TARIHIN HAUSA DA BAYANIN KATSINA
( Mahanga ta farko, kashi na farko).
Sadiq Tukur Gwarzo ne ya rubuta ga zauren binciken tarihin Hausa.
Wannan bayani ya samu ne daga hannun Dr. Barth wanda yayo tattaki tun daga Jamus izuwa cikin kasar hausa a wajajen shekara ta 1850. Dr Barth ya tuntubi tarihin kafuwar hausa da garuruwan ta daga bakunan masana na lokacin, ga kuma abinda yake cewa:
Kalmar 'Hausa' ba'a santa ba kamar yadda na lura da cewa masanin tarihi, kuma marubucin shahararren littafin tarihin afirka mai suna Leo Africanus bai taba ambatar taba.
Maimakon cewar dayayi al'ummar garin zaria, katsina, da kano suna amfani ne da yaren Gobir, da zaice suna amfani da yaren hausa.
Sai dai duk da haka, bamu da ikon yanke hukuncin cewar sunan Hausa ya samo asali ne a wani lokaci bayan gushewar Leo Africanus. Wannan hasashe ne kurum wanda ba lalle ya zamo gaskiya ba.
Amma dai, muna iya cewa kasar hausa ba dad'ad'd'iya bace wadda tun tale-tale take nan, kuma aka santa a wurin da take ba, kawai dai zamu iya cewa tazo inda take yanzu ne daga baya.
Da yake daya daga cikin jihohin hausa, wadda kuma ta shahara (ina nufin Gobir) mun santa tun da jimawa tana zaune ne acan arewaci, kuma an tabbatar min da cewa sunan 'Hausa' ya samo ne daga wannan harshe na gobir din Tamashit. Ana ma tsammanin asalin sunan 'Ausa' ne ba 'Hausa' ba. Abinda Ausa ke nufi kuwa da yaren kudancin Tuareg da kuma a wajen mutanen Timbuktu shine 'Arewa'. Kishiyar sunan shine 'Gurma', abinda kuma ake kiran kasashen kudancin babban teku kenan.
Bayanin da Sultan Bello ya fada cewa Hausawa asalinsu bayin Borno ne, babu sahihiyar hujja ko inganci a ciki. Tunda a yaren hausa, kalmomi kadan ne suka zo d'aya da yaren kanuri na mutan borno. Sannan karin magana, wakoki da sauran zantukan adabi duk sunsha bam-bam da juna.
Sai dai, zancen na Sultan Bello na iya zamowa gaskiya ta wani fannin idan muka kalli yawan al'ummar garin kano, da yadda garin ke kunshe da ababen borno da dama, watakila wasu na iya cewa lokaci ne ya sauyawa al'ummar kano harshe daga kanuri izuwa hausa.
Kalmar 'Bawo', wadda ta fito a matsayin sunan uban jihohin hausawa na iya zamowa alamar kasancewar yankin acikin bauta. Ainihin Sunan Bawa da harshen hausa shine 'Mowa', amma daga baya sai ya koma 'Bawa' daga 'Bawu'.
Shikuwa Bawu, ance mutum ne sunan ubansa Karbagari. Sunan dake nufin 'kwace-gari' da yaren hausa. Sunan na iya zamowa ne daga 'kwace garin biram' (watau uban Bawo shine wanda yayi jagorancin kwace Birnin Biram). Garin Biram kuwa a nan ne akace tsohuwar daular hausa ta asali ta kafu. Kuma ana kiran sane da suna 'Biram ta gabas' domin banbance shi da wasu garuruwan kudanci masu suna 'Biram'. Sannam an tabbatar da cewa garin ya wanzu ne a tsakanin Inda garuruwan kano dana Hadeja suke a halin yanzu.
No comments:
Post a Comment