Magance Matsalar Tsaro: Ya kamata a Sabunta darajojin Shumagabannin Gargajiya.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978
Assalamu alaikum.
Tun zamani mai tsawo daya gabata, shumagabannin gargajiya kadai garemu. Sune ke mulkin mu, sune kuma jagororin mu. Suke samar mana da tsaro, sune kuma ke juya tattalin arzikin kasashen mu. Amma a yanzu, wannan duk ya zamo 'tazo-muji-ta'.
Shin me zai sanya mu koyi da al'ummar da ita kanta bata da cijakkiyar zaman lafiya alhali muna da tarihi kyakkyawa? Tarihin Sarkin kano na farko Bagauda bazai gogu a tarihin kanon muba. Tunda shine wanda ya fara tsare kanawa daga mahara, ya samar musu da zaman lafiya gami da arzikin noma a iya shekaru sittin da shidda na mulkinsa, abin mamakin ma shine, lokacin ana tsaka da maguzanci. yayi haka ne kurum saboda dattako, kishin al'ummarsa da kuma tunanin abinda ya kamata ba domin tunanun lada ki hisabib ranar gobe kiyama ba.
Zuwan Bature wannan yanki bayan ya samu nasarar yaki da sarakunan mu sai ya bashi damar gudanar da mulkinsa a kasashen mu. Amma shi kansa, bai samu nasara ba sai daya bi ta hanyar sarakuna da sauran masu rike da mukaman gargajiya, saboda ya fahimci darajar su da tasirin su a zukatan mutanen dake yankin. Sannan yin hakan kuma, ina ganin kamar karimci ne garemu, domin kuwa ya darajanta abinda ya tarar kakannin mu suna darrajantawa.
Sai dai gashi, juyaear zamani tazo. Wadanda suka gaji wancan mulki na bature, sun sauka daga turbar daya wanzu akai. Sun sarayar da darajojin sarakuna, ba'a neman su sai idan ana neman warware fitintinu ko idan an kudunduno alluran riga-kafi. An bar su cikin k'anfa da babu, domin kuwa d'an alawushi kurum ake sammusu, ba suda hakkin karbar kasafi daga gwamnati tayadda zasu aiwatar da manyan aiyuka a yankunan su kamar yadda suke da ikon yi a lokacin mulkin turawa da kuma lokacin mulkin su Sardauna.
Abinda dai nake nufi a takaice shine, ya kamata ayi musu tsarin karbar (Grand) 'kasafin kudi' ta yadda zasu rinka bin diddigi tare da dakile matsalar tsaro tun tana kankanuwa, tare da aiwatar da aiyukan raya kasa kuma. Idan har za'a nemesu a lokutan bala'i, me zai hana a tuntube su a lokacin walwala? Ai Kowa yasan karfi na arziki. Yau ko uba ne ya kasa sauke nauyin zuriyar sa, sai kaga fad'a-ajinsa na neman dusashewa.
Don haka nake ganin, rashin martabasu da akeyi ta wajen hana su kudade masu kauri na daya daga cikin dalilan daya sa suke baya-baya da gwamnati. Akwai matsalolin da masu unguwanni ko dagaci kadai ya isa su magance idan suna da kudi. Tunda kowa yasan shari'a ta gaskiya Sai Allah, amma sasanci ake so a tsakanin mu. Misalin ace An tauye wannan anan, sai a bashi wani abu yayi hakuri, ko kuma gida kaza babu abinci sai a basu abinda zai ciyar dasu tayadda talauci bazai tursasa mutan gidan suyi abinda ba dai-dai ba wanda daga bisani zasu gunduri al'umma, a haka sai kaga an zauna lafiya.
A karshe ina yiwa wannan kasa tamu fatan cigaba da zamowa dunkulalluta, jagora, mai karfin tattalin arziki da kuma yalwar zaman lafiya. Allahumma amin.
Ku huta lafiya.

No comments:
Post a Comment