Sunday, 24 December 2017

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DANFODIO 2

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na biyu

Rasuwar Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo keda wuya sai ɗan uwansa mai suna Yakubu ya gajeshi.
  A lokacin kuma Shehu Usmanu ɗan fodio ya zauna a daular zamfara, har ma yana ganin aikinsa na wa'azi daya shafe shekaru yana yi a yankin ya samu nasara, don haka gudun kada duniya ta ruɗeshi sai ya koma mazauninsa Degel.
  Sarkin Gobir Yakubu kuwa da hawansa mulki, sai ya shiga shirin yaki don tafiya garin Dankace ɗaukar fansar ɗan uwansa Bawa Jan Gwarzo.
  Ance akan hanyarsa ta tafiya, Shehu Usmanu ya aika masa da kira izuwa tafarkin tsira, tafarkin musulunci na gaskiya.
  Kuma ana ganin yayi yunkurin bin kiran shehu Usmanu da fari, amma sai mutanensa suka hana. Sai dai shima koda yaje Dankace da yaki acan hanya ya mutu bai dawo Alkalawa da rai ba.
  Shehu Usmanu ya shiga yankuna makwabta yana wa'azi, shine har cikin garuruwan kasar Kabi (Kebbi) yana kira izuwa musulunci tare da barin shirka da bidi'a, ya tsallaka gulbin Kwara mafi girma a wannan yanki, har ma ya isa wani gari mai suna Ilo (Ilorin) ya kai musulunci, kamar yadda ya faɗa a wakensa inji Wazirin Sokoto Junaidu.
   Bayan Mutuwar Yakubu, sai ɗan Uwansa Nafata ya gajeshi.
  Shikuwa a kullum cikin k'ulla sharri yake ga Shehu Usmanu.
  Watarana sai ya kira Shehu Usmanu izuwa fadarsa. Nufin sa idan yazo ya halaka shi.
   Don haka shima sai ya tara sarakuna da malaman daularsa, ya zauna a tsakaninsu akan kujera, sannan ya hori shehu Usmanu ya shigo gareshi.
   Akace, koda Shehu Usmanu ya shigo, sai kuwa wani kurji dake wuyan Sarkin Gobir Nafata ya fashe, nan take ya faɗi sumamme. Aka ɗauke shi izuwa gida magashiyyan baya iya magana.
   Shehu Ya koma Degel. Yumfa ɗan Yakubu shine yayi masa rakiya a lokacin.
  Sa'ar da zasu rabu, sai shehu ya cewa Yumfa "Ya kai Yumfa, hakika al'amarin ubanka ya kare, alamari gareka yake, kayi kokari" (Yana masa maganar mulki ne)
   Sai Yumfa yace, "Hakika idan na samu mulki, bazan aikata irin aikin da iyayena suka aikata gareka ba, don haka zanyi ɗa'a ga kowanne alamari"
  Daga nan suka rabu, Yumfa ya koma gida ya zauna abinsa.
  Kuma koda Nafata ya rasu, sai aka naɗa shi Sarki.
   Yayi hawa ya tafi ga Shehu Usmanu, kafin ya isa da tafiyar misalin mil guda, sai ya sauka ya taka a kafa bisa makirci. Ashe a zuciyarsa cike yake da fushin shehu da Jama'arsa.
   Koda Jama'ar shehu suka ga Sarki da kansa ya tako a kafa zuwa ga shehu, sai suka rinka cewa "Bamu taɓa ganin sarki kamar wannan ba"
 An ruwaito Shehu Abdullahi kanin Shehu Usmanu yana cewa "Ni kuwa banga komai daga gare shiba sai Makirci"
  Sarki Yumfa yace da Shehu " Bani aikata komai daga binda iyayena suka aikata gareka "
  Shehu Abdullahi zaiyi magana, Shehu Ummaru Alkammu ya hana shi, har sai bayan tafiyarsa sannan Ummarun ya faɗi ga shehu cewa "Hakika, faɗinsa bani aikata abinda iyayena suka aikata, ba komai ke nufi ba sai zaiga abinda iyayensa basu gani ba"
  Daga nan fa Sarki Yumfa na Gobir, ya shiga kulla miyagun dabaru ga shehu Usmanu, burinsa kurum ya halaka shi.
   Rannan, shima sai ya kira Shehu Usmanu izuwa fadarsa, alhali ya gina rijiya ya kafa masu acikinta, yasa an rufe samanta da tabarma.
   Shehu Usmanu ya taho tare da Kaninsa Abdullahi, da abokinsa Ummaru Alkammu.
   Abudullahi yayi nufin zama akan tabarmar da akace shehu Usmanu akayiwa tanaji, amma sai shehu ya hanashi, yaje ya zauna shi da kansa. Suka gama maganganunsu suka kare da sarki Yumfa, sannan suka koma gida ba tare da wani abu ya auku ba.
   To amma, sa'ar da shehu Usmanu yaga jama'a tayi yawa gareshi, ga kuma makircin sarakuna na karuwar musu, sai ya umarci jama'arsa su fara yin tanajin makamai.
  Yace musu " Tattalin makamai sunna ne"
  Sannan kuma sai ya shiga adduar neman nasara daga Allah.
  Shehu ya faɗa a wata wakarsa cewa
  "Allah ka gwada min rinjayar addininka ga garuruwan nan namu na sudan domin darajar Abdulkadiri"

No comments:

Post a Comment