Sunday, 10 December 2017

LABARIN BAWA DORUGU 2

YAKE-YAKE DA KAMEN BAYI A KASAR HAUSA: LABARIN BAWA DORUGU; BAHAUSHEN FARKO DAYA FARA ZAGAYA TURAI.
Kashi na Biyu

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Da muka zauna kamar shekara daya, sai muka kara jin labarin yaki daga wani gari izuwa garemu. Sai muka gudu muka tafi daji, amma ba nesa ba daga garin mu. Muka kwana a daji, daa Safiya tayi mika ga mutane fulani bisa ga doki nesa daga garemu, kamar dai mun ganesu, muka hau saman bishiya muna lekensu.
Muna gani wasu mutane suka sakawa wani gari dake makwabtaka da namu wuta sai hayaki kawai ke tashi, sannan suka tafi. Sai can wani yaro yace ya hango wasu mutane na zuwa da gudu izuwa garemu, domin sun hangoshi bisa ga bishiya. Daya fadi haka, sai ubana da wadansu mutane suka tafi don su tarbo su. Da suka gamu a cikin lukuki, sai suka ce musu "namu ko ba namu ba?". Mutanen nan kuwa su biyu ne, sai suka amsa da cewa "naku". Shikenan sai suka dungumo suka dawo garemu.
Duk kanmu sai muka dau murna, don munsansu. Muka tambayesu "yaya kuka san muna nan" sai sukace ai sun hango dayn mune bisa ga itace. Muka tambayesu labarin cikin gari, suka ce mana wadansu an kashe su, an jiwa wadansu rauni,wadansu kuwa an kame su a matsayin bayi. Muna gani mukaga wadan sutane na daukar dukiyar su suna komawa garuruwansu. (Sunan garin da fulani sukayi fada dashi Shagari)
Bayan sun bamu wannan labari, sai muka dawo muka zauna a garin mu tunda yakin bai karaso mana ba. Ba'a dade ba kuma, sai muka kara jin labarin yaki, akace wai Sarkin Borno shaihu umar yana zuwa don yin fada da wani gari mai suna kanche. Daya tafi ba'a gane shiba, sai da rana tayi aka ga kurarsa, aka samu yayi fada da sarkin kanube ya basu kashi ko ya bugesu, yasa wuta ga garinsu ya dawo ga garinsa. Ya kuma kwashi dukiyarsu mai yana, suna tafe suna buga bindiga, har ma muna jiyo karar daga garinmu Dambanas. Haka ma da suka isa ta wani gari mai suna Tasau sai da sukayi fada dashi. Mutanen Tasau sun iya fada kamar wuta, kuma ba'acisu da yaki ba, sai Sarkin Borno ya wuce garinsa, ashe akwai dakarunsa da basu tafi ba.
A wannan lokacin, akwai yunwa, don haka sai mahaifin Uwata yazo ya dauke uwata. Yace da ubana "bani barin diyata gidanka, kada ta mutu da yunwa". Muna kuka dani da kanena, ya dauketa izuwa wani gari, sunansa Bangasa, inda ya aurar da ita ga wani mutum, amma bata sonsa. Takan gudu ta komu gidan ubana, mahaifinta ya zaga ya maida ita.
Rannan dai ta dauki furar da baiwata ta dama zata kaiwa ubana a gona, sai ragowar bare-barin nan da basu tafi ba sukayi arba da ita, sai suka kamata suka tafi da ita. (Shikenan ta zama baiwa).
Da ubanmu yaji labari, sai ya fadama cewa "uwaku fa an kameta", shikenan, sai muka dau hakuri. Ba'a dade ba sai ubana ya dauki kanena ya bada shi ga wani mutum dake zaune a tasau, yace masa "ka maisheshi kamar danka, kada ka maida mani shi sai na gamu dakai a lahira". Nayi kuka sosai, na zauna ina cewa a zuciyata, idan na girma bazan bar kanina acan ba.
Ban fada maka ba, (dorugu yake fadawa bature) kanina a lokacin shekararsa shidda ko bakwai. Idan na tafi yanzu ban sanshi ba, amma na sanshi ga shaushawa, amma shi bazai iya sanina ba sai idan nine na fada masa.
Bayan mun zauna sai muka ji labarin wani sarki mai suna Taniman yana zuwa zai wuce ta garin mu. Da mukaji haka sai mutane sukayi shiri, da dare yayi mukaji tafowarsa, mutanen garinmu suka jefa gagara-badau mataushin kofa, ko itace da ake sanyawa a gicciye bakin kofar birni. (Watau kenan garin dambanas nada ganuwa harda kofar gari).
Sarkin yace mu barshi ya shiga, amma muka ki. Sai yayi fushi ya wuce. Wadansu tsoffi sun gaji, sai suka zauna daga bayan birni muka same su anan da safe. Ga wakar ma da suke yiwa sarkin nasu.

"Dare, Dare, 'yan kwarugom,
Dare, Dare, kadan bakusan dare,
Kura taciku, babu maceci a kusa,
Taniman mai bindiga,
Na Yaya, Yado ba Jini"

A shekarar nan me muka ji cewa mutanen borno sun shiga cikin garin kanche, har sarkin kance ya basu damar suzo suci garin mu da yaki, amma ya fada musu cewa suyi hankali koda zasu cimu, sai kuwa sukayi mana wayooo.. Da gari ya waye suka zagaya dai-dai suna shiga cikin garin $u, ubana yace mini intafi in boye daga cikin ciyawa, sai kuwa na gudu bakin ruwa na boye a cikin ciyawa....
#SadiqTukurGwarzoYAKE-YAKE DA KAMEN BAYI A KASAR HAUSA: LABARIN BAWA DORUGU; BAHAUSHEN FARKO DAYA FARA ZAGAYA TURAI.

#SadiqTukurGwarzo

No comments:

Post a Comment