Sunday, 10 December 2017

TARIHIN ASALIN BAKIN MUTUM 7

TARIHI: ASALIN BAKIN MUTUM DA MAZAUNIN SA
    (Kashi na bakwai)

Daga SADIQ TUKUR GWARZO

 Daular bak'ak'en fata ta wanzu dubunnan shekaru a wuraren kasashen Ethiopia, Ereathrea, Sudan da Somalia. Ada can iya nan ake samun manyan biranen bak'ak'en fata, amma a hankali sun rinka fantsama izuwa sassan afirka dama wasu sassan duniya.
   Littafin Races of Africa na C. G Seligman (1966) ya fadi fahimtar sa akan yadda bakin mutum ya fantsama izuwa sassan afirka daga ainihin birnin sa, ciki harda nan yankin da muke zaune.
  Ga abinda ya rubuta a littafin, shafi na 30, " binciken masana akiyoloji ya nuna soma-war bakin mutum mai yankakken gashin kai a wuraren shekara ta 300 kafin aiko Anbabi Isa A.S. Taswirar kasashen bak'in mutum na afirka ya soma ne daga Iyakar gab'ar tekun Senegal izuwa Timbuktu zuwa Khartoum, sannan yayi kudu da yamma na arewacin iyakar Kasar Ethiopia, daga nan kuma ya nufi yamma da kudancin iyakar k'asar ta Ethiopia, sannan ya zagaya Tekun Juba izuwa Tafkin India."
   Yaci gaba da cewa " Mutanen daji sune abinda bakaken fata suka samo asali. Mutanen dajin kuma sun rabu kaso uku.
1. Kaso na farko sune kason kudu, wadanda sukayi kaka-gida a yankunan South Africa
2. Kaso na biyu sune kason Arewa, wadanda suka barbazu izuwa arewaci da gabashin afirka ta yamma. Misalin k'abilun Huikum, Aven, Kung da wasunsu.
3. Kaso na uku sune Kalahare, wadanda suka hadar da kabilun Tennekwe, Hukwe, Galikwe, da wasunsu"
   Mr Seligman ya kara da cewa " ana samun wadancan mutane ne kimanin guda hamsin a duk rukuni. Kowanne rukuni kuma suna da yare nasu daban dana wasunsu. Babban makamin su shine kwari da baka masu dafi. Asalin su farauta kurum sukeyi banda noma. Suna fita farauta gami da kamo dabbobi, su hura wuta da dutse tare da cin abinda suka kamo a tare. Amma dai duk wanda ya kashe dabba, shine mamallakin fatar jikinta.
   Tufafi yayi musu karanci, don haka tsiraicinsu kurum suke rufewa. Idan dayan su ya mutu, sukan binne gawar kusa da bukka, tare da duk abinda mutumin ya mallaka, gami da dora babban dutse a saman kabarin don gudun kada dabbobin daji su tono gawar. Idan sukayi haka sai su tashi daga wannan guri da akayi mutuwar, suyi nesa da gurin na tsawon wasu shekaru.
  Ya kara da cewa "ana samun masu bada magani acikin su. Sannan akwai karancin sani dangane da maganar addinin su ko al'adun su, ance dai suna addu'a ga wata da taurari. Kuma rawa abar yi-ce ga kowannen su".
   A fahimtar sa, wannan shine silar da bakaken fata suka rinka gangarowa a hankali-a-hankali har suka riski inda ake samun su ayau cikin afirka kamar yadda ya fadi taswirar mazauninsu a sama
   Watakila, muna iya daukar abinda kundi na shidda na littafin 'Merit student encyclopedia' ya fada akan kafuwar kasar egypt a matsayin hujjar dake nuni da gaskiyar maganar C. G Seligman wajen kafuwar manyan birane gami da nutsawar mutanen-da- suka gabace mu cikin afirka. Ga abinda littafin ya ruwaito:-
   Mazaunan Egypt na asali suna rayuwa ne rukuni-rukuni kuma a rarrabe, inda suke farautar dabbobi da tsirrai don ci.
   A wuraren shekara ta 5000 kafin zuwan Annabi Isa A.S, mutanen suka fara zama a yankin na egypt. Kowanne rukuni nada shugaba. Binciken da akayi a yankin Faiyum na egypt din kuma ya nuna cewa mutanen na rayuwa ne acikin bukkoki da aka gida da turbaya, suna rufe gidajen nasu kuma da irin dogayen ciyayin nan masu fitowa a bakin ruwa (reeds).
   Haka kuma, al'umnar kasar kenya sun gamsu da irin wannan hanya a matsayin yadda kasar su ta tumbatsa da mutane. A cewar su, kabilar kushawa da kabilar Bantu ne suka fara matsawa izuwa yankin kasar ta kenya shekaru dubu shidda da suka gabata. Dalilan motsawar mutanen izuwa yankin kuwa sune:-
  1. Neman abinci da abinsha
  2. Kubuta daga Kafewar ruwan sha gami da k'arancin ruwan sama
  3. Bullowar annobar cututtuka...

   Wani marubuci ma, mai suna Mattew Brookings ya fadi nashi hasashen akan dalilan dayasa bakaken fata suka fantsama daga ainihin inda aka sansu acan baya izuwa inda suke a yanzu a wani rubutu nasa mai taken ' Ancient world History'. Ga abinda yake cewa "Al'ummar bakaken fata na kushawa na samar da k'arafa masu inganci a matsayin makamai.. Watakila neman karfe na daga cikin silar barbazuwar su izuwa afirka ta yamma".
   Amma dai, marubucin littafin 'From Hunters to Farmers', Desmond J. Clark yafi gamsuwa akan cewa farauta ne usulin dalilin daya baro da bakin mutum izuwa yankin da ake samun sa a yanzu daga ainihin mazaunin sa..

No comments:

Post a Comment