Monday, 11 December 2017

KASUWANCI: SALON KASUWANCIN ATTAJIRI ALIKO DANGOTE

HIMMA BATA GA RAGGO: SALON KASUWANCIN ATTAJIRI NA DAYA A AFIRKA, ALHAJI ALIKO DANGOTE.

Daga SADIQ TUKUR GWARZO

"Idan kana son zamowa attajiri ko wani mutum mai nasara, sai ka fara kwaikwayon halayen attajirai da mutane madaukaka"

Alhaji Aliko Dangote, Babban attajiri na farko a duniyar afirka, mutum ne sadauki a fagen yaƙi. Yaƙi ba na takobi ko bindiga ba, yaƙi irin na kasuwanci. Kalar wanda akeyi a kasuwa, wanda kuma ya ƙunshi siye da siyarwa. Bashi da wasa sam-sam akan cimma burikansa. A wurinsa, kasuwanci tamkar rayuwa ne da mutuwa, kamar ace ''Eh ko A'a". Watau samun nasara ne da faduwa. Don haka a kullum hanƙoran samun nasara yake yi a kasuwancinsa.
A ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2011, jaridar attajirai ta Forbes ta ayyana Aliko Dangote a matsayin attajiri baƙar fata na ɗaya a duniya. Hakan na nufin yafi kowanne bakin mutum dake rayuwa a wannan duniyar tamu arziki. A wancan lokacin an ƙiyasta cewa ya mallaki kudade da kadarori dai-dai da darajar dalar amurka biliyan goma sha uku da digo takwas. Sai dai abin mamakin shine, kafin ƙarshen shekara ta 2015, arzikinsa ya ƙaru sosai, inda ya zarta darajar kudi dalar amurka biliyan ashirin da uku da doriya. Wannan ne yasa muka ga buƙatar nazartar salon kasuwancin sa don amfanuwar mabuƙata.
An haifi attajiri na daya a fadin Afirka Alhaji Aliko dangote a ranar 10 ga watan afrilu na shekarar 1957, a jihar kanon dabo. Sunan mahaifinsa Muhammad Dangote (Allah ya jiƙansa), mahaifiyar sa kuwa sunanta Hajiya Mariya Sunusi Dantata, mace mai kyauta da aiyukan alheri.
Yayi makarantun firamare da sakandire duk a kano, daga bisani ya samu damar tafiya birnin Cairo (alqahira) dake ƙasar Egypt don yin karatu, inda ya kammala digirin sa a babbar jami'a ta duniya mai suna Al'azhar.
Duk da yake, wannan rubutu ba akan tarihin Aliko Dangote yake ba, amma mun samu tarihin cewa Aliko Ɗangote tun yana ƙarami yake siye-da-siyarwa, inda ya fara siyar da biskit da alawa a ƙofar gidansu. Daga bisani kuma bayan tasowar sa, yayi aiki a ƙarƙashin kawunsa alhaji Sani Dantata.
Don haka bayan kammala digirinsa a jami'ar Al'azhar a shekarar 1977, sai Aliko Ɗangote ya ga babu abinda ya kamace shi sama da fara kasuwanci. Abinka da wanda jinin Alasawa (zuriyar attajiri marigayi Alassan Dantata) ke yawo a jijiyoyin jikinsa, hanƙoron sa kurum na ya ga ya fara kasuwanci ne. Shine akace sai ya nemi rancen kudi Naira dubu dari biyar a wurin kawun sa, da sharadin zai maido dasu zuwa shekaru uku. Amma abin mamakin shine, Aliko dangote ya mayar da kudaden ne a tsawon watanni shidda kachal, saboda ya tara jalinsa, bashi da buƙatar cigaba da zaman kudin bashi a tare dashi.
Babban abinda aka fi sani game da salon kasuwancin Aliko dangote shine 'Hikima'.  Shi mutum ne mai hikima da hangen nesa. A lokacin daya fara dillancin kayayyakin abinci dangin su sukari, gishiri da sauransu, sai ya shirya ƙaƙƙarfar hanyar isar da kayayyakin sa ga kwastominsa cikin sauƙi da sauri. Sannan an tabbatar da cewa yana da hikimar fahimtar matsalolin kwastominsa gami da daukar matakin warware su da gaggawa.
A taƙaice dai, wadannan sune sirrikan salon kasuwancin da aka gano a tattare dashi;-
1. Ka fara Kasuwanci da kadan, kana mai burin samun girma a gaba.
Aliko dangote yace " Nayi burin zamowa attajiri baƙar fata na daya a duniya tun a shekarar 2008, amma sai hakan bai samu kasancewa ba. Sai dana shafe shekaru talatin sannan na zamo abinda nake a yanzu. Matasan wannan lokaci suna da burin zamowa kamata, amma hakan bazai yiwu ba a dare daya. Ga maison gina babban kasuwanci mai nasara, tilas ya soma kasuwanci da kadan"
2. Ka nemi Sanin Mutane, ka kuma yi adduar fadowar damarmaki
Hausawa na cewa "Sabo da Maza Jari"
Haƙiƙa an tabbatar da cewa Aliko Dangote ya soma samun arziki ne tun bayan takardar izinin shigo da kayayyaki da gwamnati ta bashi a gaɓar teku ta lagos. Wannan abu kuma bai yiwu ba sai ta silar mutanen kirki da suka tsayawa Dangoten har ya samu lasisin.
3. Ka Gamsu da cewar zaka iya samun Arziki a kasar ka ta haihuwa.
Ance Dangote ya gamsu da cewar a ko ina mutum yake, yana tare da damar-maki wadanda idan yayi amfani dasu zai iya samun arziki a rayuwar sa.
4. Allah yana Taimakon wanda ya taimaki wanin sa.
"Idan kano son Ilimi, ka fara koyar da Ilimi.
Idan kana son kudi, ka fara yin kyauta da kudade" (Karma)
Aliko Dangote yana matukar aiki da wannan ra'ayi. Ko a shekarun baya, ya ware kudade maƙudai kimanin dala biliyan daya da digo uku don tallafawa mabuƙata, aciki harda 'yan gudun hijira.
5. Ka siyar da Kayayyakin ka da arha, kuma ka tabbata suna da inganci.
An taba jiyo Aliko dangote yana cewa "siyar da ingattattun kayayyaki akan farashi mai rahusa yana ƙara maka daraja a idanun kwastomomin ka".
6. Ka gina kamfani, maimakon cigaba da zamowa dillali.
Idan da akwai babban sirrin zamowa attajiri a kasuwanci bai wuce na kafa kamfani ba. Kafa kamfani kamar misalin siyan injin buga kudi ne matsawar ana gudanar dashi da tsare-tsare masu inganci.
Dangote ya taba cewa "Ka gina kamfani, kada kawai kayi ta ɓugewa a dillanci. Domin samun babban tagomashi sai na yanke shawarar kafa kamfani mai samar da abinda nake dillancin sa a baya"
7. Ka ƙaunaci kasuwanci, Sai kasuwanci ya ƙaunace ka.
Dangote yayi amanna da cewa mutum bazai taba samun nasarar kasuwanci ba har sai ya kamu da son kasuwancin a zuciyar sa. Watau dai, dole mutum ya rinƙa tunanin abinda yake so (kasuwancinsa), ta yadda zai gano matsaloli da kuma mafita domin samun nasara.
8. Kayi aiki Tukuru, ka rinƙa samun hutu kuma.
Dangote ya taba cewa " Ina hutar da kaina sosai. Na gamsu kuma da yin aiki tuƙuru don samun nasara a kasuwanci. Zai yi wahala ka samu matashin da yake kwanciya bacci ƙarfe biyu na dare, ya farka ƙarfe biyar na asubah. A gaskiya bana hutawa har sai naga na cimma wani abu"
Aliko Dangote dai shine shugaban gungun kamfanonin 'Dangote Group', masu samar da sukari, siminti, filawa, taliya da sauransu. Sannan a yanzu yana qoqarin kafa kamfanoni masu taimakawa manoma sarrafa abinda suka shuka da kuma babbar matatar man fetur a nigeria.
Domin samun gamsasshen sirrikan kasuwanci daga attajirai, kuna iya neman littafin "ILIMIN KASUWANCI DA SIRRIKAN NEMAN ARZIKI" wanda 'SADIQ TUKUR GWARZO' ya wallafa

No comments:

Post a Comment