TARIHIN HAUSAWA
(Mahanga ta hudu)
Wannan jawabi wani bature mai suna R. Sutherland Rattray ne ya wallafa shi. Shikuwa, ya amshi jawabin ne daga hannun wani bahaushe mai suna Mallam shehu, wanda suka had'u a yankin tafkin kwara inda baturen ke tsayawa don ya had'u da hausawa masu wucewa tare da tambayar su labarai, a wajajen shekarar 1913.
Labarin ya fara kamar haka:-
Da sunan Allah mai rahama mai jink'ai. Tsiran Allah da aminci su tabbata ga Annabi Muhmad (s.a.w), annabin da babu wani bayansa. Wannan shine labarin k'asar hausa wanda muka sani kaka-da-kakanni. Kuma labari ne wanda yazo daga hannun malamai da tsofaffi. Duk wata ruwaya sab'anin haka, bata inganta ba.
Idan mai tambaya ya tambayeka cewa 'daga ina Hausawa suka fito?' To kace masa ' maganar gaskiya, hausawa sun samo asali ne daga bare-bari da kuma mutanen Arewa'. Tsaya ma kaji yadda lamarin ya kasance.
Sarkin Borno yana da wani doki gawurtacce. Kunnuwan sa na azurfa ne (ko kuma ace walwali suke tamkar da azurfa aka yisu)
Sai ya kasance wannan dokin baya yin haniniya sai ranar jumma'a. Idan kuwa yayi haniniya, idan kaji kana iya cewa sarewa ake busawa don dadi. An b'oye wannan doki a wani gida babu mai hawansa.
To wannan Sarki yana da d'a. Sai ya kasance d'an sarkin yana baiwa mai tsaron dokin kud'i da kayayyaki kyauta, sai shi kuma ya fito masa da dokin ya gama su da god'iyar sa. Kullum haka ke faruwa.
Watarana sai wannan mai kula da doki ya fito dashi, shima d'an sarki sai ya fito da tasa god'iyar, suka shiga daji abinsu. Anan ne god'iya ta d'auki ciki.
To sarki kuwa tun a baya yayi shelar cewa kada wanda ya yadda dokinsa ya gamu da god'iyar sa. Idan kuwa aka samu wannan doki ya haihu, to sai an datse kan mai wannan god'iya. A haka wannan doka take.
Ana haka sai godiyar yarima ta haifi doki. Doki ya fara girma babu wanda ya sani. Wata rana sai dokin sarki yayi haniniya, sai kuma wannan karamin doki shima yayi tasa.
Ai kuwa sai karaf a kunnen sarki. Daga nan sai sarki ya bada umarnin a zagaya duk inda akaga wannan k'aramin doki, a datse wuyan maishi tun kafin azo gabansa.
Sai kuwa Fadawa suka bazama nema, gida-gida kurfa-kurfa. Har suka zo gidan d'an sarki. Abin mamaki sai ga dokin sarki da k'aramin doki wuri guda. Dawakan sunyi kama sosai. Sai fadawa suka ce da d'an sarki, 'Sarki yace dole muzo dakai.'
Yarima dajin haka sai ya zare takobinsa, kafin kace haka ya datse kawunan biyu daga fadawan nan. Ragowar kuwa da ganin haka sai suka arce da gudu. Daga nan sai d'an sarki yahau kan k'aramin dokin nan ya gudu daga garin.
Sarki yasa fadawa su bishi su kamo shi. Suka bi bayansa amma basu tarar dashi ba, ya tsere musu. Gashi kuma sarki ya hana kowa hawan wannan doki nasa, ba don haka ba, da ana iya tarar dashi idan aka haushi.
Wannan d'an sarki yayi ta tafiya har sai da yabar k'asar borno duka, daga bisani yazo Daura. Anan ne yaga d'iyar Sarkin daura ce ke mulki.
Watarana kuwa sai tace tana son ta aure shi, shima sai yace yana son ta da aure, sai kuwa sukayi auren su. Daga nan sai ta haifa masa d'a namiji, sai ta haifa masa mace, sai ta k'ara haifa masa namiji, sannan mace...Wannan shine asalin k'asar hausa.
Don haka Bare-bari da mutanen Daura sune asalin hausawa.
K'arshen wannan mahanga kenan.

No comments:
Post a Comment