TARIHIN HAUSA DA HAUSAWA
Hujjojin dake nuna Asalin Hausawa Daga misira suke daga Littafin 'Gamsasshen Asalin Hausawa da Harshen su' wanda Comrade Zakariyya Abdurrahman Shu'aibu Kabo ya wallafa a shekarar 2013.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Kashi na uku.
Amma a game da cewar Misirawa ne Asalin Hausa, Marubucin ya zayyano waɗannan a matsayin hujjoji masu tabbatar da haka:-
1. Da akwai wata takobi mai rubutu ajikinta irin ta mazauna kasar misira ada can wadda koda turawa suka zo sai da suka ce wannan takobin babu masu irinta sai misirawa. Kuma ko yanzu kaje Daura ana iya ɗauko maka ita ka ganta.
2. Yanayin tsarin gine-ginen fadojin sarakunan hausa ɗaya ne dana misirawan-da. Zakaga anyi soro, sannan katangun gida masu kaurin Gaske. Akan kuma yi manyan turaku da babban fili a matsayin tsakar gida da manyan zaurukan hutawar sarki.
Bugu da kari shine rubutu da hotuna da akeyi a bangwaye. Banbancin kurum shine su misirawa na gina gidajen sarautar su da dutsuna ko ajikin duwatsu, amma a kasar hausa kuwa babu irin waɗannan tsaunukan.
3. Tsarin sarautar fir'aunoni da mabiyansu yayi kamanceceniya dana Sarakunan hausa da mabiyansu.
4. An samu wasu marubutan tarihi masu nuna cewar asalin hausawa kibɗawa ne, an same sune kuma daga fir'auna Namrudu, kuma akace jikokin sane suka zo suka kafa daura, don haka ma ake yiwa sarakunan hausa kirari da Jikokin Lamarudu.
Duba littafin Kano daga Dutsen Dala na Farfesa Muhammad Uba Adamu shafi na 32. Shima ɗin ya danganta abinda ya rubuta da Gwamna Lugga, wanda yace ya rubuta hakan a littafinsa mai suna a 'Tropical Dependency'.
(sai dai marubucin shi kansa yace yana da ja akan haka, saboda babu Fir'auna mai suna Namarudu a Misira, sai dai sarki a Babila.)
5. Kaman-ceceniyar harshen hausa dana tsohuwar Misira. Misali idan hausawa na koyawa yaransu tafiya, da sun soma mikewa sai kaji sunce "Ta-Ta-Ta". To haka ma yake ga tsoffin mazauna misira idan haka ta faru suna cewa "Ta-Ta" sai kuma suyi ta maimaitawa. (Wannan lafazi hairogaliphiy ne inji shi)
Haka kuma, yayin da iyaye ke son tsoratar da yaransu su daina wata kiriniya, sukan tsorata sune da 'Dodo'. Dodo kuwa wani aljani ne abin tsoro a wurin hausawa. To haka ma tsoffin misirawa keyi ta hanyar tsoratar da yaransu da ifiritinsu mai suna 'Bobo' ko 'Baa-Baa'.
Waɗannan kalmomin na ifiritan kuwa duk kibɗanci ne.
Sannan, hausawa na kiran mutum mai juriya da taurin kai 'ɗan tauri', sukuwa tsoffin misirawa suna kiran irin wannan mutum da 'antayo'.
Akwai kuma hasashen yadda kalmar 'Habku' ta misirawa ta koma bako da hausa da ma'ana iri ɗaya.
Hausawa suna kiran shimfiɗar data lulluɓe jikin mutum 'fata'. Da yaren kibɗanci kuwa ana kiranta 'ɓata' ne ko 'hata'.
6. Wanzuwar Addinin bautar Rana a kasar hausa kamar yadda ya wanzu a misira. Hujjar anyi bautar Rana a kasar hausa itace wakar nan da yara ke rerawa suna cewa "Rana rana buɗe buɗe in yanka miki ragon sarki kisha jini shar shar".
8. Samun da akayi cewa sarakunan farko da suka mulki daura Mata ne. Hakan na nuna cewar mutanen da suka baro misira a lokacin mulkin Hatashbasut sune suka shigo kasar hausa. Don haka da suka zo sai suka cigaba da al'adunsu na ɗora mata a mulki.
9. Samun Wata alama mai siffar gicciye (kuros) a ganuwar data kewaye gidan sarautar maraɗi.
Wannan alama tayi kama data misirawa, kuma kamar yadda marubucin littafin 'Kitabul Maut Lil masiriyin Al kudamau' ya faɗa cewa wannan alama na nufin al hayatu, ma'ana rayuwa. Kuma akan sata ne a gidan da niyyar addu'a ta Allah ya raya gidan.
Marubucin ya kuma zayyano waɗannan abubuwa a matsayin hujjojin da yagani da idonsa a gidan Adana kayayyakin tarihi mai suna 'Mathaf Nubi' dake yankin Nubiya cikin kasar Misira, masu tabbatar da cewa tushen hausawa daga can yake.
1. Yace yaga Rigar sanyawa (Taguwa) iri ɗaya data bahaushe.
2. Yaga Fai-fan kaba irin na hausawa.
3. Wukake da kubensu masu kama da kirar kasar hausa
4. Akurkin kaji irin na hausawa
5. Dutsen nika da ake markaɗe
6. Zanen Dagi da ake yinsa a matsayin tambari a fadar sarakuna.
7. Yanayin kunyarsu da karrama bako yayi kama dana bahaushe
8. Yanayin kasar wajen da suke rayuwa yayi kamanceniya da kasar hausa...
** ** **

No comments:
Post a Comment