Sunday, 24 December 2017

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU DAN FODIO 6

TARIHIN JIHADIN SHEHU USMANU MUJADDADI, DAN FODIO.

SADIQ TUKUR GWARZO, RN.
     08060869978

Kashi na shidda.

YAKIN ALWASA
  Daga nan Sabon gari, Wazirin Shehu Usmanu Dan fodio watau Abdullahi, ya ɗauki runduna ya tafi kasar kabi da yaki, Allah kuwa ya bashi nasara, yaci garuruwa da yawa har ma aka kira yakunan da yayi da suna 'yakin ciye-ciye'.
    Daya komo sabon gari ya taradda sauran jama'a, sai suka tashi izuwa Bukkuyum, sannan suka yi Bunkasau, daga nan sukayi Felan, sai suka shiga Gazurra, sannan suka auka Margai, sai suka isa Rafin Samu, sai kuma gasu a Gwannu.
   Shi wannan yaki da ake kira na Alwasa, azbinawa ne da Gobirawa da sashen dakarun kasashen Hausawa, karkashin wannan babban sadaukin mai suna Abungulu, suka taru tare da nufo Shehu Usmanu da rundunarsa da yaki.
    Koda Rundunar shehu Usmanu ta samu wannan labari na yaki dake zuwa garesu, sai suka shiga shawara, wasu sukace a tashi aje a taryesu a gwabza yaki, wasu kuma sukace a dakacesu su karaso.
   A karshe suka sauraresu, runduna tazo har inda suke ta kafa sansani, sannan dakaru suka firfito, sashensu ya fuskanci sashe. Ba tare da ɓata lokaci ba aka shiga gwabza yaki.
   A wannan rana ma, hakika Allah ya jarrabci Shehu Usmanu ɗan fodio da rundunarsa, domin ance kimani mutane dubu ɗaya ne daga rundunarsa suka rasa ransu a wannan yaki.
   Sun fara gwabza yakin ranar lahadi ne, sannan litinin aka sake wani, talata ma haka, laraba ma akayi, aka sake wani ranar Alhamis..
  Shehu Usmanu yace da mutanensa "Da sannu Allah zai kunyatar da Abungulo".
  Ai kuwa sai da Allah ya taimaka, rundunar shehu Usmanu ta warwatsa wannan runduna, Abungulo da jama'arsa suka ɗai-ɗai ta, kuma bai sake dawowa da yaki ga rundunar Shehu Usmanu ba har Allah ya karɓi rayuwar Shehun.
   (Shi Abungulo buzu ne, sarkin kano Alwali ya sake gayyatarsa bayan ya kasa samun nasara a wancan yaki, ya bashi dawakai dubu huɗu da nufin yazo ya fatattaki masu jihadi na Kano ya kone gidajensu. Daga karshe ya haɗu da ajalinsa a wani yaki da suka gwabza da masu jihadi a Kano kusa da wani gari mai suna Tatarawa kamar yadda Qadi Muhammadu Zangi ya ruwaito a littafinsa Taqyidil Akbar)
    A shekara ta biyu da hijirar Shehu Usmanu akaci kano da yakin jihadi, aka naɗa malami adali Sulaimanu a matsayin sarkinta.
   Acikinta kuma akaci 'yandoto, wata shahararriyar alkarya mazaunar malumma.
   A shekara ta uku da hijira akaci katsina da yakin jihadi, aka naɗa Ummaru Dallaje sarki.
  Acikinta musulmi sukayi yaki da Borno, suka cinyeta, aka naɗa Mallam Zaki Kanuri shugaba, aka naɗa Mallam Yakubu shugaba a Bauchi, Mallam Ishaka a Daura, Mallam Buba yero a Gwambe, mallam Adama a Adamawa, da wasunsu kamar Larliru.
   A cikinta kuma ne Shehu Usmanu da jama'arsa suka sake kawowa Alkalawa babban birnin Gobirawa hari, amma ba'a samu damar cinye garin ba.
   Amma dai, acinkinta har ila yau akaci Mazauri da Kannu da yaki.
   A shekara ta Huɗu da hijirar shehu Usmanu aka samu nasarar cinye Birnin Alkalawa da yaki. A lokacin kuwa farkon shigar kaka ne, Muhammadu Bello ya fita yaki zjmuwa gareta, ya sauka a Lajingo, yayi kwanuka anan, sannan Ranar lahadi ya sauka kusa da alkalawa, ya kwana, da wayewar gari ya shiga yaki da Gobirawa, Allah kuwa ya buɗa masa ya shiga birnin Alkalawa, abinda a baya ya gagaresu.
   A wannan rana aka halaka sarkin Gobir Yumfa, aka kashe mazajensa da yawa, aka kama mahaifiyarsa mai suna Maitakalmi, sannan aka taso keyarta a gaban shehu Usmanu, sai dai kafin azo gareshi tuni har wani Aljani ya riskeshi da labarin wannan gagarumar nasara.
A shekarar ne dai akayi yakin Banna, aka kuma cinye Gandi dukanta. Aka naɗa Mallam Musa zazzau shugaba.
  A shekara ta biyar da hijirar Shehu musulmi suka ketare tafkin kwara da yakin jihadi, suka kafa dauloli acan.
  A shekara ta shidda da hijira shehu ya tashi daga Gwandu zuwa Sifawa da zama. A shekarar aka gina sokoto.
  A cikinta akaci Zabarma da yaki, da Gurma da Kasar Nufe, da kasar Gwari aka kamo sarkinsu a kukume aka tawo dashi Sifawa. A shekarar kuma akaci Borno dukanta.
    A shekara ta bakwai da hijira akayi yakin garin Kwatto, amma ba'a cishi ba, sai dai an samu ganimar yaki mai yawa da arziki a shekarar.
  A shekara ta takwas akayi yaki da Salihu ɗan Babari wanda ya abokanci azbinawa suka kawowa Jama'ar shehu hari.
A shekara ta tara da hijira Hamman ya fita daga Magunga yana cewa shi Mahadi ne, ai kuwa mutanen shehu Usmanu sukayi masa tsinke suka halaka shi.
   A cikinta Jelani ya Azabtar da Azbinawa da hare-hare, suka karɓi hukuncin abinda suka daɗe suna aikatawa ga Shehu da Jama'arsa.
   A shekara ta goma da hijira yakunan jihadi suka je har Bargu.
   A shekara ta goma sha ɗaya da hijira, shehu Usmanu ya baro Sifawa izuwa Sokoto da zama. Ya raya garin tare da mayar dashi shigifar musulunci.
A shekara ta goma sha uku Shehu Usmanu ya soma ciwon ajali.
  Ashekarar ne al'almarin Gagara ya auku.
  A shekara ta goma sha huɗu da hijira Allah ya karɓi ran limamin yakin jihadin tabbatar da Sunnah a kasashen hausa da makwabta, watau Shehu Usmanu mujaddadi ɗan fodio.
 Ya rasu ranar 3 ga watan jumada Auwal, 1232 bayan hijira.
  Da fatan Allah ya rahamsheshi Amin.
  Karshen Takaitaccen Tarihin Jihadi kenan.
 Sauran abinda zaizo bai wuce sanin Yadda sarautar sarkin Musulmi ta kasance ba da kuma gwagwarmayar Rikon sarauta.

No comments:

Post a Comment