Sunday, 10 December 2017

LABARIN BAWA DORUGU 4

LABARIN BAWA DORUGU; BAHAUSHEN
FARKO DAYA FARA ZAGAYA TURAI.
Kashi na hudu
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da bada labari da cewa "Bare-barin
nan sai dasuka bani suna. Daya ne ya tambayeni da
cewa menene sunanka sai nace masa Dorugu, sai suka
ce suna na 'Barka-ganna' da maganar borno. Suka raba
gidan da muke ciki biyu, dakin maza dana mata, bayi
suna daga cikin lolloki amma babu hanyar wucewa har
sai sunzo ta bakin kofar ubangijinsu. Ni kuwa koda
yaushe ina tafiya garesu. Ina yin zance dasu, muna yin
dariya da wargi. Ni kadai ake baiwa wannan damar
domin a lokacin bani da wayo sasai.
Ko wacce safiya idan nazo wucewa sai ubangijina yace
mini 'Barka-ganna mai dundufa'. Na kanyi dariya na
wuce wurin mata bayi. Amma ubangijina nada wata
baiwa sadaka, itace babba bisa ga bayi mata duka.
Rannan dana tafi garesu da marece sai ta kirani, ina
tsammanin zata fada mini maganar alheri ne, ashe
lalata take son yi dani. Tace mani 'ka taho' nace 'naki'
tace 'don me?' Nace 'ban sani ba' tace 'kana jin tsoro
ne?' Nace 'inaso in fita'. Sai ta hanani fita, tace idan
kafita, idan ka fadi ga kowa ina bugaka, sai nace da
kyau, bana fadi ga kowa.
Baya ga wannan, kwana daya ko biyu naji za'a aikeni
zuwa Borno. Nace 'ni za'a aika borno?' Suka ce 'I',
nace 'da kyau'. Suka bani tasa na zuba ruwa, suka
dorani bisa doki suka tafi tare dani, muna ta sauri
saboda suna son su iske wadansu mutane dake tare da
shanu.
Idan doki yayi gudu, sai kaji ruwan dake cikin gora yana
kara bulum-bulum, sai su hau dariya, suna yin maganar
borno, ni kuwa ban san me suke cewa ba, na zamo
kamar kurma. A haka har muka tarar da mutanen dake
tare da shanu, suka dorani bisa ga Sa, anan na samu
wani sarmayi yana yin magana da hausa, mukai ta fira
dashi har muka isa Borno.
Da muka shiga Borno, sai naga Babban gari ne. Suka
shigar dani wani gida, naga matar ubangijina fara ce
tar, sunan birnin borno Kukawa, daga zinder zuwa
kukawa kwanaki ashirin ne a kafa, tafiyan doki kuma
kwana goma. Matar ubangijina tana da diya shekarunta
hudu, dukkan su suna sona. Suna da bayi masu yawa.
Amman diyar matar ubangijina komai taci tana bani
saura, wani ciwo ya sauka gareta, sunan ciwon nan
Agana, ta zauna bata da lafiya sai ni ke zama kusa da
ita, komi takeso ina kawo mata.
Akwai kuma wata baiwa tsohuwa, itace keyin hankali
ga bayi, itama tana zagayawa wajen diyar ubangijina,
mu uku muka rinka zama harta samu lafiya. Rannan ina
daga cikin daki kusa ga bakin kofar gida, nahau tona
kasa, ina tsammanin zan samu ajiya, sai na tararda
wani abu mai Karfi daga karkashin sauran tukunya. Na
fitar dashi na bude, sai na taras kudi ne, danaga kudin
suna da yawa, ban ciri komai ba sai na ruga na tafi na
kira matar nan tsohuwa nace mata ga kudi na samu
amma bansan na wanene ba, ina magana da hausa. Ita
kuwa ba jin hausa, sai na jata na nuna mata, ta dauki
kudi duka ina tsammanin sun kai dari amma takwas ta
bani, ashe kudin wani mutum ne, ta tafi kasuwa tayo
siyayya dasu.
Ya akayi-ya akayi, masu kudi suka tambayi tsohuwar
nan ina kudi, amma sai tace musu nine na dauka,
nikuwa nace musu naga kudi amma itace ta dauka ta
bani takwas, suka zauna basuce komi ba.
Rannan na tafi wani gida inda wata mata take 'yar
garinmu, tana da yaro maijin hausa, amma komawarsu
sun fara mantawa. Sai matar ubangijina ta ganomu
muna magana dashi, sai tayi tsammanin inason nagudu
ne, shikenan ta dauki rigata da darme ga zaninta, nayi
ta kuka ina yin raurawa dajin tsoro, tace ga danta da
maganar borno "Ke ger kude sukagere" ma'ana kawo
mari ka darmeshi, a lokacin nima na fara jin maganar
borno.
Da naji haka, danta ya shiga cikin daki najiyo shi yana
taba mari, ina yin raurawa na kunche daurin da tayi min
a sannu, sannan na duqursa na rinqa mata afi ina
neman tuba, gashi bata jin hausa. Ala tilas aka nemo
wata baiwa maijin maganar hausa nayi mata bayanin
duka abinda ya faru sannan itama tayiwa uwargijiyata
bayani, sannan suka rabu dani.
A zamana na kukawa babu aikin da nakeyi, amma daga
baya sai aka maidani zuwa wajen gari wajen wani
sabon gida da ake ginawa, aka hadani da bayin
ubangijina, anan ne nake daukar kasa tare dasu suna
gina gida. Wani lokacin mukan tafi kiwon dawaki da
marece mu koma gida, wani lokacin kuwa cikin gari ake
turamu mu dauko tuwo muzo muci. Da borno sukan kira
sunan tuwo ''Brigashi''. Ko tuwo babu miya muna
hadashi da gishiri muci, don kowa nada gishiri a
aljihunsa, tuwon da akacishi da gishiri kuwa yafi mai
miya dadi. A haka har ubangijina ya karaso borno daga
zinder tare da wasu bayi masu yawa. Yana tafe ana
buga kalangu har cikin gari. Daya sauka mukaje muka
gaisheshi sannan muka dawo inda muke aiki.
Bayan kwana biyu sai wani yaron sa yake labarta mini
cewa ubangijina zai badani saboda bashi, nace dakyau,
daman naga wani bature yana zagayowa. Ashe kuwa
baturen za'a baiwa ni..
( A wannan lokacin Dr Bath da 'yan tawagarsa suka Isa Borno a tarihin tafiyarsu)

No comments:

Post a Comment