Monday, 11 December 2017

SIRRIKAN KASUWANCI

Tsakure daga Littafin 'Ilimin kasuwanci da sirrikan neman arziki' na Sadiq Tukur Gwarzo.

Idan muka koma fagen sarrafa dukiya kuwa, zamuga a ha}i}a ilimi ne mai zaman kansa kamar yadda muka fa]a wanda yake bu}atar tsawon lokaci kafin  a samu }warewa a kansa kuma.
Da yake a wannan zamanin namu, ‘yan kasuwa akafi ]auka a matsayin attajirai, sune kuma aka gamsu akan cewa sunfi kowa ilimin zamowa attajirai, ga ka]an daga sirrikan da Attajiran duniya suka fa]i don samun arziki;

Warren Buffet yace ‘Asara a kasuwanci na zuwa ne a lokacin da ka kasa sanin abin da kakeyi”.
Aristottle Onassi yace “sirrin kasuwanci shine kasan wani abu wanda babu wani masanin irinsa”.
Bill Gate yace “idan kana son koyon kasuwanci, sai kayi nazari akan kwastomanka wanda ba’a iya gamsar dashi”.
William Hazlit yace “Duk wanda baya son kasuwancin sa, shima kasuwancin nasa baya }aunar sa”.
Harold Geneen yace “A kasuwanci, kowanne mutum ana biyansa ne da abu biyu; ku]i da kuma ilimi. Amma idan kayi aiki da ilimin, da sannu ku]in zasu biyo baya”.
Swett Marden yace “Dokar kasuwanci itace: ka zamo }ar}ashin }afar kwastomanka”.
Warren Buffet yace “Dokar kasuwanci ta farko itace kar kasa ku]in ka inda zakayi asara. Doka ta biyu itace kada ka mance da doka ta farko”.
Edwin Lefevre yace “ka samar da kyakkyawar ala}a da abokan hur]arka”.
Alfred A. Montapert yace “kasuwancin da yafi }arko shine wanda aka ginashi bisa abokantaka”.
Oprah winfrey tace “ina jin a raina cewa sa’a ba komi take nufi ba illa shiryawa amfani da damar-maki”.
Steve Jobs yace “A wani lokacin kana iya }ir}iro tunanikan kasuwanci, bayan ka aiwatar dasu kuma sai ka samu matsala. Abinda yafi shine kayi saurin gyara matsalolin da suka auku, sannan ka }ara samo wasu tunanikan”.
David RockerFeller yace “Nasara a cikin kasuwanci na bu}atar darasi, gami da aiki tu}uru”.
Cohn Powell yace “Babu wani tsayayyen sirri ga samun Nasara. Ita kawai ana samun tane ta silar tsarawa, aiki tu}uru gami da koyon ilimi daga fa]uwa”.
Sam Walton yace “shugaba ]aya ne tal a kasuwanci, shine kwastoma. Zai iya korar kowa a kamfani tun daga kan manaja har zuwa lebura cikin sau}i ta hanyar daina siyan hajar ka”.
Henry Ford yace “Mutumin da zakafi jin tsoro acikin masu gogayyar kasuwanci dakai shine wanda bai damu da abin da kakeyi ba, kuma a kullum yana maida hankalinsa ne don kyautata kasuwancin sa fiye da koda yaushe”.
Walt Disney yace “Bai kamata mutum ya wofantar da iyalinsa akan kasuwancin sa ba”.
Shima wani marubuci Jeremy Kourdi acikin littafinsa mai suna “100 GREAT BUSINESS IDEAS FROM LEADING COMPANIES AROUND THE WORLD” ya kawo sirrikan kasuwanci kwarara har guda ]ari gami da yin bayani akansu, ga ka]an daga cikin muhimman sirrinkan.
Ka samu yarda da amincewa daga abokan hur]ar kasuwancinka.
Ka samarwa ma’aikatan ka }arfin guiwa ta yadda zasu samu damar yi maka aiki cikin karsashi da jin]a]i
Ka rin}a la’akari da abubuwan da kwastomominka ke so, yi }o}arin janyo kwastomominka a jiki gami da kyautata musu fiye da }o}arin samo wasunsu.
Kada kayi tsammanin cin nasara a kasuwancin ka da zarar ka fara, yi amfani da nasarar da ka samu ko fa]uwa gamida bayanai daga kwastomominka don ha~aka samun riba a gaba.

Maimakon kayi sako-sako har wasu kamfanoni ko ‘yan kasuwa su ci maka dudduge a kasuwanci, zai fi kyau ka rin}a sanya hannun jari a cikin wasu kasuwancin na daban, ta yadda idan ka fa]i anan, zaka ci nasara acan.
Ka samarwa da kasuwancin ka wata daraja (misalin gaskiya, }arko, }wari, juriya, al}awari) wanda zai sha bam-bam da sauran masu gogayya da kai.
Ka samu kyakkyawan ha]in guiwar kasuwanci da ‘yan kasuwa, ka kuma ri}e amana don ]orewar ha]n guiwar.
Ka samar da lokacin zantawa da ma’aikatan ka gami da kafar }arawa juna sani.
Kayi }o}arin maishe da ribar kasuwancinka uwa wadda zata janyo maka wata ribar, wannan ne alamar motsawar kasuwancin ka.
Ka tallata hajarka cikin raha da nisha]i ta hanyar amfani da kalmomi da]a]a masu nuna daraja ga kwastomomi.
Ka canza tsarin kasuwancinka a duk sanda bu}atar hakan ta taso domin yin dai-dai da halin da kake ciki tare da }ara janyo riba.
Sai kuma wa]ansu sirrikan kasuwanci wa]anda suka fito daga }asidar ‘Insurance Journal Magazine’ mai fitowa mako-mako a birnin Newyork ]in Amurka, ga ka]an daga ciki.
Ka san wanene kwastomanka, wato wanda yake jiran ka fitar da kayan ka kasuwa ya siya.
Ka san kasuwar da kwastomanka yake, ka samu tattaunawa dashi don jin fahimtarsa da ra’ayinsa game da abinda kake siyarwa.
Idan matsala ta samu kasuwanci, ba’a ]orata a kan mutum ]aya. Maimakon haka, kamata yayi kowa a masana’anta yaji yana da laifi akan haka.

Ka lura da bu}atar kwastomomin ka fiye da yadda kake lura da bu}atar kanka.

Kayi godiya ga duk wani aiki ko yun}uri da wani, wata ko wasu sukayi don su kyautata maka.

A koda yaushe ka rin}a auna ribar da kake samu a yanzu da a lokacin da ya wuce kayi kuma }o}arin fahimtar dalilin raguwar ribar, }aruwarta ko rashin canjawarta.

Ka samu wani fanni da kasuwancinka zai zamo na daban dana saura.
Kayi hayar }wararru da masana don jin shawarwari kafin ka samu gogewa.
Kada ka manta, ka rin}a tambayar kwastomominka da ma’aikatanka “shin akwai wata matsala ne?” don jin abinda bai gamsar dasu ba.
Ka nemi taimakon ]aukacin abokan hur]ar kasuwancin ka ta hanyar basu daraja har suji cewa abinda ya shafeka ya shafe su. Kayi sani ba zaka iya yin aikin kai ]aya ba.
{ari akan wa]annan, sune wasu sirrika da }asida mai suna “American City Business Journal’ tayi bajakolinsu da taken “Dabarun kasuwanci guda 101”.
Ka tsara kasuwancinka da tsari kyakkyawa.
Ka nemi ha]in kan iyalanka da makusantanka a kasuwancinka, lallai ya kamata susan abinda kakeyi.
Ka fahimci masu bu}atar abinda kake samarwa a kasuwanci na ha}i}a domin babu bu}atar tallata kasuwanci ga wanda bashi da bu}atar abin.
Ka fahimci kasuwar da zaka ha]u da wa]ancan mabu}atan, da yadda talla zata gamsar dasu.
{warin guiwar ka da karsashin ka zai }arawa kasuwancin ka daraja ne.
Ka rin}a }o}arin }ir}irar wani salo sabo a kasuwancinka duk sati, wata, ko shekara.
Ka shirya ha]uwa da abokan hur]arka jefi-jefi don jin ra’ayinsu da tattaunawa akan abinda suke so.

Ka sanya ha}uri, kasuwanci baya yin fice a lokaci }an}ane.
Ka rubuta bayani a duk wata ga~ar kasuwancinka mai bada ba’asin nasarori da asarar da aka samu.
Kayi aiki tu}uru akan wannan bayani don samar da gyara a kasuwancin ka.
Daga wa]annan kuma sai wasu sirrika masu kyau da wani marubuci kuma ]an kasuwa ‘Andrew Khen White’ ya rubuta, aka ya]a a }asidar ‘Arabian Business Magazine’ da taken ‘sales management, ga ka]an daga ciki:
Kada kayi hanzarin zurara ma}udan ku]in ka a kasuwanci cikin }aramin lokaci.
A cewar sa ‘kamfanoni basa saurin zuba zunzurutun miliyoyin ku]a]e farat ]aya a kasuwa, abinda suke yi shine:
Zuba ku]i ka]an-da-ka]an a kasuwa tare da auna nasara.
Ka zamo mai halin dattako, da yawan mutane zasu rin}a tuna kirkin ka, don haka zasu mayancewa yin mu’amala da kai.
Ka maida kanka mai sau}in samu ( ta waya ko ta fili) maimakon mai wahalar riska.
Ka rin}a hasashen mai zaije ya dawo a kasuwancinka.
Ya kamata ka rin}a tuntu~ar kwastomominka.
Kayi }o}arin samun gamsassun bayanai game da kwastomominka. Aiki da wa]annan bayanan zai baka damar ri}e wuyan abokan hur]a.
Idan kana son samun farin ciki a kullum, yi }o}arin farantawa na kusa dakai.
Kada ka yanke shawarar kasuwanci yayin da kake cikin ~acin rai.
Kayi }o}arin fahimtar halin da kake ciki a kowanne zangon kasuwanci (Asara ko Riba).
Kayi }o}arin }ara samun kwastoma a}alla mutum (4) duk mako ko fiye da haka.                                    **                                    **                                  **
Abu mafi kyau da attajirai sukafi ri}ewa da muhimmanci shine: suna maida hankulansu ne don fa]a]a harkokin dake kawo ku]i fiye da wa]anda ke janye ku]i daga aljihunsu.
Saboda haka aduk ga~ar kasuwanci ]an kasuwa zaiyi tunanin inda yafi samun riba mai daraja da kuma dalilin samun wannan ribar don haka sai tunanin kansa su wanzu binciko masa hanyar da zai inganta wannan guri gami da }ir}irar wani gurin kamarsa.
Kafin wani lokaci mai tsayi idan ya tafi ]o]ar akan haka, kana iya ganin cewa ribar dake shigo masa ke ]aukar duk wata ]awainiyar rayuwarsa data iyalansa ragowar kuma na }ara ha~aka, suna ta ru~anya.
Wani abu mai kama da Arashi kuma wanda jama’a basu fahimta ba shine. Attajiran dake ta}ama da darajar ku]i, basa wasa da dukiya, sun san }imar ku]i fiye da kowa a duniya. Don haka basa kashe ku]a]ensu a wajen shirme da shiririta, kamar misalin siyen wani abu wanda a zahiri basu da bu}atar sa.
Idan suka tashi siyan abin hawa misalin mota, basa fitar da ma}udan ku]a]e don mallakar motar da zasu burge mutane domin ba burga ce a gabansu ba, suna neman wadda ta kamace sune, watau irin wadda zatayi musu aiki gwargwadon bu}atar da suke da ita.
Da haka ne zaka same su masu matu}ar taka-tsan-tsan da ku]i, a kullum han}oron su shine idan har ku]i kaza suka fita daga aljihun hagu, ta wacce hanya wasu ku]a]en zasu maye gurbin su (ko }ari ma) a aljihun dama.

No comments:

Post a Comment