LABARIN BAWA DORUGU, BAHAUSHEN DA
YA FARA ZAGAYA TURAI
Kashi na takwas
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa " Mutanen garin nan da
muka je suka zo suka cewa Abdulkarim yayi musu
addua basu da ruwa, amma yace adduarmu daban take
da taku. Domin ku idan kunayin addua kuna yin magana
idanu a bude, mukuwa a sirri mukeyi. Haka nake
tsammanin ya fada musu. Sannan ya dunkule hannu
yayi addua, mutanen gari da Sarki su kuma na zagaye
dashi, ni kuma ina gefe ina masa gahawa. Daya kare
suka gode, suka tafi. A daren kuwa sai da aka samu
ruwa. Sai suka cika da mamakin yaya farin mutum ya
kira ruwa?
Da muka tashi daga garin nan, sai muka hau jirgin
ruwa. Masu jirgin mutanen Timbuktu ne. Suna maganar
Timbuktu da fulatanci, har suka kawo mu ga wani gari
wanda yake kusa da timbuktu, in katashi da safe daga
nan, kana iya isa timbuktu da marece.
Mutanen wannan gari suna kama kifi da yawa. Anan
ma naci naman Ayu mai cike da mai. Bamu jima ba
muka karasa izuwa timbuktu. Garin timbuktu acike yake
da mutane. Masallacinsu yana da tsawo kamar na Inliz.
Sau daya na shiga cikinsa, kuma naga yana da kyan
gani. A timbuktu ina tsammanin babu arna, babu
yahudawa, babu nasara sai musulmai. Idan suna kiran
Sallah kamar Arab. Suka so susa Abdulkarim ya koma
musulmi, amma yaki. Idan suka ga mutum yana shan
taba sai sukaishi ga alkali.
Haka akayi ga Abega. Yana shan taba sai bayin fulani
suka ganeshi, dayansu yace masa "ka bani tukunyar
tabarka in gani". Abega na tsammanin suna masa worgi
ne, amma da yaki sai suka fara fada. Suka ce sai sun
tafi ga alkali. Suna zuwa wajen masallaci ya hango
larabawa da yawa a wajen, sai yace bazai karasa ba,
sukuma suka ce sai yaje. Kici-kici suka fara kokawa
suna jan shi. Da larabawan suka ga haka sai suka
tambayi ba'asin abinda ya faru. Da sukaji sai sukace
musu ku kyaleshi wannan bako ne, baisan bakuson
asha muku taba ba. Sai da Abega ya dawo gida yake
fadamana, mukayi ta dariya. Muka ce masa da yau ka
shiga cikin dakin duhu na fulani.
Tunda muka zauna a timbuktu, zama babu dadi, domin
Abdulkarim yaki musulunta. Fulanin garin sukace suna
kasheshi ko ya basu dukiya don sunga wani katon
sunduki. Rannan muna bayan gari sai mukaji kidin
Tambari a cikin timbuktu. Daga nan fa garin ya cika da
dokunan fulani. Wani mutum ya zaga ya fada mana
cewa fulanin timbuktu nason dauke kayan Abdulkarim.
Wani abokin Abdulkarim mai suna Sidi-al bokayi, ya tara
'yan uwansa abzinawa wajen dari biyu ko uku.
Wadansu bisa doki da mashi da garkuwa, mukuma
muka shiga shirya bindigogin mu. Mutanen fulani
sukazo suka gewaye sansanin mu. Abzinawan nan suka
taresu. Aka hau harbe-harbe, kasan abzinawa kamar
wuta suke ga fada. Da fulanin nan sukaga ba dama, sai
suka nemi sulhu.
Bamu dade ba muka shirya kayanmu, Abdulkarim ya
shirya kayansa acikin sundukinsa hudu, muka tashi
muna murna da gode Allah. Mukayi sallama da sidi al
bokayi don inda yake kwana nan ne a wajen gari, bayan
yayi mana rakiya ya koma, mukuma muka cigaba da
tafiya. Munyi tafiyar kwana goma duka muna yawo
acikin abzinawa. Matan timbuktu kiba garesu. Wata
dana gani, dantsenta yayi cinyata. Wata kuwa 'yar
shekara goma zatayi uwata. Da jakai biyu suke tafiya,
idan daya ya gaji suhau daya. Jakunansu kuwa suna da
karfi. Matansu kamar dorina, basu da kyan gani ko
kadan, hausa sun fisu kyau. Amma kuma suna da
nagari. Idan ka samesu, sai dai idan a daji ne ganinsu
zai baka tsoro.
Muka ketare wani gari gefen ruwa, ruwan duk ga dorina
nan ta fito suna kuka. Dawakanmu suka firgita, samarin
mu suka fara harbinsu da bindiga, sai suka yo kanmu,
da sukaji harbi dai mu kuma muna ja da baya, sai suka
koma cikin ruwa.
Daga nan muka isa garin da muka hau jirgin ruwa tun
da fari. Muka ketare gulbi. Muka zaga wani gari muka
kwana anan. Da muka tashi, sai da mukayi kwanaki da
yawa muka isa gwandu. Mutanen da suka sanmu
sukayi murna, muma mukayi murna don mun zagaye
iyakar hausa.
Bamu jima anan ba, muka tashi sai sakkwato. Muka
zaga izuwa wani gari inda muka sauka da fari kafin mu
shiga sakkwato, anan ruwa ya samemu, amma bamu
kula dashi ba, don mun saba kamar kifi. Da muka tashi
sai muka bi ta wurno. Muka ga mata na daukar ruwa a
tulu bisa kansu izuwa gida, muna nan naji ance gobe
kada kowa yaje bakin ruwa koda baiwa dawaki ruwa,
don 'yan ruwa na wucewa. Wai duk wanda yaga 'yan
ruwa mutuwa zaiyi.
Muna zaune a wurno aka kawo labarin ga fatake nan
na zuwa. Sarki Aliyu ya tura mayakansa yace suje su
gani, idan mutanen lafiya ne su kyalesu, amma idan abokan gaba ne su kwato kayansu. Da sukaje sai suka kwato kayan nasu. Daga baya aka gane mutanen lafiya ne, fatake ne da suke zuwa kano, sai sarki yace a mayar musu da kayansu.
Da muka tashi daga wurno muka zaga ga Gwandu, akwai mutane da yawa tare damu. Kwanaki sha hudu muka isa birnin kano. Garin 'yam mata, don diyansu kyawawa ne...."

No comments:
Post a Comment