TARIHIN TSOHON GARI DUTSEN DAN-BAKOSHI.
DAGA
SADIQ TUKUR GWARZO, RN, GGA.
Wani mutum da ake kira 'Ɗan bakoshi' ne akace ya kafa wannan gari mai tsohon tarihi na dutsen ɗan bakoshi shekaru da dama da suka gabata.
Wasu sunce daga katsina yake, amma dai tsohon kundin nan mai ɗauke da tarihin kano da ake kira 'Kano chronicle' ya kawo cewa " (jama'a) Tun daga Tuda zuwa Ɗan-baƙoshi, daga Duji zuwa Ɗankwai, dukkansu suna taruwa wurin Barbushe a daren Sallah biyu dashi, domin shi ne babbansu a cikin tsafi" wanda hakan ke nuna cewar garin ya kai kwatan-kwacin shekarun kano kuma akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin mazaunan garuruwan biyu tun asali, haka kuma a mafi shaharar zance shine 'ɗan bakoshi ' bamaguje ne, ɗan kabilar kutumbawa waɗanda suke cikin mazaunan kano na farko.
A hakika, babu takamaimen zancen dake nuna garin ya girmewa kano, amma dai ɗaukacin masu bada tarihin garin sun gamsu da cewa akwai alakar kut-da-kut tsakanin aljanna Mararraka da Aljana Tsumburbura wadda aka bautawa a saman dutsen dala ɗaruruwan shekaru da suka gabata.
Ance garin ya shahara a zamanin da, yana da ganuwa gagaruma, kuma ba'a taɓa cinsa da yaƙi ba, wanda ya sa mutane daga sassa daban-daban suke niƙar gari domin shigewa ciki saboda neman mafakar kamen bayi da yake-yake.
Wani abin dake sanya mutane zuwa garin ma a zamanin-da shine shaharar Aljanna Mararaka, wadda akace gidanta na saman babban dutsengarin da ake yi masa laƙabi da 'Dutsen ɗan bakoshi', wanda yake a bayan ganuwar tsohon birnin.
Mutanen garin sunce a baya ana ganinta, ana kuma hurɗa da ita, ana mata yanka da hidimomi na wasu abubuwa, yayin da ita kuma takan taimaki mutane wurin samun biyan bukatunsu na rayuwa.
Watakila itace silar zaman ɗan bakoshi a wurin yana mai mata hidima kamar yadda Barbushe yayi ga tsumburbura, amma dai zuwa yanzu akwai karancin labari game da tsoffin abubuwa da suka faru tun asali a birnin.
Haka kuma, akwai labarin wurare masu ban mamaki a garin da har yanzu ana ganin suna da tasiri. Misali, ance a baya duk bakon daya kusanci mazaunin aljanna Mararraka dake saman wancan katon dutsen (gimdin wata bishiya), to fa sai ta bishi har gida ta halaka shi. Don haka ya zamo al'adar mutanen garin hana duk wani bako kusantar wannan wuri. A cewarsu, ko a zamanin turawa akwai waɗanda suka ƙi-jin magana kuma suka mutu a sabili da kusantarsu ga wurin.
Akwai kuma wani wuri da akace kafi ne irin na gari, da aka yiwa garin domin nemar masa kariya daga dukkan sharri, ance har gobe idan mutum ya taka wajen sai shauni ya kamashi iya tsawon wani lokaci.
Sunan sarautar garin Magaji, watakila tun bayan mutuwar ɗan bakoshi ta fara, tunda a zamaninsa shine sarkin garin, watau dai kamar irin yadda ya faru ga magajin dala da magajin sontolo
Daga Sarakunan garin, wani da ake kira magaji Alu shine wanda har gobe akafi tunawa dashi, saboda kasancewarsa shine fulani na farko daya soma mulki a garin, da kuma hatsabibancin daya nuna zamanin mulkinsa.
Ance a lokacinsa akwai zama lafiya da kwanciyar hankali, kuma da kansa yake kama ɓarawo, domin daya ganshi yake gane shi. Sannan idan kaje gida kaganshi a kwance, kana zuwa gonarsa sai ka sake tarar dashi.
Zuwa yanzu dai, ganuwar garin ta rushe sai dai akwai shacinta, kuma babu ko ɓurɓushin murfin kofar da ake ɓame garin, amma tana iya yiwuwa akwai tsoffin kayan tarihi da ake ajiye dasu na mutanen da suka gabata a garin.
Garin yana nan a jihar kano, karkashin karamar hukumar shanono.

No comments:
Post a Comment