Daga Sadiq Tukur Gwarzo.
A ranar alhamis, 24 ga watan yulin na wannan shekarar da muke ciki ta 2015 hukumar nan mai lura da abubuwan dake aukuwa a sararin samaniya mai suna NASA ta sanar da gagarumar nasarar data samu ga manema labarai. Nasarar ba ta komai bace sai ta wata duniya da aka hango mafi kamanceceniya da wannan duniyayar ta earth da muke ciki, a hakika wannan abune wanda masana suka shafe shekaru suna jiran aukuwar sa.
Wata Na'urar hangen nesa mai suna keplar wadda hukumar NASA din ta harba tun a shekarar 2009 ce ta samu nasarar hango duniyar. Kamar yadda hukumar ta zayyana, tace daga cikin sama da duniyoyi 500 da wannan na'ura ta hangen nesa ta hango, wannan sabuwar duniyar da aka samu itace kadai ake da tabbacin za'a samu halittu masu rayuwa, wataqila ma mutane ne irin mu, kamar yadda wasu masanan ke fatan hakan.
Tun kafin wannan sanarwar dai, wani jagoran masana masu bincike a hukumar ta NASA mai suna Ellen Stofan ne ya fara shaidawa 'yan jaridu hasashen hukumar game da hango halittu a duniyar samaniya, inda yace "Ina tsammanin zamu samu kwakkwarar shaidar wanzuwar halittu a duniyoyin sama nan da shekaru ashirin masu zuwa"
Ya kara da cewa " A yanzu munsan inda ya kamata mu rinqa kallo a sararin samaniya don binciko halittu masu motsi, sannan kuma munsan yadda zamuyi kallon, gashi muna da kayayyakin fasaha na zamani da zasu bamu abinda muke da bukata."
Dangane da Sabuwar duniyar da aka hango kuwa, hukumar ta NASA cewa tayi " A iya yanzu, mun hau turbar samar da amsoshin tambayoyin da mutane da yawa suke nema a iya tsawon dubunnan shekarun da suka gabace mu, nasarar ba komai bace sai ta duniyar da muka hango mafi kamanceceniya da earth. "
Ita dai wannan duniyar wadda aka sanyawa suna 'duniyar mu ta biyu' wato "Earth 2.0" ance tana da nisan zango tsakanin mu da ita kwatankwacin shekarar rana 1,400, kuma anyi hasashen duniyar tana zagaye falakin Tauraruwar ta acikin kwanaki 385, wato dai darin kadan ne, domin duniyar mu tana zagaye falakin Rana tauraruwar ta ne a cikin kwanaki 365.
Haka kuma masu binciken sun kalli tauraruwar da duniyar ke zagayawa sosai, inda sukayi hasashen itama tana da kamanceceniya da Rana, bambancin kurum basu wuce na haske da nauyi bane, inda sukace tafi Rana haske da kashi goma sha biyu, sannan tafi Rana nauyi da kaso hudu. Wanda hakan ke nuni da cewa ta girmi Rana da misalin shekaru biliyan daya da Rabi.
Hasashen masu binciken dai ya nuna cewar duniyar da muke magana akanta ta darar wa duniyar da muke rayuwa aciki girma da misalin kaso sittin. Akwai alamun turbaya da kuma duwarwatsu a dandamarin ta. Sannan kuma ana da yakinin za'a samu ruwa da iska kwatankwacin samfurin wadanda muke dasu a duniyar mu.
Daga yanzu dai abinda hukumar NASA zata maida hankali akai sune hango sawu, motsi ko duk wata alama da zata nuna cewa a baya halittu sun wanzu a cikin duniyar, ko kuma a yanzu haka akwai wadanda suke rayuwa.
Daman dai babban burin masu binciken shine a samo wata halitta wadda ke rayuwa a wata duniya wadda ba tamu ba tayadda idan da yiwuwa za'a karanci tarihin halittar, yanayin ta da kuma iliminta, idan kuwa son samu ne, masu bincike suna son a samu wata halitta kamar jinsin dan Adam wadda za'a rika musayar sakonni tsakanin duniyar mu da tasu, daga bisani kuma sai a ziyarci juna..
A karshe muna cewa Allah ya bada sa'a.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo

08060869978
No comments:
Post a Comment