LABARIN BAWA DORUGU; BAHAUSHEN FARKO DAYA FARA ZAGAYA TURAI.
Kashi na uku
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Na jima kadan, sai Babana ya zaga yana nemana daga cikin ciyawa. Ya kirani ina jinsa amma ban amsa ba har sau biyu kana na amsa. Yace mani babu komai sai lafiya, nace idan lafiya to mutafi gida. Da muka isa gida nayi zamana amma zuciyata bata zauna ba. Na cewa matar ubana (sunanta Baka, amma ba uwata ba, ubana ya fada mani cewa ya aure tane tun yana saurayi ita tana budurwa amma bansan me ya fitar da ita ba, amma ina tsammanin ta shiga bauta ne don tana yin maganar bare-bari. Ita ya kawo ya ajiye a gidanmu kamar uwata). Nace mata ki dauki kwarinki ni kuma na dauki kibiyata da malafan ubana mutafi wani gari. Sai taji maganata, bata raina niba. Muka tafi tana gaba ina binta a baya. A lokacin kuwa ina dan shekara sha daya, har muka ketare ruwa, a lokacin kuma ubana baya gida, ya tafi wurin mutane yana jin labari.
Da yaje gida bai same muba sai yayi gudu yabi sawunmu har ya iskemu ya maishemu gida. Amma zuciyata na raurawa.
Da muka jima kadan a gida, ubana ya fita, sai muka ga wani mutum bisa doki amma shi ba bahaushe bane ya shigo, tare da wani mutum mai tsagun bare-bari. Suka ce suna son hatsi saboda dokin bare-barin. Yana yin maganar borno matar ubana na mayar masa. Idan yayi maganar Borno nakan tambayi matar ubana me yace? Tace mini yana son hatsi ne. Nace masa bamu da hatsi, amma yace zai kira samari su shiga dakinmu su duba, anan sai na tsorata.
Muna cikin haka sai mukaji sarkin borno Shehu Umar na tahowa izuwa garinmu, da marece rana ta kusa faduwa kasa, mukaji wani mutum yana zagayawa yana shela yana cewa kowanne bako ya daure sirdinsa, yahau bisa dokinsa. Mukaji busar Sarki, kotso da algaita da kalangu da kube da ganga suna yi masa kidi. Sarkin yana da tuta babba. Da suka buga bindiga sai kowanne bako ya shiga kama mutanen gari a matsayin bawa, amma sai ubana yayi min magana cewar na zagaya wajen wata kofa. Amma kaina ya gigita, ban san me yake cewa ba har mutumin borno dake cikin gidanmu ya kamani. Ubana kuma wani bahaushe ya kamashi amma ban san wanda ya kama matar ubana ba.
Cikin gari fa duk ya rude, yara duka sai kuka, uwa ta rabu da 'ya'yanta, miji ya rabu da matarsa. A haka duk muka watse. Wanda ya kamani ya kama dokinsa da hannu yana jana. Har muka fita daga cikin gari, qaya ta soke ni kafata duk jini, ya hau bisa doki ya daukeni ya ajeni ga bayan doki. Akwai wani yaro abokina dake bisa dokin ubangidansa, ina zance dashi. Nace masa ka gani yanzu mun shiga cikin bauta ko? Yace mani bamu iyayin komi sai dai aikin Allah. A haka har muka karasa sansani.
Da nayi waiwaye haka, sai na hango matar ubana tana bin wani mutum da wuka a hannunsa, ya tafi gaban Sarkinsu da ita. Ni kuma kafata tahau jini da kaikayi, suka kawo mana gujjiya suka ajiye a gabanmu, amma bamu ciba, domin babu yunwa a tare damu saboda zuciyarmu bata jin dadi. Da suka wawushe garinmu sai kuma suka banka masa wuta. Kwan kaji yayi ta fashewa, ji kake bus kamar bindiga.
Suka daukemu suka kaimu ga sarkinsu ya ganmu duka. Sannan suka kaimu muka zauna. Wannan shine mafarin Bauta ta.
Idan da munsan zasu kamamu da mutan garinmu sunyi fada sosai dasu, amma sai suka bimu da wayo. Muna da kibbau masu dafi da zafi, idan dai mutum ya lasa sai ya mutu. Idan da munyi fada dasu da sai mutanen mu da nasu masu yawa sun mutu, amma sai gashi babu fada sun kama mu kamar 'ya'yan kaji, gasu da asiri. Sai dai ban saniba ko wani ya mutu dan garinmu ko a nasu bangaren.
Zan iya tunawa, mutanen dana gani sun kama basufi dari biyu ko uku ba. Sai dai a tsammani na ko sun aike da wadansu cikin dare. Mu dai anan muka tafi tare dasu, muka wuce wani gari kusa da garinmu, suka dauki mutanen garin, ina tsammanin sunyi dari hudu, muka tafi tare dasu suka qona garinsu, muka tafi izuwa wani babban gari, muka kwana anan, da safe suka daukemu muka zaga ta garin kakata mai suna Kunduwoshe. Na hango kakata tana tsaye a gefen gidanta, data ganoni saita ganeni, jikinta ya soma raurawa, ta tambayeni tace Ina Adam? Nace ban sani ba, sai na daga mata hannu nace mata sai wata rana, na wuce inayin kuka. Daga nan sai muka zaga ta Zinder.
MUN TAFI BORNO
Muka zaga ta zinder, ana muka zauna kwanaki dayawa. Da akwai wadansu da aka aike dasu ga borno, naji labarin ubana, Sarkin Zinder ya bashi 'yanci, ya kuma ce masa ka tafi ka nemi danka, idan ka sameshi kayi tafiyarka garinka dashi. Ya dauki dundufansa yana yin kidinsa domin idan najiyo dundufansa zan ganeshi.
Amma najiyo kidi daga cikin gari kamar hannunsa, sai dai bani da ikon fita waje daga gidan da aka ajiye mu. Sai dai idan zamuje baiwa dawaki ruwa ne. Dana zauna daga cikin gida, bayi da suke daga ciki na ubangijinmu suka tafi dauko ruwa sai suka gamu da ubana daga can yana kwance karkashin dutse kusa da hanyar ruwa, sai ya tambayesu (kunsan duk garinmu daya sunsan juna dashi) ina Dorugu? Suka ce yana gida, mun kirashi amma bai jimu ba don haka muka fito diban ruwa banda shi.
Da suka dawo sai suka ce mini Dorugu yau munga Ubanka yana kwance a hanyar ruwa yana jiranka, nace musu don me baku kiraniba? Sai sukace mini saida muka kiraka baka jimuba.
#SadiqTukurGwarzo

No comments:
Post a Comment