TARIHIN SAMUWAR K'ASAR GWARZO
Gabatarwa
Littafin 'Mazan Kwarrai' shine wanda Marubuci IBRAHIM BALA GWARZO ya k'addamar dashi a wajajen shekara ta 2000, wanda ya tattaro tarihin kafuwar garuruwa kimanin talatin da suke a tsohuwar K'asar Gwarzo. Bisa bukatuwar wannan tarihi da muke dashi, kuma bisa bukatar yad'a Ilimi, yasa na nemi (Sadiq Tukur Gwarzo) sahalewar Marubucin (wanda yake Uba gareni) domin rubuta wani yanki gami da yadashi ga al'umma. Hakika marubucin yaji dadin haka, ya kuma sahale min izinin yin hakan. Godiya da fatan alheri a gareshi.
TARIHIN SAMUWAR GARIN GWARZO
Kamar yadda tarihi ya nuna mana, akasarin garuruwan Kano Maguzawa ne suka Kafasu. Wannan gari na Gwarzo mai tsohon tarihi ya samu kafuwa ta hannun wani Bamaguje wanda ake kira 'GWARZO'.
A zamanin da, zakaga mutum ya samu guri ya kafa gida shi kadai, wanda daga baya idan mutane suka fuskanci wurin yana da yalwa sai kaga suna zuwa da kadan_da_kadan domin zama.
Ga al'adar mutanen da, wanda ya fara zuwa guri ya kafa gari shine sarkin garin.
Bayan wannan Bamaguje mai suna Gwarzo (wanda akace yazo ne daga arewa a wuraren K'arni na Sha shidda zuwa na sha Bakwai) Ya kafa 'yan tsangayunsa ya zauna a wannan guri, sai wani Malami yazo daga kasar Sakkwato wanda ake kira Malam Rashidu ya sauka a gurin shima. Sai Mallam Rashidu ya shiga rokon Allah subhanahu wata'ala ya albarkaci wannan guri da suke zaune, ya kuma kareshi. Ai kuwa hakan ya samu, domin har lokacin yake-yake yayi k'aura ba'a taba cin k'asar Gwarzo da yaki ba.
Bayan wani lokaci sai wani mutum da ake kira Isau yazo shima ya kafa bukkarsa ya zauna tare da Bamaguje Gwarzo da kuma Mallam Rashidu. Suna nan zaune abinsu sai ga wani Bamaguje ya risko wajen, sunan sa Kutunku, amma anfi kiransa da Riji.
Ganin haka sai Bamaguje Gwarzo yayi murna, ya samu danuwa. Wannan yasa yayi tunanin raba wannan wuri da suke zaune biyu b'angaren gabas da yamma masu kudu, sannan ya baiwa Bamaguje Riji mulkin barin gabas, shikuma yaci gaba da mulkin b'angarensa. Sai ya kasance duk bak'on da yazo ya zauna a b'angaren yamma maso kudu (wanda daga bisani ake kiran wurin da suna Gwarzo), to ya zama talakan Gwarzo, wanda kuma ya zauna a barin gabas (shima daga bisani Riji ake kiran wurin), Riji ne shugabansa.
A iya wannan lokaci, mutane sun rinka zuwa suna zama a wannan yanki. Akwai misalin wani hab'en mutum mai suna Katamba, wanda Gwarzo ya bashi wuri a inda ake kira Katambawa a yanzu, sannan da misalin wasu mutane da suma suka zo shigewa suka nemi a basu matsuguni, sai Gwarzo ya basu wani wuri a gabas dashi, inda a yanzu ake kira da Tsohon Garu. A wancan lokaci, ba iya wurin da mutum zaiyi gida kadai ake baiwa bako ba, A'a, ana bashi ne har ma da inda zai noma domin ya ciyar da kansa da kuma iyalinsa.
A kwana-a-tashi, sai Allah ya kawo wani dan-fulani mai suna Baba. Daya zo sai ya sauka a yankin da Gwarzo yake iko dashi. Shikuwa wannan bafullatani ance yazo ne daga Musawa ta k'asar Katsina, kiwon shanu da dabbobi itace sana'ar sa.
Ance wata rana sai dabbobin Bafullatani Baba suka shiga cikin gonar wani Bamaguje mai suna Rijau tare da tafka masa b'arnar amfanin gona, wannan yasa ya kai k'ara ga Sarkin wurin watau Gwarzo. Da aka kira Baba dan fulani sai aka tsareshi sai daya biya kimanin b'arnar da dabbobinsa sukayi, sannan aka yanka masa tara ya biya.
Ganin haka sai wannan bafullatani Baba ya sayar da dabbobinsa ya k'ulle kudinsa ya tafi kano wajen d'an iyan Kano domin lokacin shine mai kula da yammacin kano, inda ya nemi sarautar Gwarzo, wadda akewa lak'abi da 'd'an Gwarzo'. Sai kuwa yayi dace aka bashi. Aka tanaji dawakai daga kano bayan nad'insa, aka rakoshi zuwa garin Gwarzo ana kad'e-kad'e da bushe-bushe.
Koda Bamaguje Gwarzo, wanda yake sarkin Gwarzo (d'an Gwarzo mai ci) yaji kade-kade da bushe-bushe, sai ya aika aje a gano masa menene ke faruwa. Inda aka zo aka sanar masa cewa bafullatanin nan Baba da aka yiwa tara aka nad'o daga kano a matsayin sabon d'an Gwarzo. Jin haka keda wuya sai Bamaguje Gwarzo da Mallam Rashidu suka shiga gida, wanda har yau babu labarin d'uriyarsu. Domin basu fito daga gidajen nasu ba, ba'a kara ganin suba, ba kuma a sake jin labarin bullarsu a wani wurin ba.
Kawo wannan sabon d'an Gwarzo Baba, sai garin Gwarzo ya k'ara habaka. Fulani suka rinka kwararowa daga wurare mabanbanta, musamman ma daga Sakkwato. Haka ma sauran jinsuna ba'a barsu a baya ba wajen zuwa wannan gari domin zama.
Ance a lokacin Jihadi (1804), d'an Gwarzo Baba ya taimaki Shehu Usman Danfodio da dukiya da kayayyaki domin samun nasarar jihadinsa. Tarihi kuma ya nuna akwai alaka tsakanin fulanin biyu, watau d'an Gwarzo Baba da kuma Shehu Usmanu.
Dangane da yake-yake dake nuna Gwarzantaka ta mutanen Gwarzo kuwa, ance a zamanin Sarkin kano Abdullahi dan Dabo, anyi wani cikakken mayaki a Gwarzo mai sun DANBALKORE. Wata rana Sarkin Kano ya taba tura Sarkin Dawaki D'an Ladan domin fuskantar wancan sadauki, amma sai Danbalkore ya kashe Sarkin Dawaki d'an Ladan. Sarki kuwa yayi bakin ciki matuka da jin wannan labari. Ance tun a wancan lokacin ake kallon mutanen Gwarzo da masarautar Gwarzo a matsayin wadda taci sunanta ta ko w

No comments:
Post a Comment