LABARIN DORUGU, BAHAUSHEN DAYA FARA ZAGAYA TURAI
Kashi na Goma
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa "Da muka bar garin nan,
muna tare da mutum uku ko hudu don Abdulkarim yana
kan rakuminsu, idan sun kaishi garin da yake so zai
biya su sai sukoma ga garinsu. Dayansu kuwa yaro ne
gwanin harbin bindiga, a kowacce rana ina tsammanin
yana kashe barewa daya ko biyu, amma bai kashe dila,
don sun fishi wayo.
Da suka kai mu garin da zasu kaimu, sai suka sace
zanena, daga rannan na sani larabawan nan beraye ne,
idan kana tafiya da rana idan kai mai wahala ne, idan
kaso kayi barci abinka da rana, da dare kuwa sai kayi
hankali da kayanka ko kuwa su yanke maka wuyanka
kamar yadda sukewa kaza. Su mutane ne masu zalunci,
idan ka basu kadan zasu nemi kari, gasu marowata,
idan sun sami abinsu suna ja nesa daga gareka.
Tun da muka barsu, muka isa wani gari na mance
sunan sa. Anan aka sace min tasa. Daga nan sai gamu
a Tarabulus. Amman kasuwar Tarabulus tafi kasuwar
duka dana gani kyau, mutane da yawa suna cemin
zakayi tafiya cikin rairayin nan? Nace musu "I". Suka ce
bazaka kara ganin wani gari ba, nace "bana tsoro". A
garin akwai hausawa da mutanen borno, anan
Abdulkarim ya siya mana sabbin riguna dani da Abega.
Gajeriyar rigace amma daga wuyan rigar har kasanta
maballai ne na farin karfe, in ka gansu kamar zinare, ya
siya mana hula mai kyau Ja da wando. Mukayi ta
murna a rannan.
Amma hausawan dake garin nan suna son komawa
kasar hausa, sai dai basu da kudi, wasu kuma da yake
bayi ne, idan sun samu kudi suna boyewa, in sunyi
yawa sai su fanshi kansu. Bansan girman Tarabulus ba,
amma cike yake da gidaje masu tsawo, mun shiga
masallacin garin, shima yana da kyau sosai.
Da muka kwana kamar biyar anan, sai muka shiga jirgin
ruwa. Sunan sa jirgin hayaki. A kasansa akwai dakuna
da wurin barci. Nace wanga gari guda ne. Da muka
jima kadan, sai mukaji jirgin na kururuwa kamar zaya
hademu, ko ina na jirgin yahau motsi, mukace yau mun
shiga sabuwar duniya.
Da jirgi ya fara yin tafiya, sai nacika da mamakin meke
tunkudashi? Ga ruwa ya koma fari duka. Daga nan sai
Abega yace min mudan zagaya mana. Nace masa to.
Muka shiga zaga cikin jirgi, har muka hadu da wasu
yara biyu masu maganar hausa, amma bayi ne, na
tambayesu ko su kadai ne? Suka ce a'a, suma za'a tafi
dasu Santambul be. Nayi murna don na samu masu
maganan hausa, amma naji tausayi don bayi suke.
Dayansu yace da Abega "wanga aikin tuka jirgi na
muhammadu ne?" Nace watakila suna yi ga garin
Nasara. Yace " suna dai koya". Yace "baka ga karfen
da ake juyawa bane jirgin ya motsa?" Nace masa
nagani.
Jimawa kadan naji zuciyata bata son wurin ruwa, har
na fara tofi. Ina cin gurasa kekasasshiya amma bata
yimin komai ba, ga kaina yana gewayawa, sai na shiga
kasan jirgi wajen Abdulkarim, nace masa kabani wani
abi naci don kaina yana gewayawa, ina jin kumallo,
bakina yana daci. Ya amsa mini yace "oh' Oh!, jeka
kwanta daga can...

No comments:
Post a Comment