HIKAYAR YARIMA HALA, MAFARAUCIN DABARUNƁRIKON SARAUTA.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
0806086998
Kafin k'arni na bakwai, kafin wanzuwar manyan daulolin k'asar hausa, anyi wata k'abila dake rayuwa a wannan yanki mai suna 'Sontsi'.
Fatar jikinsu bak'a ce mai sheki da laushi.
Fuskokinsu sirara ne masu ɗauke da dogayen hanci, dukkansu suna kamanceceniya da juna a fizge, abinda ke labarta cewar usulinsu na iya zamowa daga tsatson jikin mutum ɗaya suka fito.
Suna rufe jikunansu ne da ganyaye, amma jaruman cikinsu da Sarkinsu, fatun dabbobin da duke farauta ne mayaninsu da kuma gwadon rufarsu.
Kabilar sontsi jarumai ne, zomaye, kyarkeci da ita kanta barewa, ne kaɗai zasu iya bada labarin kaifin saitinsu a wajen harba kibiya.
Sunan sarkin su Jarma Murmu, sai kuma ɗansa dake jiran sarautarsa mai suna Hala.
"Hala nada jaruntaka, nasan shi gwanine a wurin harba kibiya"
Jarma Murmu ya faɗa a zuciyarsa yana tunanin yadda rayuwa zata iya kasancewa bayan rasuwarsa.
"Sai dai, wannan yayi kaɗan ga Hala ya zamo sarkin wannan kabila dashi... Hakika yana buk'atar karin hikimomi" inji Sarkin.
Sannan ya gyatta zamansa daga kishingiɗe izuwa zama.
Yana bisa buzun fatar damisa ne, acikin wata bukka dake shacin gidansa.
"Hala! Hala!! Hala!!!"
Sarki Jarma Murmu ya kwallawa ɗan nasa kira har sau uku, sai dai kafin ya gama rufe bakinsa daga kira na ukun har Hala ya shigo bukkar da gudu.
"Gani ranka ya daɗe" Hala ya faɗa cikin girmamawa.
"Hala, kai ne yariman garinnan, don haka dole akwai bukatar ace kana da hikimomin rayuwa, waɗanda zasu taimakeka wajen tafiyar da mulki bayan mutuwa ta"
Inji Sarki Jarma Murmu bayan ya nunawa ɗannasa wurin zama, almar dake nuna magana zasuyi mai muhimmanci.
"Baba, ka sanar mini a ina zan samo waɗannan hikimomi. Nikuwa na rantse da girman mulkin ka yanzu zan fita naje nazo dasu" inji Hala.
Sarki Jarma ya numfasa cikin murmushi, saboda yaji zance na kuruciya daga bakin ɗansa, sannan yace masa "Kai Yaro ne, wannan fa ba abune na gaggawa ba.."
Sannan yaci gaba da cewa "Ni bazan iya sanar maka a inda zaka ɗauki hikima ba a rayuwar nan, to amma haka al'adarmu take, tilas kowanne sarki ya zamo mai hikima da dabaru sama da mabiyansa"
Iya abinda suka yi kenan, kashe gari sarki Jarma sai ganin Hala yayi cikin shiri, yazo gareshi yana neman sanya albarkarsa da niyyar zai fita duniya neman hikimomin rikon mulki.
Sanye a jikinsa walki ne na fatar kura, sai kwarinsa da kwanson baka. A kansa kuwa wata igiyace ya ɗaure kansa da ita gami da soka gashin ɗawisu a cikin gashinsa. Wannan alama ce ta mutum neshi mai daraja a kabilarsu.
Sarki Jarma ya sanyawa ɗan nasa albarka, sannan ya ɗauki wasu sulallan tagulla guda biyu ya bashi da nufin koda cinikayya zata kamashi a wani wurin, ya samu na ɓatarwa.
Hala ya baro garinsu da tafiya mai nisa, sai yazo wata mararraba inda hanya ta rabu biyu, ɗaya gabas ɗaya kuma arewa.
Ya tsaya ya natsu yana tunanin hanyar daya kamata yabi. Amma daga cikin zuciyarsa yaji kamar ana bashi umarnin yayi gabas, sai kuwa yabi gabas ɗin.
Tun bai fara nisa akan wannan hanyar da yabi ba ya lura da cewar ya shiga wani yanki daban da yankinsu.
Kasar yankinsu Ja ce mai danko a jiki, to amma wannan kasar tafi ga rairayi, sannan babu irin bishiyoyin dalbejiya daya saba gani a yankinsu, bishiyoyin wannan yanki kwakwa ce da ayaba a mafi akasari.
Yana cikin wanan nazari ne ya hango wani manomi yana ta aiki a gonarsa.
"Mai aiki barka dai, ka taimaka ka sanar mini nan a ina nake" Inji Hala.
Ba tare da manomi ya ɗago kansa ya kalli mai magana ba yace "kai shashasha, yanzu baka san nan ba?... nan ai kana daura ne da tafkin Jimeru"
Hakika Hala baiji daɗi ba da aka kirashi da suna shashasha, to amma a ransa sai ya danne yana mai tuno abinda ya baro shi gida.
"Ina iya zamowa shashasha, to amma neman hikimomi ne suka baro dani daga garinmu. Babana yace sai ina da dabarun rayuwa zan iya gadon sarautarsa idan ya mutu"
Inji Hala.
Manomi ya tuntsure da dariya, shi yaji mugunta.
Ya ɗago kansa, ya kalli Hala. Yace a ransa "lallai anyi sakarai a wurin nan"
Bayan ya kare masa kallo ne tsaf sannan yace
"Yo kai yanzu daka baro gida saboda wauta a ina kake tsammanin zaka samu hikimomi, ko kuwa kana zaton akwai kasuwar da ake siyar dasu ne zaka siya?"
"eh, na fito ne da niyyar nayi farautarsu a duk inda suke, to amma idan akwai inda ake siyar dasu na rokeka ka sanar mini"
Inji Hala.
"Idan na sanar maka, dame zaka siya? Manomi ya tambaya yana murmushin k'eta".
"Inada Wasu sulalla biyu na tagulla gasu a tare dani". Hala ya faɗa yana kara matsawa kusa da manomi.
Manomi yayi yak'e, gami da gabatowa kusa da Hala sannan yace "idan har zaka siya, inada hikimomi da zan sanar maka, don haka ka huta yawon nemansu a duniya"
Hala ya fiddo sulallansa, ya mika su ga manomi cikin russunawa yana cewa "ai kuwa da ka hutar dani da wahalar yawon duniya".
Manomi ya karɓi kuɗi, ya sokesu a ɗamarar dake ɗaure a kugunsa, sannan ya dubi Hala yace.
"Hikimomin da zan sanar maka guda biyu ne rak, saurareni dakyau kajisu.
Ta ɗaya, inada wani hali. Duk inda naje naga anyi mini shimfiɗa domin na zauna, to bana yadda na zauna face na sauyawa wannan shimfiɗar matsuguni. Hakan na nufin ba dukkan abinda ya burge mutane ke burgeni ba.
Hikima ta biyu itace, duk sanda naje tafki yin wanka, to bana yi a inda kowa da kowa keyi, domin hakan zaisa naji ɗaya nake dasu, maimakon haka sai na matsa can gaba abina nayi wankana.
Don haka kaji hikimomi na kuɗinka, sai kayi gaba kabar ni nayi aikina.
Hala yayi godiya sannan ya juyo abinsa da nufin komawa gida don ya labartawa mahaifinsa hikimomin daya siya.
To amma kuma sai hanyar daya biyo ta ɓace masa.
Tun da tsakar rana yaketa bilin-bituwa har gabannin faɗuwar rana, sannan ne ya hango wani ɗan kauye a gaba da inda yake tunkara.
"Gashi na gaji sosai, ina bukatar hutawa kuma da abinciƴ, don haka bari na karasa wannan kauyen na nemi makwanci, inyaso da safe sai su ɗorani akan turbar kauyen mu"
Hala ya faɗa a zuciyarsa.
Daga nan yaja kafa cikin gajiya ya doshi kauyen, sai dai kuma kafin ya karasar wa cikin kauyen ya gamu da wani karamin tafki da mutane aciki suna kurme.
" Ya kamata nayi wanka don wartsake gajiyar jikina.." Hala ya raya a zuciyarsa.
Don haka, daya isa tafkin sai ya soma yunkurin faɗawa ruwa don wanke jikinsa, to amma sai ya tuna da dabarar da aka siyar masa babu jimawa, kurum sai ya koma can gefe inda duhuwar tsirrai take a cikin tafkin, ya shiga domin soma wanka.
Yana cikin wankan ne sai yake hango wani kyalkyali na fitowa daga tsirrai. Don haka yaji a ransa a kamata yaga ko menene.
Isarsa wajen ciyayin keda wuya ya tarar da wata tukunyar k'asa cike da sulalla na tagulla an cusa su tsakankanin ciyayin saman ruwa an ɓoye.
''Da alama ɓarayi ne suka sato wannan dukiyar suka ɓoye anan saboda kasancewar wurin babu mai zuwa don yin wanka aciki." Hala ya faɗa a zuciyarsa.
$Yanzu gashi kuɗin sun zama nawa" inji shi cikin annushuwa.
Cikin karsashi da murna ya fito daga cikin tafkin da niyyar shiga gari don neman makwanci kafin gari ya waye.
"Kai samari, wanene kai, kuma me ka tsinta kake ta murna haka, tun ɗazu idonmu akanka yake" inji wani dattijo, yayin da mutanen dake zagayen tafkin su kimanin goma suka taso baki ɗaya izuwa gareshi.
"Ku tsaya-ku tsaya" inji Hala
Sannan ya sanar musu da cewa shi bako ne yammaci yayi masa har ya kasa gane hanyar kauyensu, don haka yazo nan domin samun makwanci kafin gobe da safe. Sai yanzu kuma yana wanka yayi tsintuwar tukunyar sullallan tagulla masu daraja.
Anan fa aka shiga rige-rigen wanda zai bashi makwanci. Wannan na cewa yana da yalwataccen fili a gidansa, wannan na cewa yana da sabuwar tabarmar kaba, wancan na cewa shi yafi cancanta ya baiwa bakon makwanci saboda yana da yalwatar abinci da zai ciyar da bakon har zuwa safiya.
Daga baya dai, Hala ya zaɓi ya tafi tare da mutumin daya soma tambayarsa shi wanene.
Suka tafi cikin kauyen tinkis-tinkis, me gida na gaɓa Hala na biye masa a baya, rungume da tukunyar dukiya.
Da isarsu gidan, sai maigida ya umarci Hala ya ɗan jinkirta, zai shiga ya sanar da mai ɗakinsa yayi bako don a gyatta masa makwanci a kuma samar masa da abinci.
Shiru-shiru Hala na saurare har ya soma kosawa, daga can kuma sai maigida ya leko yace masa ga shigo.
Da yake rana ta faɗi, duhu ya baibayi garin. Kowanne ɗan boto na gidan an kyasta fitila don samar da haske a cikinsa.
Megida ya shigar da Hala wani ɗan boto, acikinsa akwai wani ɗan tudu daga can kurya, sai kuma tabarmar kaba shimfiɗe akan tudun.
Sannan akwai tukunya cike da abinci da abinsha a gaban tabarmar.
" Nasan dole kana da gajiya, don haka sai ka ajiye tukunyar tagullanka agefe, ka kwanta akan tabarmar ka huta"
Inji Maigida.
Hala ya ajiye tukunyar tagullansa a gefe bayan maigida ya gusa, sannan ya nufi tabarma da nufin shimfiɗewa ya ɗan wartsake gajiya sannan yaci abinci, to amma sai ya tuno da dabara ta biyu daya siya da kuɗinsa daga wurin manomi, don haka nan da nan ya ɗauke tabarma tare da sauya mata wuri.
Sai dai, yin hakan keda wuya ya lura ashe mugunta aka shirya masa, domin kuwa tabarmar a saman wasu itatuwa take sirara waɗanda aka gicciya saman wani wawajeken rami sabon hak'awa.
"Da alama maigida yana so na auka ramin nan ne kodai na mutu ko kuma naji mummunan rauni, inyaso sai yazo ya mallake dukiya ta... To kuwa ahir ɗinsa, hakan ba zata yiwu ba" Hala ya raya a zuciyarsa.
Sannan kafin kace haka, ya suntumi tukunyarsa ya fita daga bukkar a guje.
Ashe kuwa maigida kasak'e yayi yana sauraron yaji ihun Hala bayan ya faɗa rami. Amma koda ya hango gittawarsa a guje, sai shima ya biyo shi da gudu.
Fitarsu keda wuya sai mutanen kauyen duka suka runtumo suna wa Hala ihun atara-atara. Ashe Suma ɗaukacinsu sun kwallafa rai akan wannan tukunyar sulallan tagulla, maganin kada suyi faɗa dashi shiyasa suka shirya masa mugunta don ya faɗa, ko kuma idan dare yayi suje su halaka shi su ɗauke dukkiyar.
Duk da gajiya gami da yunwar dake addabar Hala, amma sam baiyi kasa a guiwa ba, haka ya rika runtuma gudu cikin daren nan har doshin wayewar gari, sannan ya fara fuskantar ya komo hanyar daya soma bi tun da farko.
Daga lokacin daya tabbata babu mai binsa, sai ya hau hanyar kauyensu, kafin wani lokaci sai gashi ya dawo gida.
Mahaifinsa ya tarbeshi da cewa ''Kai yarona, kai daka ce ka tafi neman dabarun rikon mulki, ya zan ganka ka juyo a iya kwana ɗaya tal?''
Hala yace "kwarrai kuwa Ranka ya daɗe, na siyi dabarun rikon mulki da tagulla biyun daka bani, gashi kuwa sun samar mini da tukunya cike da sulallan tagulla".
Daga nan ya kwashe labari ya sanar wa mahaifinsa.
Aikuwa sarki Jarma Murmo yaji daɗi sosai.
Yasa aka tara ɗaukacin mutanen garin aka sake labarta musu labarin.
Bayan Sarki Jarma Murmo ya rasu, ɗansa Hala ya gaje shi, ya zamo shugaba mai adalci kuma abin soyuwa ga jama'arsa.
Shekaru masu yawa, mabiya Hala 'yan kabilar sontsi sun rike waɗannan hikimomi nasa dakyau, duk inda suka je aka basu wurin zama, to kuwa tilas sai sun mayar da abin zaman gefe zasu zauna.
Idan kuwa wanka zasuyi a tafki ko Rafi, to ba-sayi a wurin da kowa da kowa keyi.

No comments:
Post a Comment