TARIHIN IMAM HASANUL BASRI: Gwarzon addinin Musulunci.
Sadiq Tukur Gwarzo
Musulunci bazai mance da Shehin masani Imam Hasanul Basri ba saboda gagarumar gudunmuwar sa wajen kafuwar wannan addini.
Ya kasance Tabi'i ne, an haifeshi a madina birnin musulunci shekara ta 642 miladiyya, 21 bayan hijira, dai-dai da shekaru tara bayan wafatin Annabi Muhammad s.a.w.
Mahaifinsa mai suna Yassar bawan Sahabi Zaid bn Thabit al ansari ne, mahaifiyar sa kuwa ana kiranta Khayyira, itama baiwa ce ga Uwar muminai Nana Ummu salama matar Annabi s.a.w. Dukkan su sunyi rayuwa ta addinin islama, sun kuma dukufa neman ilimi a zaman takewarsu.
Wani masanin tarihi Muhammad ibn Salam yace "Ummu salama ta kasance tana sanya mahaifiyar Hasanul Basri aikace-aikace har sanda aka haifeshi. Wani lokacin ma idan ta ajiyeshi tana yin aiki yakanyi kuka, har sai ta tsaya ta shayar dashi nono. Sannan akan fita dashi wajen da Sahabbai ke taruwa bayan wafatin Annabi, har ma watarana Sayyidina Umar R.A yayi masa addua da cewa " Ya Allah ka sanar dashi addinin ka, ka kuma sanya mutane su soshi".
Haka nan, an jiyo daga Imam Hassan din kansa yana cewa "Na kasance ina shiga d'akunan matayen Manzon Allah (s.a.w) har ma nakan tabo sorayen dakunan ina yaro a lokacin halifancin sayyidina Usman R.A. Inada shekaru 14 aka kashe shi."
Ance Imam Hassan ya girma acikin sahabbai, har ma ance babu wanda bai gani ba acikin sahabbai 70 da suka je yakin Badr tare da Annabi s.a.w. yaji hadisai da yawa a wurinsu, daya fara tasawa ne ya koma garin Basra, inda ya cigaba da neman ilimi, daga bisani kuma ya soma karantarwa a babban masallacin garin. Makarantarsa kuwa shahararra ce wajen amsa fatawowin ilimai; na addini dana falasifa.
Abu Hilal ya taba fadin cewa "Naji Al Hassan Basari yana cewa ' Annabi Musa yana rufe al'aurar sa a duk sanda yake yin wanka'. Sai wani da ake cewa Ibn Buraidah yace 'A wajen wa kaji wannan?' Sai Albasri yace 'a wurin Abahurairah'.
Haka kuma an samu cewa Imam Hassan yana kuka riris aduk sanda yake karantar da hadisin da Anas bn Malik ya ruwaito, wanda yake cewa "Ma'aikin Allah ya kasance yana tsayuwa kusa da wani itace a duk sa'ar da yake mana hud'uba, har ma yana jingina da bayansa. A lokacin da al'umma suka k'aru a masallacin, sai Annabi yace da sahabbai 'Kuyi mini mumbari mai hawa biyu', kuma abinda akayi kenan. Sa'ar da Annabi s.a.w ya mik'e akan mumbarin yana huduba, sahabi Anas yace ina cikin masallacin, sai muka ji wannan itace yana k'ugi, yana tayi-yana tayi, har saida ma'aikin Allah ya sauko gareshi ya rungumeshi sannan ya daina". Don haka da zarar Imam Hassan yazo nan a karantarwar, sai yakan ce " ya ku bayin Allah, itace ma yayi kukan rabuwa da Manzon Allah, alhali kune ya kata kuyi hakan".
Muhammad bn Sa'ad ya ruwaito a kundinsa na ilimi mai suna 'Al-Tabaqat' cewa "Al Hasanul Basri cikekken masani ne wanda ba'a shakku a zancensa, mai gaskiya ne kuma abin gaskatawa, bawan Allah ne mai neman sani, mai yawan bautar Allah, kuma mai kyawun surar jiki ne".
Imam Ibn Burdah ya fada cewa "Babu wani da yake kamanceceniya da sahabban Manzon Allah (s.a.w) sama da Hasanul Basri."
Imam Hassan gwanin zuhudu ne, ance baya kwana da kud'i a tare dashi sai dai idan zaiyi wata buk'ata dasu da sassafe. An taba jiyo shi ma yana rantsuwa da Allah cewa duk wanda ya daukaka kudi a rayuwar sa, sai k'imar sa ta ragu a wurin Allah. Sannan ya taba cewa "abokai guda biyu basuda amfani ga mutum sai idan ya rabu dasu, sune Dinari da dirhami".
Abu ja'afar Ar Razi yayi shaidar gudun duniyar Al Basri, a inda yace imam Hassan yana yawan kuka, har ma a kullum idan ka ganshi kana iya cewa wani mummunan labari aka shaida masa.
Haka nan, Khalid Ibn Safwan, makocin Imam Hasanul Basri ya fada cewa " Ban taba ganin mutum irinsa ba, kalmominsa sunyi dai-dai da aiyukansa. Shi yake fara aikata kyakkyawa kafin yayi umarnin a aikata, kuma shi yake fara hanuwa daga mummuna kafin yayi hani dashi. Ban taba ganinsa yana neman wani abu a wajen wani mutum ba, amma shi a kullum mutane na nema a wurin sa"
A fannin Ilimi da karantarwa, Imam Hassan gawurtacce ne, har takai ga ana kafa hujja da fadar sa. Mu'ath bn mu'ath yace "Na tambayi al Ashath cewa me yasa daka hadu da Atta baka tambaye shi komai ba?" Sai Al Ashath din yace " ay tunda na hadu da Al hasanul Basri, duk wani malami dana gani sai na ganshi karami a ido na"
Ance ma, wani ya taba tambayar Imam Atta din a game da karatun Alkur'ani mai girma yayin binne mamaci, sai Atta yace "ba'a koyar damu ba, kuma bamu taba jin hakan ba".
Sai kuwa wani dake wurin yace "al hasanul basri yace muna iya karantawa" Ai kuwa da sauri sai Atta yace "To kuyi aiki da maganarsa, domin babban malami ne".
An kuma samu cewa a lokacin da tsufa ya riski sahabi mafi jimawa a duniya Watau Anas bn Malik, idan an tambayeshi fatawa, yakan ce "Ku tambayi Hasanul Basri, domin shi yana tunowa, mu kuwa muna mancewa"
Haka kuma Abu Qatada ya fda cewa "..ban taba ganin mutum mai ra'ayi iri daya dana Sayyidina Umar ba misalin Hasanul Basri".
Allahu Akbar.
Imam Hassan ya shafe rayuwarsa wajen karantar wa ta addinin islama a garin Basra. Ya rasu yana da shekaru 89 kuma ance mazajen garin kaf saida suka ziyarci ta'aziyyarsa. Domin shi mutum ne wanda ya guji abin hannun mutane, wanda kuma mytanen keso.
Dafatan Allah ya rahamce shi amin

No comments:
Post a Comment