Monday, 11 December 2017

TARIHIN KAFUWAR GARIN GETSO

TARIHI: ASALIN KAFUWAR GETSO
Gabatarwa
Littafin 'Mazan Kwarrai' shine wanda Marubuci IBRAHIM BALA GWARZO ya k'addamar dashi a wajajen shekara ta 2000, wanda ya tattaro tarihin kafuwar garuruwa da suke a tsohuwar K'asar Gwarzo. Bisa bukatuwar wannan tarihi da muke dashi, kuma bisa bukatar yad'a Ilimi, yasa ni (Sadiq Tukur Gwarzo) neman sahalewar Marubucin domin rubuta wani yanki gami da yad'ashi ga al'umma. Hakika marubucin yaji dadin haka, ya kuma sahale min izinin yin hakan. Godiya da fatan alheri a gareshi.
Asalin Garin Getso
Garin getso tsohon Gari ne, kuma tarihin sa mai yawa ne, amma dai daga abinda muka samu shine ya samu kafuwa tun kafin garin Gwarzo ya kafu. Ance wani Bamaguje ne mai suna 'Babbaka Toro' ya fara saran garin, watau ya fara yin bukka ya tare a yankin, don haka muna iya cewa shine wanda ya kafa garin, kuma shine Sarki na farko.
Sai dai kuma, abinda aka samu shine, wannan mutum a wani wuri ya zauna yamma da inda garin getso yake a halin yanzu, wancan wuri nan ne asalin Getso, har ma ance akwai wata Jar rijiya da har yanzu tana nan yamma da garin Getso inda akace anan ake sare kan masu laifi a tsohuwar getso. Daga baya ne mutan garin sukayo kaura zuwa inda suke a yau.
Bamagujen nan Babbaka Toro nada 'ya'ya uku, sune Yabani, Dosare, da Dungure. Ance manyan 'ya'yansa sune Yabani da Dosare, kuma dukkansu yayi musu gidaje a yamma da nashi, amma karamin mai suna Dungure, nasa gidan yana arewa ne da gidan mahaifinsa. Lokacin da Babbaka toro ya mutu, sai dansa Dosare ya gajeshi, sai shima ake masa lakabi da Babbaka Toro, wannan na nufin asalin sarautar Getso sunan ta Babbaka Toro.
Bayan rasuwar Dosare ne akayiwa Dank'arya sarautar Babbaka Toro, shikuma d'an wajen Dungure ne. Daga nan ne kuma saiwani Bafillatani mai suna Amadu wanda asalinsa mutumin D'ange ne ta k'asar Sokoto yazo Getso da zama. Ganin yadda wannan Bafillatani yake da ladabi da kuma karimci, sai yasa Babbaka Toron Getso D'anK'arya ya janyo shi a jiki, harma yayi masa sarautar Galadima, bayan rasuwar D'ank'arya kuwa, sai mutane suka zabi Amadu a matsayin wanda zai gaji sarauta. Kenan, muna iya cewa wannan shine asalin yadda fulani suka riski garin getso har kuma suka amshe sarautar ta.
Akwai wata unguwa a garin Getso, sunan ta Nini (Niniyawa). Asalinta wani bafullatani ne mai suna Niniya ya kafata. Shi mutumin jaulere ne ta k'asar shanono, kuma sun samu sab'ani ne da dagacin Shanono, don haka sai Niniya ya tara yayansa, barorinsa da shanunsa ya taso su a gaba ya baro shanono, ance kudu yayi niyyar nufa, sai dai yana daf da shigewa ta Getso sai labari ya iske San-Getso na wannan lokacin mai suna 'Maigada'....

No comments:

Post a Comment