Labarin Dorugu, Bahaushen Daya Fara Zagaya Turai
Kashi na goma sha daya
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa" naje Na kwanta, ban jima
ba bacci ya kwasheni. A jirgin nan muka kwana daya.
Da rana ta fito INA ganinta tana fitowa daga cikin gulbi.
Can kusan marece muka isa ga garin Malta. Muka
shiga cikin garin bayan mun sauka daga jirgin, muka
shiga wani babban gida. Da muka ga gidajen malta dani
da Abega mun cika da mamaki, domin gidaje ne masu
kyawun gani. Hanyarsu a share, kasuwan su kuwa da
muka gani bamuso mukara dubata ba, don ta sanyamu
ruwan ido, ga abubuwan siyarwa da yawa, bazan iya
fadin abin da ke cikin kasuwar ba don komi sabo ne
gareni.
A garin mune Muke yanka kaji Idan zasu kawo mana
muci, don bama cin yankansu da sauran naman da ba
mune mukayi yankan sa ba. Abdulkarim ya kaimu gidan
sarkin garin, gida ne duk a share ga manyan dakuna ko
INA ka duba tsaf-tsaf yake.
Mun zauna a Malta kamar kwanaki biyar muka zaga ga
wani jirgin mai cike da mutane. Muka Shiga ciki, sai da
mukayi kwana uku muna tafiya a saman ruwa sannan
muka isa wani gari Wanda banji sunan saba, domin ni
kurma ne ga mutanen jirgin, bana gane me suke cewa.
Muka zauna a wannan garin, muka Shiga wani gida
kayatacce, aka bamu abinci mukaci, muka zauna
hutawa har dare yayi. Da Daren ne mukaji rugugi da
yawa yana matso mu, Sai Abdulkarim ya dauki
jikkunansa yayi wajen wani daki, yace muma mu
biyoshi. Muka kuwa bishi abaya da gudu, haka muka
shiga daki mai duhu muna rige-rige da sauran mutane.
Da muka Shiga kuma nan ma naga akwai mutane a
ciki, bamu Dade ba da Shiga muka ji dakin ya fara
tafiya damu kamar ana turamu.
Mukayi ta mamakin meke turamu dani da Abega, har
yana cewa dawakai ne ke turamu. Sai da gari ya waye
muka sauka a wani gari mai kyawun gaske, Na tambayi
Abdulkarim sunan abinda muka hau jiya da sunan garin
da muka zo yanzu. Shine yace "sunan abinda muka hau
jiya 'dokin Victoria' (jirgin qasa), nan garin kuwa sunan
sa LONDON".
Gidan da muka sauka mashigi ne, Don mutane masu
tafiya ga wani wuri suna sauka ga gidan. A kasar mu
babu iron wadannan gidajen, idan bakin sun sauka a
gidan, sai su shiga cikin gari idan sun samu wani gidan
acan sai suzo su dauki dukiyarsu sukoma can. Dakunan
su duk a rataye da karau-karau, idan kana son ka kira
Bara, sai kaja karaurawa, bada jimawa ba zaka ga
saurayi yazo maka yana tambayar ka me kakeso. In
zasu ci abincinsu suna buga babban kuge, da kowa da
yaji sai kaga ya taho wajen cin abinci.
Wajen cin abincin kuwa babban teburi ne, tsayinsa yayi
gaba uku, a saman suna shimfida farin alkamura,
sannan kaga an jera a kushin abinci da wukake a gefe
da cokula. Mazan London basa son suga matamsu Na
wahala, da mace ta yanke da wuka ko ta buge
hannunta zakaga mijinta ya rude yana fadin "
masoyiyata me ya sameki?" Idan kaga abin ba zaka Iya
boye dariyar kaba. Idan kuwa kayi dariya suna cewa
kana da rashin kunya.
Bayan cin abinci, mata suna fita izuwa wani babban
daki da yafi kowanne Girma, dakin da mutane ke
taruwa kenan. Samari kuma susha giya sannan su tafi
dakin taro wurin 'yam mata su samesu suna yin rawa
ga wani makidi muryarsa kamar sarewa. Makidan suna
da littafi mai rubutu a gabansu, suna yin waqa suna
wargi...
Sai Na rasa dalilin Daya sa mu mutanen afirka, maza
basa cin tuwo tare da matansu, sai dai idan mata ta
gama tuwo ta kawowa mijinta, idan tare yake da
abokansa Suci tare, in sun gama ya kirata ta dauke
kwanon. Amma su London kowanne maigida da mata
tasa take cin abinci har ma da 'ya'yansu"
Shafin Hausa kokarin ilimantar da al'umma akan fannonin ilimi mabanbanta da suka shafi Tarihi, Kimiyya, Falsafanci da makamantansu.
Sunday, 10 December 2017
LABARIN BAWA DORUGU 11
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment