben.Har ila yau, gwamnatin Shagari ta naɗa shi jakadan Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya watanni bayan kammala zaben.
A can ne kuma ya jagoranci Kwamitin Musamman kan Yaki da Wariyar Launin Fata na majalisar, wanda masu sharhi ke ganin ba karamin matsayi ba ne.
  Hakazalika, bayan da Shugaba Shagari ya lashe zaɓe a shekarar 1983 ya sake nada Maitama Sule Minista Mai Kula da Tafiyar da Kasa, wato mai taimakawa shugaban kasa kan yaki da cin hanci.
  An taba ruwaito shi yana cewa: "Kowanne mutum yana da baiwar da Allah Ya yi masa. Allah Ya ba 'yan arewa kwarewa ne wajen shugabanci. Bayarabe wajen dogaro da kai da kuma kyawawan dabi'u. Igbo suna da baiwa wajen kasuwanci da kuma kere-kere. Allah Ya halicce mu daidai kuma kowa da baiwar da Ya yi masa."
Wasu sun yi amfani da wannan kalami nasa wajen bayyana damuwa game da yadda 'yan arewa suka mamaye fagen shugabancin kasar.
A shekarar 1957 gabanin Najeriya ta samu 'yancin kanta, marigayi Maitama Sule shi ne ya kewaya da Sarauniyar Ingila Elizabeth yayin da ta kai ziyara Kano yana yi wa jama'a bayaninta.
  A karshe, Ya rasu a watan yulin shekara ta 2017, ya bar 'ya'ya 10 - maza hudu, mata shida.
  Da fatan Allah yajikansa Amin

No comments:

Post a Comment