Sunday, 10 December 2017

TARIHIN ASALIN BAKIN MUTUM 6

TARIHI: ASALIN BAKIN MUTUM DA MAZAUNIN SA
    (Kashi na shidda)

DAGA SADIQ TUKUR GWARZO

  Koda yake, fadin cewa asalin mutanen da suka kafa egypt daga wani yanki suka zo mai suna 'punt' shine yafi shahara a duniya, binciken kwayoyin halitta da gidan ajiye kayan tarihi na kasar Egypt tare da hadin guiwar jami'ar California dake Kasar Amurka ya gabatar a Shekarar 2010 akan burbushin gashin wasu birrai da akace tarihi ya nuna an kawo su egypt ne kyauta daga yankin Punt ya bada haske akan yankin. Binciken ya nuna kamance-ceniya tsakanin gashin birran da akayi binciken akansu dana birarrikan dake rayuwa a yankin Ethiopia da Erithrea sama dana ko ina a sassan duniya. Wancan yanki kuwa idan ba'a manta ba nan ne inda garin Mazaber ya wanzu, anan kuma tarihi ya nuna daular bakar fata ta farko ta fara wanzuwa.
   Amma dai idan mun koma kan maganar da Marubucin littafin 'Travels to discover the source of Nile" watau James Bruce ya ruwaito a shafi na 305 na littafin nasa kamar yadda muka kawo a baya, cewa "bayan daukewar ruwan d'ufana, Cush (dan Hamu dan Nuhu) ya tafi da iyalansa izuwa gabashin tekun Nilu har ya riski tsibirin 'atbara' a lokacin babu wani abu mai rai a yankin. Daga nan kuma suka haye tsibirin suka riski yankin Aksum, inda suka fara zama.." Zamu fahimci cewar indai maganar da gaske ta inganta, to a wancan lokacin shi da zuriyar sane suka fara riskar wannan guri. Kamar yadda tana iya kasancewa wasu daga 'yan uwansa da sauran tsirarun mutamen da suka tsira suma sun tashi daga ainihin inda suka dira kuma suka fara zama izuwa wani wasu wuraren a sassan duniya.
    Maganar ruwan dufana dai tsayayya ce, littattafan mu na addini duk sun kawo shi. Kusan kowanne addini ya gaskata faruwar hakan.
  A kimiyance ne ake dan tababar tabbatarwar sa. Abaya can tun lokacin wani mai binciken tarihi dan kasar girka mai suna 'Eusebius' (275-339 miladiyya) ake bin diddigi ba tare da an samu wata kwakkwarar shaidar aukuwar sa ba. Amma dai a yanzu, muna iya cewa an dace, tunda dai masanin akiyolojin nan wanda ya binciko jirgin ruwan 'Titanic' mai suna Robert Ballard ya shaidawa kafar yada labaru ta ABC cewar an samu hujjar data tabbatar da wannan abu a kimiyance.
  Ga abinda yake cewa " mutane da yawa suna ikirarin sun gano hujjojin da suke tabbatar da aukuwar ruwan dufana da kuma gagarimin jirgin da Nuhu A.S ya shiga shida mutane da kuma jinsin mace da namiji na kowacce dabba. Amma dai a shekarar 1990, wasu masanan kimiyyar k'asa Wilham Ryan da Walter Pitman sun kawo hujjojin dake nuna aukuwar abin a yankin gabas ta tsakiya, wuraren shekaru dubu bakwai da dari biyar da suka gabata"
   Binciken nasu ya nuna a yankin Turkey jirgin Annabi Nuhu A.S ya sauka. Don haka har yanzu gungun masana na cigaba da gudanar da bincike.
  Idan kuwa haka ne, idan har lissafin shekarun ruwan dufana da masanan suka bayar ya inganta, muna iya cewar gaskiya ta fito cewa bayan daukewar ruwan dufana da wasu shekaru masu yawa, wasu yankuna da dama a duniya aciki harda egypt duk akan ruwa suke. Har ma sai da rayuwa tayi nisa a wasu sassan sannan garin na egypt ya kafu.
   Sannan, muna iya fahimtar cewa Cush dan Hamu ya samu zama ne na tsawon wasu shekaru a inda ya riska, tayadda har saida zuriyar sa tayi yawa a inda ya zauna, sannan sannu a hankali mutanen wurin suma suka tashi gami da sake nutsawa cikin duniya, a haka- a haka ne har garuruwa suka rinka samuwa, a haka biranen bakaken fata dana indiyawa da sauran tsoffin kabilu suka wanzu, kuma egypt ma ta a haka ta samu.
   A yanzu haka dai, labarin kafuwar egypt da al'adunta ne ya mamaye ko ina a duniya. Har ma muna iya cewa ya shafe na girka wadda itace usulin turai.
  Dalilin haka ba komai bane sai wanzuwar ilimai da kuma rubutaccen tarihi da aka samu a egypt din.
  Malumman Girkawa da yawa misalin su Homer, Herodutus, Diodura Siculus da wasunsu ma da dama sunje egypt daukar Ilimi. Sun sanya egypt kuma a littattafan su na ilimi. A yanzu haka kuma a hannun girka mafi yawan ilimin zamani yazo. Ban sani ba ko an fahimci yadda lamurran suka sauya..
   Ba'a maganar tsoffin biranen bakaken fata da suka girmi egypt a yanzu. Birane da yawa sun wanzu bayan ruwan dufana wadanda a yanzu an mance dasu. An shafe su, babu kuma tarihi rubutaccen akansu. An mance da biranen 'Mazaber' wanda littafin 'Liber Axumae' yace Itiyopis dan Cush ne ya kafa da kuma 'Meru' wanda littafin 'The puranas' ya bada labari a matsayin asalin daular kushawa kafin komawar ta birnin Meroa. An mance da biranen Yeha dana Dukki gel, dukkansu shahararru ne shekaru aru-aru da suka shude, kuma bakaken fata ne tamfatse a cikin su. Shi kansa Meroa wanda anan-nan yankin kasar Sudan ya kafu an mance dashi.
  Gari hamshaki irin Meroe, wanda sai daya mulki egypt, sai daya zarta egypt kere-kere, ilimi, karfin iko da komai ma. Sannan kusan duk abubuwan da aka samu a egypt a yanzu haka Charles Bonnet da yan tawagar sa na samun kwatankwacin su a inda suke hako tsohon garin na Meroe. Abinda ke kara tabbatar da maganganun masanan da muka kawo kenan na cewa wayewar egypt daga garin na meroe take. Ko kuma ace kowannen su ya samu wayewar sa dai-dai gwargwado.
    Bakaken fata gaba daya an sauya musu tunani da tarihi. Komi nasu na tarihi, al'ada da zuri'a sai ace ana hasashen asalin sa daga egypt yake, ko kuma daga wani garin fararen fata yale, alhali egypt din kanta daga biranen bakaken fata ta samu mafi yawan wayewar da take takama dashi. Sannan bakaken fata sun kaiwa makurar da a duniya ko Girka da Rum albarka.
   Daular bakaken fata ta wanzu dubunnan shekaru a wuraren kasashen Ethiopia, Ereathrea, Sudan da Somalia. Ada can iya nan ake samun manyan biranen bakaken fata, amma a hankali sun rinka fantsama izuwa sassan afirka dama wasu sassan duniya. Littafin Races of Africa na C. G Seligman (1966) ya fadi fahimtar sa akan yadda bakin mutum ya fantsama izuwa sassan afirka daga ainihin biranan sa, ciki harda nan yankin da muke zaune. Ga abinda ya rubuta a littafin, shafi na 30...

No comments:

Post a Comment