Monday, 11 December 2017

TARIHI: ZUWAN MUSULUNCI KASAR HAUSA (Labari daga Borno)

TARIHI ABIN TUNAWA: ZUWAN MUSULUNCI KASAR HAUSA.

   Tare da SADIQ TUKUR GWARZO
               08060869978
Wani mawaki yana cewa "wanda ya kiyaye tarihin wadanda suka gabace
shi, ay kamar ya kara shekaru akan shekarun sa".
Ance Akwai wani mutum can a borno, daga 'yayan sarakunan su, sunan sa
Dalama. Sai ya samu nasarar hawa kan karagar mulkin borno, shine ake
ce masa 'Maidinama', ma'anar kalmar shine 'sarki ma'abocin rinjaye'.
Ance sa'ar da yayi watanni akan karagar mulki, sai ya aiki wani
yaronsa mai suna Gujalo izuwa kasar Madina domin karbo musulunci.
Alokacin kuwa an tabbatar da cewa Sayyidina Abubakar Allah ya qara
masa yarda ne keyin halifanci. Dalilin hakan shine, tun kafin hawansa
sarauta, yana jin labarin musulunci.
   Lokacin da dan aike ya iske Khalifa, sai ya iske shi yaki yasha
masa gaba don haka baice masa komi ba. Sai khalifa yace kazauna nan,
daga nan bai tuna dashi ba, yana ta faman yaki da masu tawaye. Ana
kan haka ne sai dan aike ya mutu. Bayan Wata uku da kwanaki kadan, sai
Khalifa Abubakar (R.A) shima ya rasu.
   Daga nan ne sai Sayyidina Umar (R.A) ya zamo khalifa. Shine kuma ya
tuna da al'amarin dan aiken da aka aiko daga kasar hausa. Shine ya
nemi shawarar sauran sahabbai, kuma suka hadu akan aika dan aike izuwa
borno. Shine fa aka aiki Umarul Asi da takardu na alkur'ani wanda
akace Abdullahi dan Umar khalifa (R.A) ne ya rubuta da hannunsa, da
rawani, da garkuwa da hular sarauta, da sauran kayayyaki har ma da
akushi a matsayin kyauta daga Khalifa Umaru (R.A) izuwa Mai-nadinama.
   Sa'ar da dan aike tare da tawagarsa suka kusa zuwa borno, sai ya
aika borno a sanar. Da jin haka sai sarki da jama'ar sa suka hau
dawakai suka fito suka tarbi dan aike. Aka sanyawa Sarki rawani, aka
kuma sabunta sarauta tasa a matsayin Sarkin borno. Dan aike ya danka
kyaututtuka ga Sarki, ya zauna tare da mutane yana koyar dasu addinin
Allah, farillai da sunnoni da sauran mustahabbai. Mutanen borno kuma
suka cigaba da girmama shi matukar girmamawa, har ma suna cin ragowar
abincinsa don neman albarka. Mutane da yawa suka rinka yo hawa daga
wurare mai nisa domin ganinsa, wasu suna hawan saman runfuna don
ganinsa, wasu suna shafar tufafinsa don neman tubarraki. Shi kuma yayi
musu rubuce-rubuce da hannunsa don koyar dasu addini.
    A haka ya zauna zamani mai tsawo, har yaji labarin cewa mutane da
yawa a kasar hausa suna yabonsa, suna kuma kaunar ganinsa domin shiga
musulunci. Da yaji haka bai gaskata ba, sai ya tashi dan leken asiri
ya tura shi izuwa cikin kasashen hausa.
   Dan aike kuwa ya yawata sosai kasar hausa, ya samu labarin haka nan
ne, yaji yadda ake ambato da yabon Manzon Allah Annabi Muhammad
(s.a.w) don haka sai ya dawo ya sanar da Umar bn Asi gaskiyar abinda
ya jiyo. Daga nan ne Sai ya tashi rundunar mutanen sa mai dauke da
larabawa kimanin mutane dari uku a karkashin jagorancin Abdulkarim bn
Munkaila yace suje sukai musulunci kasar hausa.  Daga nan Abdulkarimu
ya nufo kano, yana daf da shiga sai ya tura dan aike, yace a sanar wa
mutanen kano cewa ga dan aiken dan aiken khalifan musulunci yazo
garesu.
    Daya shiga garin sai ya sanar dasu sakon daya ke tafe dashi. Sai
kuwa al'ummar kano suka amshi musulunci. Daga nan ya zauna tare dasu
yana koyar dasu shari'ar Allah. Yana yi musu rubutu. Ance baizo da
littafi ba daga wurin Umarul asi. Don haka wanda yake da burin koyon
rubutu mai kyau sai dai a turashi borno.  Alokacin kano bata gama zama
babbar alkarya ba. Mutanen kano sun rinka yi masa tambayoyi na
abubuwan da babu su a larabci. Kamar misalin su tunku, yanyawa,
gafiya, bodari da tsari. Amma sai yace shima bai sani ba, su bari sai
ya koma can gida zai tambayar musu.
   Yana nan haka, sai mutane ke bashi labarin wani gari dake kusa da
kano, sunan sa katsina. Mutane suka ce idan da sun ganka, da tabbas
sun bada gaskiya da abinda kazo dashi. Da jin haka sai ya tashi da
kansa ya nufi katsina. Mutanen katsina suka karbeshi sosai, shi kuma
ya koyar dasu musulunci. Amma ance bai rubuta musu alkur'ani da hannun
sa ba, wai dalili kenan daya sa mutanen kano suka zarce na katsina
sanin alkurani.
   Bayan wani lokaci, sai Abdulkarimu ya dawo kano. Daga nan ma bai
jima ba yace zai koma borno. Shine akace larabawa da kadan ne suka
bishi, ragowar suka zauna a kano suna aiyuka nagari ana basu girma,
sune kuma daga baya aka rinka kira  da suna sharifai. Ha kika
Abdulkarimu kafin barinsa kano ya nada Alkali, da limami, damai yin
yanka, damai koyar da yara addini, damai kiran sallah. Ya halatta musu
abinda Allah ya halatta, ya kuma haramta musu abinda Allah ya haramta.
   Daya koma wajen umarul asi sai ya sanar dashi labari, har da
abubuwan da mutane suka tambaya. Ance shima sai yayi jim, yace sai sun
koma ga Halifa. Bayan wani lokaci suka koma gida, kimanin watanni
shidda suka turo da sako a game da wadannan tambayoyi, aka hana mutane
cin wasu abubuwan, aka kuma halatta cin wasu. Amma dai ance
Abdulkarimu bai sake dawowa borno ko kano ba, shikuwa Umarul asi ya
samu nasarar zama sarkin Masar.
   Daga nan sai kasar hausa ta rabu biyu. Wasu suka rinka zuwa Kano
don sanin musulunci, wasu kuwa suka rinka tafiya katsina. Sai kasar
Kabi ne kurum suka ki shiga musulunci. Sarakunan su suka cigaba da
zamowa kafirai. Ga sunayen su ma; Barbarma, argaji, Tabariu, Garjai,
Gobari, dadafami,zartai, katari, Bardo,Kudamdam, shariya, karfu,
Darka, gunba, katatar, tamu. Sai da zaidu yaci sarautar kasar Kabi
sannan wasu suka musulunta. Ga sunayen sarakunan kabi na farko a
musulunci; Farinsu, Zaidu, Muhamadu,
Namakata, Sulaimana, Hisrikoma, Abdulahi,
Dunbaki, Alia,
Usmanu, Chisgari, Barbarmanaba, Muwashi,
Muhamadu-Karfi, Bata-Musa.
Bayan nan sai fumu yaci sarauta, sai ya koma kafirci. Wasu sarakunan
suka biye masa. Daga nan kuma sai Kanta yaci sarauta, shima sai ya
koma musulunci tare da wasu sarakunan masu yawa. Daga bisani Barbarma
yaci sarauta, sai ya kara komawa kafirci da jama'ar sa. Kafirci ya
wanzu har lokacin Hudu. Hudu kuwa shine wanda Usman Dan fodio ya yaka,
ya kuma koreshi. Buhari dan abdul Salami sarkin jega ya kasheshi a
kusa da garinsa. Har yanzu kuma zuriyar sarkin ke mulkin jega.
   A kano kuwa, musulunci yaci gaba da kafuwa bayan komawar
Abdulkarimu gida da shekaru da dama. Har lokacin da Mainabugabadi ya
karbi sarauta. Shine fa ya daukaka sarauta, ya kaskanta musulunci. Ya
maido da bautar gumaka. Yayi kafirci sosai har mutuwar sa. Daga nan
dan uwansa Kunbari ya hau karaga, yaciga da kafirci. Daga shi sai
Rumfa yahau karaga, shima yayi kafirci sosai. Shine ma ya auri mataye
1000. Yayi horo da arinka yi masa sujjada don gaisuwa gareshi. Ya bata
addini dukansa. Shine wanda ya gina gidan Sarautar Kano na yanzu. Amma
duk da haka, addini bai saki mutan kano ba. Ance basa shan giya sai
yan kadan. Matansu kuma Basa barin kawunansu babu lullubi.
   Daga bisani aka samu wani malami mai tsoron allah yana wa'azi.
Sunan sa Muhammadu Zari. Sarki rumfa baiji dadin hakan ba. Sai kuwa ya
kulla masa kutungwila. Ance da dare aka kasheshi a masallaci. Da safe
kuma wajajen lokacin sallar duha aka bizne shi a kabari. Kabarinsa
ance har yanzu yana nan a kano, ana ziyartar sa. Ana kiran sa da Mai
kalgo.
   Daga nan sai akayi wani malamin mai suna abdullahi. Shima yana kan
wa'azi Sarki yasa aka tsoratar dashi. Daman kuma ance babu mai
sauraronsa sai kaskantattin mutane. Daga nan sai ya gudu kauyuka yana
wa'azi. Acan ma sarki yasa aka kamo shi ana ta bugunsa, a haka ya
mutu. Kabarinsa yana nan bayan gwauron dutse, amma ba'a ziyartarsa.
   A haka dai kafirci ya wanzu a kano har lokacin sarki Muhammadu
alwali (auwalu). Shekarar sa goma sha bakwai yana mulki dan fodio yazo
yayi yaqi dashi ya kuma koreshi. Ba'asan inda yayi ba. Ance daga zuwan
Abdulkarimu izuwa zuwan Dan fodio, anyi Sarakuna Saba'in da shidda
akano. Dukkanninsu a kano aka binne su in banda Muhammadu Auwalu....

No comments:

Post a Comment