KIMIYYA: MANYAN ABUBUWAN MAMAKI DA SUKA GAGARI MASANA KIMIYYAR ZAMANI, WADANDA KUMA AKA SAMU AMSOSHIN SU A CIKIN ALQUR'ANI MAI GIRMA
(Abin daya kamaci duk musulmi ya sani)
Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
Da sunan Allah mai Rahama mai jinqai. Allah yayi dadin tsira ga Annabi Muhammad (s.a.w).
Wannan qasida ta tattaro zantukan manyan Masana wadanda yawa-yawansu ba musulmai bane akan gaskata ayoyin alqur'ani gami da tsinkewa da mu'ujozozin sa. Alqur'ani dai ya sauka ne ga Annabi Muhammad (S.a.w) tun a zamanin rayuwar sa, sama da shekaru 1400 kenan, amma sai gashi a yanzu masanan na nanata abinda littafin ya fada bayan sun bata lokaci wajen duba madubai, daukar hotuna da sauran matakan bincike, haqiqa wannan ne yasa da yawa suka gaskata Alqur'ani da Annabi Muhammad (S.a.w), suka tabbatar da cewa littafin ba wani mahaluqi ne ya rubuta shiba, tabbas saukar wa ce daga Ubangiji Makadaici.
1. Da farko zamu fara da Dakta T. V. N Persaud, farfesa akan jikin dan adam, farfesa akan likitanci da lafiyar yara, kuma farfesa akan likitancin mata, naquda da haihuwa a jami'ar mannitoba, a winnipeg dake qasar Canada. Har ila yau wannan mutumi ya rubuta karbabbun littattafai na kimiyya guda 22 da kuma qasidun kimiyya guda 181. A shekarar 1991 kuma qungiyar masana kimiyar jikin dan adam ta bashi lambar girma ta fitaccen masani a fannin nasu mai taken 'J.C.B Grand award'.
Wannan mutumi yayi bincike sosai akan alqur'ani, ga kuma abinda yace alokacin da aka tambayeshi abubuwan mamaki dake cikin littafin
"Kamar yadda aka sanar dani, Muhammad mutum ne gama-gari, wanda bashi da ilimi, bai iya karatu da rubutu ba. Sai gashi a yanzu muna maganar shekaru dari har sau goma sha hudu wadanda suka gabata. Wancan mutumin mara ilimi ya fadi maganganu wadanda a zahiri suke na gaskiya a kimiyance. Ni a karan-kaina nasan wannan ba abin wasa bane. Akwai zantuka masu yawa na gaskiya a maganganunsa game da kimiyya, don haka nima kamar Dakta Moore, na amincewa zuciya ta cewa ilimin aka saukar masa shiyasa har ya samu damar fadar wadancan abubuwa".
Ance Farfesa persaud yana yawan janyo ayoyi da hadisai don yin kwatance ko kafa hujja dasu acikin lakcocin sa.
2. Dakta Joe Leigh Simpson, farfesa ne a fannin nasabar dan Adam a Baylor College of Medicine dake Houston ta jihar Texas dake Amurka. Kwararre, gogagge kuma masani ne akan fannin kimiyyar dan adam, kuma shine shugaban kungiyar ' American Fertility society', ya amshi manyan lambobin girma a duniya ya kuma yi nazari akan wasu hadisai na Manzon Allah (s.a.w).
Wadannan hadisan sune;
I. Hadisi mai lamba ta 2643 acikin littafin sahih Muslim, yake da kuma lamba 3208 a sahih Bukhari, wanda Annabi (S.a.w) yake cewa " kowanne dayanku, dukkan sassan jikinsa na gama haduwa ne acikin mahaifar mahaifiyarsa idan ya cika kwanaki arba'in."
II. Hadisi mai lamba ta 2645 a littafin sahih muslim wanda Annabi (s.a.w) yake cewa "Idan dan tayi ya cika kwanaki arba'in da biyu a cikin mahaifa, sai Allah ya turo mala'ika wanda yake yiwa dan tayin siffa, kuma ya qera masa ji, gani fata, tsoka da qasusuwansa.."
Wannan Farfesa yayi matuqar nazari akan wadannan hadisai har ma ya qayatu sosai dasu, don haka a wani babban taro na masana yake cewa "wato dai maganganun Annabi Muhammad sun bamu ilimin abubuwan dake faruwa ga dan-tayi kafin cikar sa kwanaki arba'in acikin mahaifa. (Abinda a baya bamu sani ba). Abinda ya kamata mu gane shine wannan ilimi ya sauka ne a lokacin da babu wani mahaluqi daya isa ya bincika hakan. Don haka tabbas, addini yana iya jagorantar Kimiyya izuwa turbar bincike ta gaskiya.. Hakan kuma na tabbatar da cewa zantukan dake cikin Alqur'ani zantuka ne na Allah"
3. Dakta E. Marshal Johnson, wani qasurgumin farfesa ne a kimiyyar jikin dan Adam, da kuma Ilimin rayuwa a Jami'ar Thomas Jefferson dake Pennysylvania ta qasar Amurka. Har ila yau, shine shugaban gungun masana mai suna 'Teratology Society' wanda kuma ya wallafa takardu karbabbu na kimiyya sama da 200. Ya gabatar da wani dogon rubutu a wani taron masana mai taken 'seventh medical conference' wanda ya gabata a Dammam dake qasar Saudiya. Ga kadan daga abubuwan da yace " Alqur'ani ba iya sassan waje na jikin dan adam kadai ya wassafa bayani akai ba, har ma da sassan ciki, yana mai wassafa muhimman abubuwan dake wakana mataki-mataki a jikin dan adam"
Ya qara da cewa " A matsayina na masanin kimiyya, ina gaskata abinda na gani ne kurum, ina kuma iya fahimtar kalmomin da aka fassara mini na cikin alqur'ani, don haka kamar yadda na baku misali, idan da nine zaku mayar izuwa lokacin da littafin ya sauka, ina tabbatar muku da cewa bazan iya yin bayanin da alqur'ani yayi ba (akan jikin dan adam). Don haka banga hujjar da zata sa na yarda da cewa wannan mutum, Muhammad daga wani waje yake qirqirar zantukan sa ba. Tabbas zantukan sa saukarwa ne."
4. Dakta willim W. Hay, fitaccen masanin albarkatun ruwa. Farfesa ne kuma na ilimin ma'adinai a Jami'ar colorado ta amurka. Bayan tattaunawa da akayi dashi akan zantukan da Alqur'ani yayi a game da Ma'adinan ruwa, ga abinda yake cewa "haqiqa na tsinkaya matuqa ganin wafannan zantuka a cikin littafin daya jima irin alqur'ani, kuma gaskiya bansan daga inda zantukan suke ba.." Da akay masa tambaya akan usulin alqur'ani, sai yace tabbas saukarwar ubangiji ne.
5. Dakta Gerald C. Goeringer, farfesa ne a fannin likitancin dan tayi dake cikin mahaifa a jami'ar Georgetown dake birnin Washington D.C na Amurka. Yayi bincike matuqa gaya akan ayoyin alqur'ani da suka shafi dan-tayi, ga abinda kuma ya sanar ga masana, kuma mahalarta taron 'Eighth saudi medical conference' da aka tabayi a riyadh na qasar saudiyya.
"A cikin ayoyi marasa yawa da suka kawo zantukan girman da dan-tayi keyi acikin mahaifar mahaifiyarsa, sai gashi alqur'ani ya fahimtar da duniya yadda manyan abubuwa masu mamaki ke aukuwa mataki-mataki. Tabbas, ba'a taba samun kwatan-kwacin irin haka ba a wani littafi a duk tarihin duniya"
6. Dakta Yoshihide kozai, gagarumin farfesa ne a jami'ar Tokyon qasar Jafan, shine kuma daraktan wata cibiyar binciken sararin samaniya dake garin Mitika, a qasar ta jafan mai suna "National Astronomical Observatory". Shima ga abinda yake cewa a game da Alqur'ani da kuma ilimin sararin samaniya "Na qayatu matuqa dana samu zantuka na gaskiya a game da sararin samaniya acikin alqur'ani, kuma ta bayyana cewa mu da muke masana sararin sama na wannan zamani ilimin da muka sani akan Madaukakiyar duniya (Universr) dan kadan ne. Kuma mun maida hankulan mune wajen sanin abin da yake qalilan, domin aduk sanda muka hangi sama da maduban mu na hangen nesa, qaramin yanki kurum muke iya hangowa ba tare da tunanin sauran sassan ba dake cikin madaukakiyar duniya. Don haka ta hanyar karanta alqur'ani da kuma amsa tambayoyi, ina ganin zan iya samo hanyar yin bincike na ga sararin samaniya"
7. Farfesa Tejatat Tejasan, shine shugaban sashin ilimin sassan dan adam dake jami'ar Chiang Mai dake Thailand, ya kuma taba rike shugabancin tsangayar Ilimin Likitanci ta Jimi'ar, shima ga abinda ya wassafa a wancan taro na 'Eighth Medical conference' da akayi a Riyadh.
"Shekaru uku da suka wuce na kamu dason alqur'ani.. Daga bincike na da kuma abinda na koya a wannan taron, ya nuna cewa dukkan abin da yazo acikin alqur'ani shekaru dubu da dari hudu da suka gabata gaskiya ne wanda za'a iya tabbatar dashi zahiri a kimiyance. To tunda ance Muhammad bai iya rubutu da karatu ba, tilas mu yadda cewa shine dan aiken daya isar da gaskiyar (Sallallahu Alaihi Wa Sallim) wadda tazo daga wani bunqasasshe wanda muke iya kira da mahalicci. Wannan Mahaliccin haqiqa shine Allah. Don haka ina tunani wannan lokaci ne da zan ce La ilaha Illallaahu Muhammadur Rasoolullah (anan take ya karbi musulunci). Saboda gashi binciken da muka shafe tsawon lokaci munayi ashe tuni amsar sa na rubuce a littafin daya shafe shekaru dubu da dari hudu a duniya.. Anya za'ace Muhammad ne ya qagi wannan littafi? Lalle wannan littafi saukar wa ne daga Allah..."
Hmmmmm. Alhamdullahi bi Ni'imatul islam. Mai son qarin haske yana iya bincika Video mai taken "This is the truth" a yanar gizo don ganewa idon sa jawabin masanan da kansa. Haqiqa Mungodewa Allah abisa kasancewar mu Musulmai, muna fatan kuma Allah ya bamu rabo da cikawa da imani. Amin

No comments:
Post a Comment