K'ASIDATU TARIHIN SARAKUNAN KANO
(wak'ar Bagauda)
Wanda ya rera: Abubakar Bak'in Ruwa
Wanda ya rubuta a ajami: Shu'aibu Kabuga
Farfesa Abdullahi Uba Adamu ya alkinta mana ita.
Sadiq Tukur Gwarzo ya kawo muku ita daga ajami zuwa hausar boko.
Bismillahir Rahmanir Raheem. Sallallahu Ala sayyidina Muhammad wa ahlihi wa sahbihi wa zurriyatihi wa sallim taslima.
Ta'ala Rabbuna sarkin sarauta, Kariymu Rahiymu Allah ne da baiwa.
Idan roko gareka ka roki Allah, Gama shine ya bawa kowa.
Sarauta da dukiya da duniya tabaka, kabar cira kai kana Rowa ciccikawa.
Kabar hura hanci duniya ce, Abinda tabaka baya tabbacewa.
Ka duba sarakunan da akayo abaya, Da labarinu ya rik'a sai b'acewa.
Bagauda shi ya sari kano da fari, Tana daji sa'annan babu kowa.
Yana Gaya shi Bagauda gidan sa, Maharbine rikakke mai kashewa
Yazo cirani yayi bukka mad'atai, ya zauna yanuwa sa suna tafowa
Maharba gwargwado suka d'aura taro, Gunsa suna kisan zaki da giwa.
Da nama yayi yawa danye k'afaffe, fa ba mata maza ne ke dafawa
Da Gwale da shida Yakasai da Sheshe, da Guguwa nanya-manyan maguzawa
Ana cewa dasu sune sarakai, na noma sun kazo dawa gewayawa.
Suka kulle dawa suka kama gona, fa sai aiki iyali na tafowa
Ga Mallam Nuhu naji babu k'age, batuna bashi tareda k'aryatawa
Manoman da sunka tafo da fari, sukan sara suna kuma dandad'ewa
Sa'annan sai ruwan bazara ya sauka, sukai shukar su ta rinka furfutowa
Sukai dawa, gero ba misali, aka samu ana kuma ribatawa
Su kai k'arfi na bayi har dawaki, Da sune manya-manyan tajirawa
Gabas ta taho da yamma har arewa, wajen kudu sunka b'arko maguzawa
Da barnawa da katsinawa da daura, da zanfara can tahabi da gobirawa
Mutan zurmin da suda mutan talata, Bakura dasu Anka suna tafowa
Sukai ta awo suna kamun gidaje, kabawa da kunburawa da Adarawa
Da tun daga yankatsari gida ya zaga, ta mariri ya kawo gunduwawa
Mutane na asarari sunyi shanya, da babu sarki fa, babu wurin tsarewa
Da tunbi da sudawa shashen-ga nayza, suna gama kai suna kame kanawa
Da manya suka ce sai an sarauta, sukai sarki Bagauda mai tsarewa.....

No comments:
Post a Comment