Monday, 11 December 2017

TARIHIN HAUSA A MAHANGA TA 2

Tarihin Asalin Hausa da Hausawa
  (Mahanga ta biyu)

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

  Wannan mahanga Dier Lange ne ya rubutata acikin littafin "African zion: Studies in Black Judaism'. Edith Bruder da Tutor parfitt ne suka fasalta shi, kamfanin 'cambridge scholars publishing' kuma yayi d'ab'insa a shekarar 2012.
   Mahangar ta ce:-
Da fari dai, an samu aukuwar wasu hijirori guda biyu daga sassan duniya izuwa yankin kasar hausa shekaru da dama da suka gabata. Hijira ta farko itace ta mutanen Kan'ana da falasd'inu, k'arkashin jagorancin Najib/Nimrod, daga baya kuma sai Abdul Dar sannan wasu sarakuna mata suka biyo su.
   Ance wadannan masu hijira ta farko, sun ratso ne ta kasar egypt, sannan suka keto ta Afirka ta arewa izuwa yankin sahara har izuwa tsakiyar sudan. A Wannan hijira akwai sarauniya Magajiya Daurama, itace kuma ta kafa garin Daura.
   Hijira ta biyu kuwa ita ce ta Bayajidda ko ace Abu yazidu dan Sarki Abdullahi na Bagadaza, wanda ya baro gida tare da wasu dakaru masu yawa izuwa masarautar Kanem-borno. Ance ganin irin karfin da Bayajidda ke tare dashi yasa sarkin Borno yayi dabarar aura masa d'iyarsa, daga bisani kuma sarkin yayi nasarar kwace ikon dakarun daga hannun sa tare da neman halaka shi, ganin haka yasa Bayajidda tserewa daga borno izuwa inda kasar hausa take a yau, tare dashi akwai matar sa mai d'auke da ciki juna biyu.
   Bayan wani lokaci sai matar tasa ta haihu d'a namiji, wanda aka sanya masa suna Biram. Daga nan sai akace Bayajidda ya barsu ya cigaba da tafiya har ya karaso Daura. Wurin daya barsu d'in kuwa sai ya zamo birni, wanda aka sanyawa suna 'Biram-ta-gabas'.
    Isar Bayajidda garin daura keda wuya sai ya hadu da wata tsohuwa mai suna Ayana, a kusa da wata rijiya. Bayajidda ya kashe wani katon maciji mai hana mutane d'ibar ruwa tare da daddatsa shi gunduwa-gunduwa, hakan kuma yasa daga bisani sarauniya Daurama tace tana sonsa da aure.
   Bayan ya amsa sunyi aure, sai ya kasance kuyangarta mai suna Bagwariya ta rigata haihuwa da Bayajidda, sunan dan data haifa Karba-gari, ko karaf-da-gari, wanda shine akace ya haifi 'ya'yaye bakwai wadanda suka samar da garuruwan banza bakwai, ita kuwa daurama daga bisani sai ta haifi danta mai suna Bawo, wanda shikuma akace ya haifi 'ya'yaye bakwai wadanda suka kafa garuruwan Hausa bakwai.
   Ance bayanan da aka samu daga masarautun Gobir, da marad'i, sun nuna cewa jarumin daya kashe wannan maciji gida bakwai ya rarraba shi. Bayanin daya fito daga masarautar zamfara kuwa cewa yayi sunan jarumin daya kashe wannan maciji 'kalkalu', kuma gida goma sha biyu ya daddatsa shi.
   Wannan abu sai ya tuna mana da ruwayar kafuwar daular Babylonia, wadda itama akace wai wani sadauki ne ya kashe wata macijiya mai suna Tiamat, ya daddatsa gangar jikin, daga nan kuma aka soma yin bikin tunawa da kashe wannan macijiya a duk shekara, bikin da akewa lak'abi da 'Mesopotamian Akitu', wanda yayi dai-dai da bikin 'Gani' na Daura, wanda shima akace ya samo asali ne bisa murnar kashe wannan maciji da Bayajidda yayi.
   A wata ruwayar kuma, ance Bawo ne sunan sadaukin daya kashe wannan maciji sannan ya auri Sarauniya Magajiya Daurama. Kuyanga Bagwariya kuma ta haifa masa d'a mai suna karb'a-gari, shikuma karbagari shine uban 'ya'yaye bakwai masu sunayen jihohin hausa.
   Watakila ana iya cewa an samu sab'anin ruwaya ne, amma dai malaman fulani a k'arni na sha tara irin su Muhammad Bello, da Abdul Qadir bn Mustafa suna d'aukar Bawo a matsayin shugaban jihohin hausa/daular hausa wanda akace Sarkin Borno ya nad'a. Littafin wakar Bagauda na tsohuwar masarautar kano mai d'auke da sunayen sarakunan hab'e na masarautar kuwa ya ayyana Bawo a matsayin wanda ya kafa k'asar hausa (ko ace wanda ya samar da k'asar hausa da jihohin ta).
   Allah ne masani.

No comments:

Post a Comment