Monday, 11 December 2017

TARIHIN SHEHU MUSA 'YARADUA

TARIHI: GUDUNMUWAR ZURIYAR MARIGAYI ALHAJI MUSA 'YAR ADUWA GA CIGABAN NIGERIA.

Daga Sadiq Tukur Gwarzo
08060869978

1. SHEHU MUSA 'YAR ADUWA
An haifi Marigayi Alhaji shehu Musa 'yar Adua a ranar 5 ga watan maris na shekarar 1943, shine Yaya ga Marigayi Shehu Musa 'yaradua, tsohon shugaban qasar Nigeria, kuma shine mahaifin Murtala 'yar Adua Tsohon ministan tsaron Nigeria.
Mafinsa, Marigayi Alhaji Musa 'Yar adua, matawallen katsina, ya kasance tsohon malamin makaranta, bafillatani, mutum mai amana, wanda ya taba zama ministan babban birnin tarayyar Nigeria a jamhuriya ta farko (a lokacin fadar gwamnati na Lagos) na tsawon shekaru tara, watau daga shekara ta 1957 izuwa 1966.
Marigayi Shehu Musa 'yar adua, yayi aji daya da Shugaba Muhammadu Buhari a makarantar katsina provincial School, wadda yanzu ake kira da Government college Katsina, anan ne ya samu nasarar cinye jarrabawar daukar sojoji, inda aka dauke shi a matsayin soja a wancan lokaci tare dasu Buhari da wasu manyan mutane a qasar nan a wajajen shekarar 1962. Daga baya akace saboda qwazon daya nuna, aka turashi qaro karatu a ingila, can wata makaranta mai suna 'Royal Military Academy'.
A shekarar 1964, marigayi Shehu 'yaradua ya dawo nigeria daga qasar ingila yana da muqamin second lieutenant, inda aka aikashi qasar Inugu aiki a qarqashin shugabancin kanal Adekunle fajuyi. Ance a lokacin yaqin basasa, shehu 'yar adua ya zamo kwamandan wata bataliya wadda take aiki bisa umarnin Marigayi Janar Murtala Muhammad. Shine har wani labari yazo cewa Shehun ya taba jagorantar wani harin sunquru ga sojojin biafara don karbe iko da jihar Onicha wadda alokacin sojojin biafaran suka mamaye. Amma cikin rashin sa'a, sai sojojin biafaran sukayi luguden wuta akan wannan runduna, ciki kuwa harda marigayi shehu 'yaradua domin yana ciki. Wannan abu yayi sanadiyar mutuwar daukacin wadannan dakaru, qalilan ne suka sha da qyar, ciki harda Jagoranta Shehu yaradua.
Bayan an kammala yaqin basasa, janar Murtala ya amshi shugabancin qasa a wajajen shekara ta 1976, sai ya nada shehu Yaradua a matsayin ministan zirga-zirga. Wanda kuma aka dorawa alhakin rage cunkoso a babbar gabar teku ta lagos. A wannan lokacin ne gwamnati tayi wani yunquri na bada kwangilar siminti har Ton miliyan sittin wanda za'ayi amfani dashi don giggina barikokin sojoji a fadin qasar nan. Sai dai daga baya gwamnati taga cewa babu isasshen wurin da za'a ajjiye simintin a gavar tekun, shine akayi shawarar rarraba kayan izuwa sauran tashoshin ruwa da ake dasu, inyaso sai a qara gina sabuwar tashar jirgi a Lagos. Sai dai kafin wadannan aiyuka su tabbata Allah ya qaddara rasuwar Janar murtala muhammad.
Da hawan Janar Obasanjo kan karagar mulki kuma, sai aka canzawa Shehu yaradua wurin aiki, inda aka qara masa muqami izuwa shugaban ma'aikata, aka kuma dorawa ofishinsa alhakin samar da abinci wadatacce a wani shiri da aka qirqiro mai taken 'Operation Feed the Nation OFN'.
Babban abinda shehu Yaradua ya duqufa dayi a lokacin shine samar da wadataccen takin zamani ga manoman Nigeria, hadi da irin noma ingattacce. A lokacin sane aka siyo kayayyakin noma na zamani wadanda suka hadar da motoci, injina da sauran na'urori, aka rarrabasu lungu da saqo na qasar, sannan aka dora alhakin koyarda hanyoyin amfani dasu ga manoma a hannun matasa masu bautar qasa. Wannan abu yayi silar qara danqon zumunci a tsakanin matasan sassan qasar nan da kuma manoma na wancan lokaci, sannan ya cusa sha'awar yin noman a zukatan 'yan qasa.
Daga baya, Shehu Yaradua ya jagoranci harkoki gami da tsare-tsare na ganin an ciyar da talaka gaba a lokacin mulkin farko na shugaba Obasanjo. A lokacin sune aka qirqiro qananun hukumomi, aka kuma yi musu tsari wanda kai tsaye zai rinqa tava talakan dake qasa. Wannan tsari kuwa har yau ana cin moriyar sa, domin masana sun tabbatar da cewa gwamnatin qaramar hukuma tafi kusanci da talaka fiye da kowacce gwamnati a qasar nan.
Baya da haka, ya taimaka matuka a loacin mulkinsu don ganin an gudanar da zabe na farko a Nigeria. Domin kuwa a shekarar 1979, gwamnatin soja dasu Shehu yaradua ke jagoranta a qarqashin janar obasanjo suka miqa mulki a hannun farar hula na farko, Alhaji Shehu Shagari bayan an gudanar da zabe. Don haka tunda anyi zabe kuma an danqawa farar hula mulki, sai Janar shehu musa yaradua ya ajjiye kaki, ya koma gida a inda ya fara gudanar da kasuwanci. Amma tafiya batayi nisa ba, sai kuma ya sanya rigar Siyasa a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida, kasancewar sa mutum ne mai son ganin komai ya tafi dai-dai a wannan qasa.
A lokacin ne marigayi shehu Yaradua ya zama dan majalisa mai wakiltar mazabar katsina, sannan dashi da Marigayi Ibrahim dasuki, da wasu manya suka kafa qungiyar siyasa mai suna 'Consensus/Democrat Group' a shekara ta 1987. Koda yake daga baya qungiyar ta rushe inda aka maida makwafinta da wata babbar qungiya mai suna 'Peoples Front'. Mambobin wannan qungiya sune;- Babagana kingibe, Abdullahi Aliyu sumaila, Ahmad Rufa'I, Yahaya Kwande, Ango Abdullahi, Sabo Bakin zuwo, Babalola Borishage, Rabiu musa Kwankwaso da kuma Abdul'aziz Faruk. Wannan qungiya tana cikin jam'iyyar SDP, jam'iyyar data samu nasarar lashe kujeru masu rinjaye na zaben 'yan majalisu da aka gudanar fiye da jam'iyyar NRC.
A haka dai lamurori suka wanzu sauyawa, Marigayi shehu yaradua yana ta fafutikar wanzar da mulkin demokaradiyya na adalci a qasa, yana kuma cin karo da cikas kala-kala. Hakika Abubuwa marasa dadi sun auku wadanda yayatasu bashi da alfanu, amma dai daga qarshe an daure Marigayi Shehu Musa yaradua tare da Janar obasanjo a gidan kurkuku na qiri-qiri, a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha har na tsawon shekaru hudu, inda a qarshe Allah ya amshi ransa ranar 8 ga watan disanba na shekarar 1997.. Allah ya jiqansa.
Haqiqa, za'a jima ana tunawa da Marigayi Shehu Musa 'yaradua saboda jajircewar sa gami da yin yaqi domin kare haqqin talaka. Ya sadaukar da rayuwar sa alokacin yaqin basasa don ganin nigeria ta zamo qasa daya dunqulalla. Ya qirqiro hanyoyin da gwamnati zata rinqa tallafawa talakawan ta. Yayi fada da tsoffin abokanan sa sojoji a lokocin dayayi ritaya don ganin mulkin siyasa ya dore a wannan qasa. Shine kuma shugaban kwamitin gina babban masallacin jumu'a na tarayyar abuja har lokacin mutuwarsa. Ance saqon sa na qarshe daga kurkuku ya fito ne a shekarar 1995, inda yake cewa "Kada ku damu sosai dani, wannan abu sadaukarwa ce daya kamata wasun mu suyi domin 'yantar da qasarmu.."
Allah ya jiqansa. Allah ya gafarta masa. Allah ya kyautata namu zuwan. Amin
#‎Dg‬ Sadiq Tukur Gwarzo

No comments:

Post a Comment