Wednesday, 27 December 2017

TARIHIN SIR AHMADU BELLO SARDAUNAN SOKOTO

5. SIR. AHMADU ƁBELLO SARDAUNAN SOKOTO

DAGA Sadiq Tukur Gwarzo RN.
  08060869978

 An haifi marigayi firimiyan arewa Ahmadu Bello a shekarar 1909  agarin Rabbar na gundumar Sokoto. Mahaifinsa Ibrahim Bello shine ke rike da sarautar Sarkin Rabbar, kuma jika ne ga mujaddadi shehu Usmanu ɗan fodio ta wajen ɗan Shehun watau Muhammadu Bello.
  Ahmadu Bello yayi karatun addini a gida, sannan ya tafi sokoto inda yayi makarantun boko acan.
 A shekarar 1931 bayan ya kammala karatu ya zamo malami mai koyar da turanci a makarantar Midil ta Sokoto.
  A shekara ta 1934 Sarkin Musulmi na lokacin Hassan Dan Mu'azu ya naɗa Ahmadu Bello dagacin garin Rabbar.
 A shekarar 1938 kuma aka kara masa matsayi a sarautance izuwa Dagacin gundumar Gusau wanda samu damar kasancewa ɗan majalisar sarkin Musulmi..
 Ahmadu Bello yana da shekaru 28  a duniya yayi yunkurin zamowa Sarkin musulmi bayan rasuwar Sarkin Musulmi Hassan Dan Muazu, amma bai samu dama ba, yayin da Sarkin Musulmi Abubakar Siddiq na uku ya zamo sarki wanda ya shafe shekaru 50 akan gadon sarauta.
   Sai dai, Sarkin Musulmi Abubakar na uku na hawa mulki, sai ya naɗa Ahmadu Bello Mukamin Sardaunan Sokoto, kuma babban mai baiwa sarki shawara.
   A shekara ta 1944 Ahmadu Bello ya shiga jam'iyyar siyasar nan mai suna 'Jam'iyyar Mutanen Arewa', wadda daga baya aka sauya mata suna izuwa 'Northern Progressive Congress', watau NPC. A shekarar 1948, Ahmadu Bello ya samu tallafin karatu na gwamnati, inda ya tafi Ingila karo karatu..
  Daga dawowarsa kasa Nigeria a wuraten shekarar 1951 sai aka zaɓe shi a matsayin ɗan majalisa mai wakiltar sokoto a majalisar Arewa, don haka sai ya dukufa aiki tare da sauran yan majalisu na sassan Arewa don ganin an ciyar da yankin Arewa gaba da kuma samar da zaman lafiya tsakanin kabilun Arewa.
  Abinda ya dukufa yi kenan har zuwa shekara ta 1952 da aka soma zaɓe a majalisar Arewa, inda Ahmadu Bello yaci,  ya zama ministan Aiyuka na yankin Arewa.
  A shekarar 1954 Ahmadu Bello ya zama firimiya na farko a jihar Arewa. A lokacin kuma shine shugaban babbar jamiyyar siyasa ta arewa watau NPC.
  A zaɓen 'yancin kai na shekarar 1959, Jamiyyar NPC da Ahmadu Bello ke shugabanta ce ta mamaye mafi yawan kujerun majalisar kasa, don haka sai tayi haɗin guiwa da  Dr. Nnamdi Azikiwe na jamiyar NCNC (National Council of Nigeria and the Cameroons) suka kafa gwamnatin tarayya ta farko wadda ta karɓo 'yancin kai daga hannun turawa a shekarar 1960.
  An nemi Ahmadu Bello a lokacin ya zama Firimiyan Nigeria, amma sai yaki, ya mika kujerar ga mataimakinsa Sir Tafawa Balewa, (wanda a baya shima ya sahale masa zamowa shugaban NPC domin samun goyon bayan talakawa da sarakunan Arewa kasancewarsa ɗan sarauta) shikuma Ahmadu Bello ya cigaba da zamansa a matsayin shugaban (firimiyan) Arewa, yayinda Dr. Azikwe yake rike da matsayin shugaban kasa.
Daga cikin manyan abubuwan da Ahmadu Bello ya kawowa arewa na cigaba, akwai haɗin kai da son juna gami da zama lafiya a Arewa, sai kuma kamfanoni irinsu Northern Nigeria Development Corporation (NNDC), Bank of the North da kuma Northern Nigeria Investments Ltd (NNIL).
 A karshe, an kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka jagoranta.
  Da fatan Allah yajikanaa Amin.

No comments:

Post a Comment