Friday, 22 December 2017

MAFITAR LALACEWAR AURE A KASAR HAUSA

Assalamu Alaikum
>   Matsalolin da suka danganci
> aure, suna daya daga cikin matsaloli masu wuyar magani,
> wadanda kuma a kullum suke barazanar gurbata wannan al'umma
> tamu ta Hausawa daga mai kyau izuwa mummuna.
>   Wataqila wuyar magance musu baya
> rasa nasaba da yadda masu qoqarin magancewar suka gaza
> binciken asalin matsalolin tun daga tushe, yadda a qarshe
> za'a samu nasarar samar da hikimomin da zasu zamo magunguna
> ga matsalolin.
>     Da farko dai, Malaman mu
> sun sanar damu cewa kakanmu Annabi Adam A.S shine farkon
> mutum da Allah ya fara halitta, sai daga baya ya halicci
> matarsa Nana Hauwa'u daga jikinsa, wasu malaman ma sun tafi
> akan cewa daga haqarqarin Annabi Adam A.S na barin hagu aka
> farar da halittar Nana Hauwa'u.
>    Hakanan, baya da fifikon Namiji
> akan mace da Allah Ta'ala yasha bayyanawa acikin littafinsa
> Alqur'ani mai tsarki, wani sahihin Hadisi daga Abu Hurairata
> R.A yace Manzon Allah s.a.w yace" wanda duk ya bada gaskiya
> ga Allah da Ranar lahira kada ya cuci makwabcinsa, kuma ina
> yi muku wasiyya da ku kyautatawa mata domin su an haliccesu
> ne daga qashin qirji, haqiqa qashin qirjin da yafi
> tankwashewa shine na sama, idan kai nufin miqar dashi sai ka
> karya shi, idan kuwa ka barshi sai yaci gaba a karkacen. Ina
> yi muku nasiha da ku kyautatawa mata."
>     Duk wannan, Allah Ta'ala
> na nufin sanar da mutane cewa Namiji shine jagoran mace,
> mace zatayi masa biyayya, shi kuma ya tausasa mata. Wato dai
> ilimi ne aka saukar yadda zamu san kanmu, yadda idan matsala
> ta taso ba zamu rasa hikimar warware ta ba.
>   Mu dauki misalin Mutumin da ya
> sayo abin hawa, mota babur da sauransu. Idan wannan abin
> hawa nashi ya lalace, tabbas mai abin hawan ne zai miqa shi
> wajen gyara, domin abin hawan bashi da ikon zuwa don a gyara
> shi. Ana cikin haka, sai akayi sa'a, wani mai gyara ya
> koyawa wannan mutumi gyaran abin hawan. Yaya kuke tunani? Ai
> kuwa duk a inda wannan abin hawa ya lalace masa bazai rasa
> hikimar da zai gyara kayan saba tunda ya samu ilimin
> gyaran.
>    To ayau, Asalin tabarbarewar
> aure shine Rashin ilimi. Mutane da yawa basu san kansu ba,
> basu da manufar rayuwa a duniya ballantana su san irin
> abokiyar zaman data kamace su, su kuma san hikimar zama tare
> da wannan abokiyar zama. Amma duk da haka kuma, idan yayi
> aure, burinsa abokiyar auratayyar sa zatayi masa dai-dai da
> abinda ransa yake so.
>     Don haka, a gaskiya mun
> dade muna jahiltar kawunan mu. Ya kamata mu san cewa namiji
> da mace ba daya suke ba. Aikin su daban ne, manufar da Allah
> yake son su  cimma daya haliccesu shine Bauta, kowannen
> su kuwa yana bin hikimomi daban-daban don samun cimma waccan
> manufa, amma fa abin da wannan yakeso yasha bam-bam da
> abinda wancan yakeso. A taqaice ma zan iya cewa halittar dan
> Adam ta qunshi jinsin halittu biyu ne, wato halittar namiji
> da halittar mace, kawai dai munyi kama da junane, muna kuma
> rayuwa tare, kamar misalin Bacteria da Archea ga masana
> ilimin qananun halittu.
>     Saboda haka, batun ayi
> aure ace ba za'a samu matsala ba, wannan tatsuniya ce. Dole
> a rinqa samun sabani, shiyasa Hadisin Annabi s.a.w ya umarci
> namiji a matsayin sa na babba ya tausasawa wadda zatai masa
> biyayya wato mace, har ma akai mana hannun ka mai sanda
> wajen jagorancin cewa kada yayi amfani da ruwan zafi, kada
> kuma yayi jagorancinsa ta ruwan sanyi, wato dai anaso yayi
> sai-sa-sai-sa cikin hikima.
>    Kawai dai, ga duk mai son
> warware matsalar sa ta auratayya, ilimi ya kamata ya nema
> wanda ya shafi yadda Fiyayyen Talikai ya rayu da ahalinsa in
> yaso sai yayi hikimar warware tasa matsalar dai-dai da halin
> daya tsinci kansa. Akarshe, Rashin ilimi shine asalin
> tabarbarewar aure, neman ilimi kuwa shine magani. Ku huta
> lafiya. 

No comments:

Post a Comment