BAKAN DABO: TUNAWA DA MARIGAYI MAI-MARTABA ALHAJI ADO BAYERO.
(Dubu Jiran Mutum Daya)
Fitowa ta Biyu; Yadda Ta auku a fada bayan Shugabar Alqalai da Alkalin kotu sun gurfana a gaban sarki.
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
Babbar maishariah ta kasa justice Maryam Aloma Muktar ta bayyana a fadar mai martaba sarkin Kano, Alh Dr AdO Bayero CFR LLD JP, dubu jiran mutum daya, domin amsa kiran sarki. Atare da ita akwai babban
Alqali mai shariah na kotun data tura sammaci ga mai-martaba Sarki. Ance sunan sa Justice SamueL Egbedi.
Wani Marubuci lamido, ya ruwaito mana cewa; Alokacin da suka isa fadar, Mai martaba san kano dan abdu, yana harde akan gadon sarautarsa sanye da kayayyaki na alfarma kamar yadda ya saba a koda yaushe, gami da wani bakin tabarau a fuskarsa, ance fuskar sa babu walwala. Marigayi mai girma
Galadiman kano Alhaji Tijjani Hashim na
zaune a kasa dab da karagar sarkin. Yayinda sauran yan majilisar sarki ke zaz-zaune a mazauninsu, kowannen su ya natsu don jiran umarnin mai-martaba Sarki.
Justice Maryam wadda ta rufe jikinta rujuf da wani hijabi babba, ta taso daga inda take ta zube a gaban mai-martaba sarki Ta kwashi gaisuwa sannan ta Koma ta zauna, shima Alqali Samuel yayi irin yadda yaga Shugabar tasa tayi, yaje ya zube ya kwashi gaisuwa amma ance
sarki ko kallansa baiyiba balle ya amsa
masa.
Fadar Sarki dai tayi shiru har tsawon kimanin mintuna goma ba abinda kakeji sai kirarin dogarawan sarki. Ga abinda ma akace suke fadi;
'Hucewar ka lafia mai Kano,
lafiya alkalin alkalan Nigeria,
Lafiya sarki me hukunta masu hukunci, hucewarka lafiya magajin dabo,
Ayi kurum."
Allahu Akbar !
Daga nan sai aka umarci justice maryam da ta gabatar da jawabinta. Alqalan Alqalan nigeria Mai shari'a JUSTICE MARYAM ta fara jawabi kamar haka: "Assalamualaikum Allah ya taimaki
Sarki ya karawa sarki lafiya da imani, nazo wannan fada mai daraja domin amsa
kiran sarki, ajiya ne na dawo daga kasar England domin kammala hutuna
na karshen shekara, awa na hudu da sauka sai na samu kiran waya
daga Sakataran gwamnatin tarayya Dr
Anyim cewa sarki na nemana a fada, sai nace masa yallabai lafiya kuwa? Domin
nasan cewa in sarki na nemana mai dakin mataimakin shugaban kasa ke
sanar dani, amma sai Dr anyim
yace mini ai ba lafiya, saboda Yaranki sun vallo miki ruwa, sun jajubo miki tashin hankali domin kuwa sunyiwa mai
martaba sarki rashin kunyar cewa wai ya
gurfana a gabansu, sai nace Innalillahi
wa'innaillaihir raji'una, nashiga uku ni Maryamu.." Ance adai-dai wannan lokacin akaji fada ta rude da dariya har shi kansa Mai Martaba sarki, sai da akaga yana murmushi.
Daganan Justice taci gaba da cewa "Babu shiri nakira wanda ya jika mana. wannan aika-aika wato Samuel
Egbedi, nace kana ina? yace wai yana
airport zai tashi zuwa Dubai, nace masa uban Dubai zaka ba Dubai ba, bayan ka vallo mana ruwa shine zaka zame ka barmu aciki to maza ka zo yanzu mu tafi Kano domin gurfana a gaban sarki. To, ranka ya dade gashi mun amsa
kira munzo. Akarshe, amatsayina na 'Yarka Maryam, mai biyayya agareka, ba Chief Joji ba, ina neman afuwa, tuba
muke, Allah ya huci zuciyar Sarki, shikuma Samuel zamu zartar masa da hukuncin da sarki ya umartar ai masa Nagode, Salamu alaikum."
Daga nan, sai fada ta qara yin shiru, aka shiga dakon bayanin shugaba, bijimin sarki, mai yi don Allah, Mai-martaba San Kano Alhaji Ado Bayero.
Bayan wani dan lokaci, sai mai martaba Sarki ya fara nasa jawabin, ga abinda aka ruwaito yana cewa "Assalamu alaikum muna godia ga 'yarmu Maryam a bisa kauna da soyayyarta a garemu da
kuma jajirce-warta akan gaskiya. Allah
yayi miki jagora. Sannan muna horon Alkalai dasu kasance masu adalci
da girmama masu girma. Su kasance
masu gaskiya da rikon amana, su daina amfani da kujerunsu suna zalintar talakawa, Alkalai su guji yin fariya, su guji karvar cin hanci da rashawa. A karshe muna umartar babbar kotun daukaka kara ta qasa data sabunta ginin masallatanmu na juma'a guda biyu dake
jami'o'in Bayero anan kano, Galadima da
Jarma zasu bi diddigin aikin su tabbatar an farashi nan take. Wannan umarnine ba shawara ba muna fatan Allah yamaida
manyan Alkalanmu gida lafiya. Salamu
alaikum."
Daga nan, sai marigayi Mai Girma Galadiman Kano Alh. Tijjani Hashim ya kalli justice Maryam yace "wannan shine
SamueL Igbedi din?" Tace "Eh- shine ranka yadade."
Galadima ya kalli egbedi, ya juya harshe izuwa turanci yace: "My lord kenan, kozaka iya gayawa fada wane matakine dakai a karatun shariah?"
Samuel egbedi yace: "Degree na uku ranka ya dade."
Galadima yace "a wace makaranta kayi?"
Samuel: yace "a makarantar Nsuka."
Galadima: ya qara cewa "A wace jaha kake?"
Samuel: yace "a Jihar Ogun."
Galadima yace " Local Govt nawa kuke dasu?"
Samuel yace "Ranka yadade guda 16".
Galadima: yace "Sarakunan gargajiya nawa kuke dasu?"
SamueL yace "Guda 8 ne."
Galadima yai murmushi, sannan yace "to yanzu kana wacce jihane?"
Samuel yace " Jihar kano yallabai".
Galadima: "local Govt nawa muke dasu a kano?"
Samuel "guda 44 ne".
Galadima: "Sarki nawa muke dasu a kano?"
Samuel "Ranka ya dade guda 1 ne kawae."
Galadima " galadima nawa muke dasu?"
Samuel: "kaine kawai ranka yadade".
Kunji fa. Allah Sarki, marigayi Galadiman kano kenan Alh tijjani Hashim
shugaban majalisar ladaftarwa ta fadar
kano, ruwan sama zane nagida zane na waje.
Daga nan sai Galadima ya dubi Justice maryam yace "wannan fada na umartar ofishinki daya maye gurbin Justice SamueL Igbedi da wani Musulmin shugaba mai adalci. Wannan mataki ya
biyo bayan rashin kunya da rashin
girmama Sarki da Samuel yayi kuma saboda muna fatan wannan hukunci zai zamo darasi ga sauran Alkalai irinsa."
Ance Angano Justice Samuel yana kuka yana neman afuwa amma galadiman yayi banza wofi dashi. Babu jimawa kuwa aka tsigeshi, tare da maye gurbinsa da Justice Muktar sakamakon umarnin da fadar marimayi maimartaba sarki ta bayar.
Haqiqa munyi rashin jagora, mai kishin musulunci da son talakawa.
Allah ya gafarta Masa, ya Raham-sheshi. Amin

No comments:
Post a Comment