RA'AYI: Siyar da Kadarorin Kasar nan bazai zamo alheri ba.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
A wannan makon daya wuce ne wasu 'yan uwa 'yan Nigeria suka bada shawarar siyar da manyan kadarorin gwamnati masu kawowa k'asar arziki, a ganinsu hakan ne mafita ga matsalar tattalin arzikin da k'asar ta tsinci kanta aciki.
A kan haka, Gwamnan babban banki Mr Godwin Amefiele ya shaidawa 'yan jaridu cewar siyar da kadarorin zai samar wa da k'asar dala biliyan goma ne kachal saboda karyewar darajar naira. Ita kuwa hukumar tara haraji cewa tayi a iya shekaru takwas, kamfanin Nigerian Liquefied Natural Gas (NLNG) wanda daya ne daga kamfanonin da akeson siyarwa, ya zubawa kasar kudi har kimanin dala biliyan shabiyu da d'oriya duk kuwa da rashawa da tayiwa harkar katutu.
Asge kenan muna iya cewa ' ba cinya ba k'afar baya', yin hakan wani sharri ne da zai k'ara tsaurara zafin rayuwa ga talakawa masu rinjaye a k'asar, duk kuwa da zai farantawa tsirarun attajiran da zasu siye kadarorin zuciya.
Attajiri na d'aya a fadin Afirka, Alhaji Aliko Dangote ne ya fara bada wannan shawarar a firar sa da gidan talbijin na CNBC. Sai dai idan mukayi duba na tsanaki, muna iya cewa shawarar durkusar da k'asa Dangoten ya bayar ba-ta tayar da komad'ar tattalin arziki ba.
Dalili shine, tarin kadarorin Dangote masu darajar dala biliyan ashirin da daya ne suka bashi damar zamowa babban attajiri na d'aya a afirka, ba tarin kudi ba. Sannan da kansa ya bayyana cewar yayi asarar kudi har dala biliyan hudu saboda wannan k'angi da kasar take ciki. Abin tambayar shine, me yasa bai fara tunanin siyar da kamfanin sa na Obajana ba don farfado da asarar da yayi? Ai wanda rashin lafiya ya kama magani yake nema ba guba yake sha ya mutu ba. Amma da yake attajiri Dangote yasan ciwon kadarori, maimakon ya siyar da wata kadarar, a yanzu haka wasu yake shiri. Tunda ya fadi cewar yana kan kudurin kafa wasu kamfanoni wadanda darajar su Takai ta dala biliyan ashirin, ga kuma kamfanin Arsenal da yake hankoron siya nan da shekaru hudu masu zuwa.
Magana ta gaskiya itace, wajibine mu yabawa sanata Ekweremadu, tunda ya fadi illar abin ga 'yan kasa da masu tasowa. Duk uba nagari, yama son yabar wa 'ya'yansa kadarorin da zasu ci moriyarsuvbayan ransa. Me zaisa a tunkuda uwar mu Nigeria tavsiya da nata kadarorin?
Haka ma Sanata Akume, Shehu Sani da Majalisar koli a kan tattalin arziki duk sun cancanci yabo, domin sunyi fatali da shawarar, tunda sun san babu alheri acikin ta.
A ra'ayin mu, indai da gaske attajiran 'yan kasuwa da 'yan siyasa nason kawo karshen wannan matsala, kamata yayi su fara sadaukar da rabin dukiyoyin su ga wannan kasa tamu mai albarka. Hakan na iya zuwa a matsayin kyauta ko bashi. Kenan maimakon su bada shawarar kuntatawa talakawa, sun bada dukiyar su don tallafa musu. Wannan kuwa zai janyo musu soyayya daga 'yan kasa, kuma abune da zai kara samar da zumunci gami da zama lafiya a kasa.
A karshe, muna kira da gwamnati ta kara azama don kawo karshen wannan matsala. Gwamnati ta tunbuke duk wani mai kawo nakasu ga tattalin arziki, ta kuma bi diddigin maganar da shugaban hukumar FIRS ya fada na cewa akwai kamfanoni dubu dari bakwai da basu taba biyan haraji ba. Kuma Koda an ciwo bashi a wannan lokaci ba matsala bane, domin lalurar data fad'o mana ba mai dawwama bace, nan da 'yan lokaci zata zama tarihi da yardar Allah.
Dafatan Allah ya warware matsalolin wannan k'asa tamu. Amin

No comments:
Post a Comment