Monday, 11 December 2017

TARIHIN HAUSA DA BAYANI KAN KATSINA 2



Tarihin Hausa Da Bayanin Katsina
   (Mahanga ta farko, kashi na biyu)


Dr. Heinrich Barth yaci gaba da cewa
Bayanin da Sultan Bello ya fada cewa Hausawa asalinsu bayin Borno ne, babu sahihiyar hujja ko inganci a ciki. Tunda a yaren hausa, kalmomi kadan ne suka zo d'aya da yaren kanuri na mutan borno. Sannan karin magana, wakoki da sauran zantukan adabi duk sunsha bam-bam da juna.
   Sai dai, zancen na Sultan Bello na iya zamowa gaskiya ta wani fannin idan muka kalli yawan al'ummar garin kano, da yadda garin ke kunshe da ababen borno da dama, watakila wasu na iya cewa lokaci ne ya sauyawa al'ummar kano harshe daga kanuri izuwa hausa.
   Kalmar 'Bawo', wadda ta fito a matsayin sunan uban jihohin hausawa na iya zamowa alamar kasancewar yankin acikin bauta. Ainihin Sunan Bawa da harshen hausa shine 'Mowa', amma daga baya sai ya koma 'Bawa' daga 'Bawu'.
   Shikuwa Bawu, ance mutum ne sunan ubansa Karbagari.  Sunan dake nufin 'kwace-gari' da yaren hausa. Sunan na iya zamowa ne daga 'kwace garin biram' (watau uban Bawo shine wanda yayi jagorancin kwace Birnin Biram). Garin Biram kuwa a nan ne akace tsohuwar daular hausa ta asali ta kafu. Kuma ana kiran sane da suna 'Biram ta gabas' domin banbance shi da wasu garuruwan kudanci masu suna 'Biram'. Sannam an tabbatar da cewa garin ya wanzu ne a tsakanin Inda garuruwan kano  dana Hadeja suke a halin yanzu.
 Bawo shine akace sarkin garin Biram, wanda kuma ya haifi manyan jihohin hausa guda shidda, watau:
 *Katsina da Zeg-Zeg (tagwaye)
 * kanu da Rano
 * Gobir da Daura
   Amma ance Daura ne babban da acikin su.
Abu mafi inganci ma wanda zai iya tabbatar da wannan abu na sama shine ambatar sunan 'Diggera' a matsayin mahaifiya ga wadannan 'ya'yaye na Bawo. Ita kuwa ance ta fito ne daga kabilar Berber ne, wadda ta wanzu a garin Muniyo,, wadda kuma ta taba zamowa kakkarfa a baya.
   Biram, Daura, Gobir, kano, Rano, katsina, da zeg-zeg sune hausa bakwai, sune kuma asalin garuruwan hausawa.
   Banza bakwai kuwa na nufin garuruwa bakwai da hausa ya warwatsu garesu, kuma sune:
   Zamfara, kebbi, Nupe ko Nytfi, Gwari, yawuri, yoriba ko yariba da kwararrafa.
Wadan can 'ya'ya shidda na bawo, sai ubansu ya danka musu mukami a masatautar sa.
  * Gobir shi aka nada sarkin yaki
  * Kano da Rano aka nada sarakunan Baba (marina)
  * katsina da Daura aka nada sarakunan kasuwa
  * shi kuwa zeg-zeg, an nadashi ne mai samarwa 'yan uwansa kayayyakin bukata a wuraren da suke zaune, kamar misalin bayi da makamai.

  Rano, garin da a yanzu ya ragu sosai, ya kasance babban gari a baya, kamar misalin sauran garuruwan duk kuwa da cewa babu wani marubuci daya taba ambatar sunan sa, garin yana nan a kudu maso yammacin garin kano.
   Idan zamu aminta da yadda Leo Africanus ya bayyana kasar hausa a lokacin daya ziyarce ta, zamu gane cewa garin katsina bai kafu a inda yake yanzu ba a wancan kokacin, domin ya bayyana yankin da 'yanki mai kunshe da tsirrai' kamar yadda ya rubuta yana bayyana wurin da cewa "piccoli casali fatti a guisa di capannie'.
    Sannan wani abin tunawar shine wanzuwar wani mutum mai suna Muhammad Al Baghadadi (Wanda hausawa ke kira Bayajidda) a garin Daura. Wannan ne yasa ni hasashen akwai alaka tsakanin wannan mutumi da wasu masallatai (wuraren bauta) dana gani akan hanyata daga Tintellust zuwa Agadez, domin anyiwa wuraren lakabi da 'sidi-sidi Baghdadi'.
  A tarihi, muna iya cewa Sarkin katsina Ibrahim Maji (musulmi na farko a sarakunam katsina) ya wanzu ne a tsakiyar karni na goma bayan hijira.
 A yanzu kuwa idan mukayi lissafi daga wancan lokaci, muka kara shekarun mulkin sarakunan katsina da suka gabace shi, har muka tik'e izuwa kan Kumayo, wanda duniya ta gamsu cewa shine ya kafa garin katsina, lissafin zai bamu akalla shekaru 350. Abinda zai kaimu ga tsakiyar karni na bakwai kenan bayan hijra.
   Don haka sam bana goyon bayan wofantar da sunayen sarakunan katsina da wasu sukayi, domin ba kawai sun shiga zuciyar mutane bane, an same su ma a rubuce.
  Watakila muna iya cewa da gan-gan fulani suka suka lalata littafin dake kunshe da sunayen sarakunan katsina a lokacin jihadin fulani da suka kwace garin domin sauya tarihin kasar ta katsina.
    Abinda muka samu shine, kumayo ne ya kafa garin katsina. Sai kuma sarakuna masu suna Ramba, Taryau, Jatinnata da Sanawu suka biyo bayansa a mulki (tsawon mulkin su gaba daya ne shekaru 350). Ance sanawu yayi tsawon shekaru talatin akan mulkin katsina, sannan akace korawa ne suka kasheshi, wasu al'umma kenan da suka zo daga 'yantandu suka kafa daular su a katsina. Sune suka danka jagorancin katsina a hannun Sarki Ibrahim maji. Watakila hakan ya auku ne a wajajen shekara ta 950 bayan hijira.
   Sannan an samu cewa, shekaru talatin kafin zuwan Ibrahim Maji a mulki, (wuraren shekarar 1513 miladiyyaa, 919 hijiriyya) Sarkin Songhay Alhaji Muhammadu Askia ya kwace garuruwan Hausa gaba daya.
   Kamar yadda wasu suka ruwaito, sunce lokacin katsina na karkashin ikon kano ne, kuma lokaci kalilan sukayi a karkashin daular ta Songhay, lokacin kuma sarkin kebbi ya karfafa, shine kuma yayi turjiya ga sarki Askia.
  Sai dai babu tabbaci a game da wadannan shekaru saboda sassauyawar su a bakunan maruwaita tarihi.
   Karshen wannan mahangar tarihi kenan.

No comments:

Post a Comment