Monday, 11 December 2017

TARIHIN KAFUWAR GETSO 2

Tarihi: Cigaban Asalin Garin Getso.


Sai San-Getso Maigada ya tambayi bafillani cewa Modibbo ina za'a ne ? Sai shiƙkuma bafillace mai suna Niniya ya labarta masa abinda ya baro dashi gida.watau saɓanin da suka samu da ɗanshanono saboda haka zai tafi kudu. Sai San Getso Maigada ya aiki wakili ga ɗan shanono yana mai cewa yaya zai bar bafillatani mai arziki kamar Niniya yabar kasarsa?  Sai shikuma Ɗɗanshanono ya aiko da cewa idan shi Sangetso yana son wannan ɓafillatani to ya rikeshi.
   Sai kuwa SanGetson ya tambayi bafillatani ko yana da sha'awar zama anan? Inda shikuma Niniya ya amince da hakan. Daga nan ne aka kaishi wani tsauni wanda a yanzu ake kira 'Tsaunin fulani' aka bashi wurin don ya zauna da iyalansa da dukiyarsa kuma.
   Ance daga baya sai Niniya ya sakarwa yayansa harkokin kiwo, shikuma ya dawo fada kusa da San Getso maigada. A lokacin da Sangetson kuma  ya rasu sai ya kasance 'ya'yansa duk kananu ne basu isa sarauta ba, don haka sai akayi shawarar abaiwa Niniya sarauta tunda anga shine mafi kusanci da marigayin. Sarkin kano na wannan lokacin shine ya naɗa shi sarauta.
   Ana cikin wannan hali sai wani mutum mai suna Kalu yabada labarin zuwan Wazirin sokoto kasar zazzau. A lokacin kuwa fulani sunci kasar hausa da yaki tun jihadi, yana rangadin yawan zaga k'asa, sai kuwa wani mutum daga getso sunansa Mani ya sayi kwalli, tandu da sauran kayayyaki na tsaraba ya tafi zazzau ya gaishe da wazirin sokoto gami da bashi kyaututtukan. Sannan ya rokeshi idan zai koma gida ya sauka a getso. Ai kuwa haka akayi, domin waziri yaji daɗin wannan abu.
    Da waziri yazo getso sai ya sauka a unguwar Niniyawa. Ance saukar sa keda sai wata tsohuwa mai suna Yayambi ta ɗauko taɓarya tana dukan dawakan wazirin sokoto saboda an ɗaure su a kofar ɗakin tane. Ance sakamkon haka Wazirin sokoto yace ya cire Sangetson lokacin, ya kuma maye gurbinsa da Mani wanda yayi silar zuwan sa Getson kenan. Sai dai ance hakan baiyiwa Sarkin kano na lokacin daɗi ba.
    Ana wannan turka-turka ne Alu ya amshi sarautar kano, shine kuma ya kamo Tsigi ɗan dumare mau saukar raini yayi masa sarautar sangetso. Inda daga baya ya gudu (bamuji dalili ba), sai aka kawo mamuda aka ɗora a mulki. Mamuda na cikin wannan sarauta sai shima ya gudu, sai Sarki Alu yace a kawo ɗansa zaiyi masa sarauta, to ance sai aka kulla munafinci akace ai ya haukace, inda aka kai wani daban a maimakonsa. Amma sai sarki Alu yace bai yarda ba, shidai lalle a kawo masa ɗan mamuda, wanda ance sunansa jibrin.
   Yayin da aka ka jibrin gaban sarki sai yayi masa tambayoyi. Daga nan Sarki ALu yace shi baiga alamar hauka ba, don haka ya naɗa Jibrin San getso.
   Bayan rasuwar Jibrin, sai akayiwa Gandau. Shikuwa Gandau ance shima guduwa yayi sakamakon wani mutum mai suna Damina Magaji daya sara da adda. Daga nan sai akayiwa Sidi, Sai Salmanu, Sai San Getso mai Zabo har ta gangaro zuwa yau.
A takaice dai:-
* Sarkin Kano Abbas ya naɗa Also San Getso a shekarar 1903.
* Angina masallacin kasa a kofar fadar sangetso a shekarar 1913
* An fara daddatsa getso a shekarar 1921, inda aka fitar da Kara, karkari, koya, sabon birni, dankado da kwatama.
* An naɗa San getso Alu a 1932
* Anyi fashin garin getso a 1951
* Angina masallacin siminti a getso a 1953.
* An dawo da San getso Salmanu daga sabon birni a 1964.
     

2 comments:

  1. Ni danmalikin Getso AUWALU ABDULLAHI
    Nayi farinciki da Samun Wannan tarhin

    ReplyDelete
  2. Ni saifullahi yusuf salis k/fada getso nayi matuqar jindadin wannan tarishi Allah yaqarawa garinmu Albarkha amin

    ReplyDelete