Monday, 11 December 2017

TARIHIN HAUSA A MAHANGA TA 3

TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA: Alak'ar hausawa da yahudawa
   (Mahanga ta uku)

  Daga Sadiq Tukur Gwarzo

  Dier Lange ne ya rubuta wannan mahanga a littafinsa mai suna 'African zion; studies in Black Judaism'.

    Daga abubuwan da maruwaitan tarihi suka kawo, muna iya hasashen asalin hausa daga haduwar wasu al'ummatai guda biyu, watau asalin mazauna yankin, da kuma wadanda suka yo hijira daga baya.
   Hujjoji mabambanta, sun alak'anta yahudawa a matsayin al'ummar da suka yi hijira daga garuruwan su izuwa kasar hausa bayan karyewar Daular Babylonia, saboda rikice-rikice da suka rinka aukuwa a k'asashen su.
   Hujja ta daya itace: Sunayen sarakunan Mulki na kasashen sudan ta tsakiya nada alak'a ko kamanceceniya da sunayen yahudawa.
 Misali;
Daular kanem_Borno
 Sunan 'Bulu' wanda akace shine ya jagoranci tawagar data riski yankin na kanem yayi kamanceceniya da sunan 'Nabopolassar'
Haka ma  sunan sarkin kanem 'Arku' na kama da 'Assur'.

Daular Oyo
Sunan 'Majeogba' na kama da Mushezib
Sunan 'Abiodun' na kama da Nabopilassar
  Masarautar Daura
Sunaye takwas na sarakunan mulki na farko wadanda suka biyo bayan Abdul-Dar, sarkin da ake cewa bayahude ne jika ga Lamarudu sunyi kamancecenita da sunayen Yahudawa.
  Kamar 'Hazo' na kama da Ahaziah.

  Masarautar Gobir (yankin sakkwato a yau)
Sunan Gobir ma kacokan na iya samo asali ne daga 'surukul ko Gubur', sunan da ake lakabawa wani yanki dake can gabashin garin makkah.
  Idan kuwa ba haka ba, watakila ya samo usuli ne daga bayahuden sarkin nan Bit al Gabbar, wanda shima tana iya yiwuwa isar sa gobir yasa ake kiran wurin da sunan sa.
   MaSarautar Biram (Hadejia a yau)
Biram tsohon birnin hausa ne da aka ce ya wanzu kimanin kilomita 180 a arewa maso gabashin kano, itama sunayen sarakunan ta sunyi kamanceceniya da sunayen yahudawa. Biram din kanta yafi kama da Abraham, haka sunan Bomu na iya zuwa daga B.m.h ne, sunan wani daga cikin 'ya'yayen Bit al Gabbar.
  KANO
Littafin tarihin kano ya nuna cewa ana kiran wanda ya kafa Kano da Bagauda ko kuma Da'ud/David. Kuma ance ya riski Dirani/Dora (sunan da yayi dai-dai da sunan gabar tekun tsohuwar palasdinu), Barka (watakila cyrenaica ne ainihin sunan) da kuma Birnin Saul (sheshem) kafin ya iso kano.
  Watakila ma, Bagauda na iya zamowa daga 'Mutumin Gath', wanda zamu iya hasashen ko shine sarkin yahudawan nan daya zauna a Gath.
   Haka kuma sunayen sarakunan da suka gabace shi, duk na kama dana yahudawan. Misali, Warithi na iya zamowa daga Solomon,  Gijinmasu na iya zamowa daga Moses, Gawata da Nawata da iya zamowa Magog da Gog, yayin da Yusa ke iya zama Josua.
  Hujja ta Biyu itace ta bautar gunkin Cukanal/Shekhinah wadda ta wanzu tsawon lokaci a kano har sanda fulani sukayi jihadin su, da kuma bautar gunkin Mune a yankin Kanem-borno. Dukkan wadannan sunyi kamanceceniya da bautar gumaka da yahudawa jikokin Lamarudu sukayi tun a wancan lokaci.
   Hujja ta k'arshe kuwa itace ruwayar wasu matubuta da suka hadarwa Al yaqubi na wanzuwar wasu al'karyar yahudawa a cikin kasar ta hausa, inda ma har wasu ke hasashen Sunan hausa ya samo usuli ne daga Sunan wani Sarki Bayahude mai suna Hoshea, ko kuma ya samo asaline daga kalmar 'Haloshan', kalmar dake nufin 'yare ko harshe' a yaren yahudanci.

No comments:

Post a Comment