LABARIN BAWA DORUGU, BAHAUSHEN DAYA FARA
ZAGAYA TURAI
Kashi na shida.
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Dorugu yaci gaba da cewa " Da muka tashi daga Konu,
sai muka zagaya hanyarmu ta fari wadda take kaimu ga
kukawa, muka shiga gidanmu, amma gidanmu ba kusa
bane gana Sarki. Da muka zauna, da dare sai tsohon
ubangijina yazo zai tafi dani, amma Tebib ya hana.
Washe gari Tebib ya dinka min sabon riga da alkamura,
ya fadawa Ibrahim cewa zai kaini gidan tsohon
ubangijina da kansa.
Ibrahim ya wuce gaba, Tebib na binsa a baya bisa doki,
nikuma ina biye dasu abaya har gidan. Ibrahim ya shiga
ya kirawo shi, sukayi magana da yarensu, ina
tsammanin Tebib ya bashi kudi, amma ni nashiga cikin
gida, matar ubangijina ta tareni da murna.
Daga can kuma sai tsohon ubangidana ya kirawo ni,
yace na bashi rigana da wukar daya taba siyamin, yace
nabi Tebib. Daganan na koma hannun Tebib a matsayin
bawa.
Na zauna kwanaki kadan agidan Tebib, sai ya saisheni
ga wani mutum arab, nashiga hannun sabon ubangiji.
Ina tsammanin sunan sa Bohal, ya zauna a wajen arab
ne, ko yaushe yana fita yawo dani, ina son wannan
sabon ubangijina, don yana yin dariya. Yana son
mutane dayawa acikin kukawa, da yawa kuma sun
sanshi, kuma suna sonsa.
Kwanaki kadan ina hannun Bohal, sai naga ibrahim ya
zago ga gidan. Ya ganni na gaisheshi, ya tambayeni
idan inason komawa gidan Tebib, nace inaso. Yace mini
Tebib nason ya siyeni. Sai ya tambayi Bohal idan zai
siyar dani, kuma kudi nawa? Ina tsammanin Bohal ce
masa yayi da azurfa zai siyar dani, Ibrahim ya tafi ya
fadi haka ga Tebib.
Ba'a dade ba sai Ibrahimu ya dawo garemu da kudi
kunshe cikin zane, ya zube a kasa, suka kidaya. Da
suka gani yayi dai-dai, ibrahimu ya kirani muka fita
waje muka tafi muna yin zance. Yace mini "yanzu kai
ba bawa bane". Amma ban yadda ba, har dai muka isa
gidan Tebib. Dana ganshi saina gaisheshi, daman yana
jin hausa kadan-kadan.
Suka kirawo wani malami sunan sa Madiyar Mami, ya
rubuta mini laya, yace kubaiwa Tebib ya rike masa har
ya girma. Sannan yace mini yanzu Da kake ba bawa ba.
Na godewa Tebib, nayi murna kwarai dana shiga
hannunsa. In dare yayi yakan shimfida mini tabarma
daga dakinsa, nakanyi kwanciyata anan. Shikuma
yahau bisa gadonsa, da safe na tashi na wanke
fuskata. Wani baran Tebib ya koya min yadda ake
gahawa, nakanyi gahawar, sannan na wanke abinda
Tebib keshan gahawar dashi.
Wata rana kuma, nakan daura masa sirdi, nakan tafi
tare dashi izuwa gidan wani galadima, sunansa Alhaji
Bashir, shine babban bafaden Sarki. Daga nan kuma
muna zagayawa gidan wani bokinsa alhaji, sai kuma
mu koma ga gida. Amma fa duk inda ya shiga, nike
tsayawa a waje na rike dokinsa har ya fito ya isheni.
Wani lokacin muna tafiya ne da wani abokinsa Bature
mai suna Abdulkarim gidan sarki.
Tunda na zauna ga Tebib, kowace safiya da marece,
yana tafiya shan iska, yana daukar bindigarsa ya rataya
a wuyansa, mutafi harbi. Yana kuwa da idon harbi
kwarrai. Idan yaga tsuntsaye ko barewa yana kashewa,
nikuwa sai nayi jiransa ina rike da dokinsa, sai rana ta
kusa faduwa muke dawowa gida.
Rannan muntafi harbi wani gari kusa da chadi, muka
tafi tare da baransa ibrahim da wani abokinsa Kalumba.
Tebib da abokinsa Suka harbi tsuntsaye daga ruwan
chadi. Da muka kare farauta muka bar kalumba agarin
muka dawo birnin kukawa. Da akayi ruwa muka koma
chadi, daga can muka gamu da kalumba, muka samu
kifaye sun fito waje don anyi ruwa da yawa, muka
kama da yawa muka dora bisa bayan doki. Idan abokin
Tebib ya soki kifi shikance ga Tebib "nochira nochini?".
Tebib kuma shikance "nochi". Ma'anarsa shine "kasan
sukan kifi ko baka sani ba?" Shine tebin yake cewa
"nasani". Da muka gama sai muka koma ga kukawa.
Bayan watanni kadan, sai mukayi shiri zuwa ga
Goshiba. Muka labtawa rakumi daya kaya, mukatafi da
Tebib da Ibrahim da wani mutum wanda sarki ya turo
ya wuce mana gaba don ya kaimu ga goshiba. Muka
sauka a wani gari mai duwatsu masu tsawo da dabino
na mance sunansa, muka kwana agarin, da safe muka
hau kan wani dutse, sai aka aiko wani mutum ya
kiramu domin sun ganomu akan dutsen.
Da muka shiga, sai muka taradda mutanen garin sunyi
fushi don babu wanda ke hawan dutsen nan. Ina
tsammanin mutanen Mandara ne. Bamu dade a garin
ba kuwa muka tafi, don Sarkinsu bashida lafiya. Daga
nan muka isa Goshiba, muka danyi fatauci, sannan
muka dawo kukawa.
Rannan Tebib ya kirawo baransa don ya daura masa
sirdi. Abega, daya daga cikin barorinsa ya dauki
bindigarsa, suka fita wajen gari, suka iske wani tafki,
wurin bashi da nisa ga kukawa, masu fatauci na sauka
a wurin su aika a nemo musu mazauni kafin shiga gari.
Daga nan Tebib ya karbi bindigarsa a hannun Abega, ya
gano tsuntsuwa fara, ya tafi ya harbeta amma ta tashi,
yayi gudu don ya kamata bai same taba, sai ya kara
binta, shine fa tabo ya rike takalminsa, amma bai kama
tsuntsuwa ba. Ya fita daga tabo babu takalmi,ina
tsammanin Abega ne ya fita ya kwaso takalmin ya
wanke, ya bashi yasa, don duk abinda akayi bana wurin,
saida Abega yazo ya bani labari.
Da dare yayi sai kafar tebib ta fara ciwo, muka zauna
kwanaki kadan ciwo yayi masa karfi. Yace mana zaifi
kyau mutafi ga garin abokinsa mai suna Kalumbo, kusa
da ruwan chadi. Yana tunanin idan yaje zai samu
rangwame. Da safiya tayi muka tafi, ya tsaya a ruwan
chadi yayi wanka, amma a daren wannan rana bai
kwana ba.
Da safiya tayi mukayi masa kuka nida Abega, aka aika
wani mutum zuwa kukawa don ya fadowa Abdulkarim.
Abdulkarim ya yayo sukuwa bisa doki zuwa garemu, ya
sauka hawaye na zubar masa. Sannan bayan jimawa
kadan yace da Abega dani kada muyi kuka. Abdulkarim
ya da daya abokin Tebib suka wanke gawar tebib, suka
sashi cikin alkamura, muka haka kushewa karkashin
wata babbar itaciya, sannan suka sanya shi cikinta, aka
shimfida kilishi da wadansu abubuwa da yawa sannan
aka maida kasa aka binne.
Da muka kare, sai muka dawo kukawa. Sai dai Ibrahim
shine babban Baran Tebib, bayan mutuwarsa sai ya
dauke mukullan sa, ya dauki kudi daga kayansa, amma
Abdulkarim bai sani ba. Daga baya Abdulkarim ya nemi
kudin Tebib bai gansu ba, sai ya kirawo Ibrahim yace
masa kai ka dauki kudi? Yace bashi ya dauka ba.
Abdulkarim yace masa idan baka kawo kudin nan ba
zan kaika ga sarkin Borno, sai dai ya samu wasu kudi,
amma ban tsammanin duka. Mudai muka koma hannun
Abdulkarim, ya kuma rikemu kamar Tebib.
TAFIYA TIMBUKTU
Sai naji Abdulkarim nason zuwa Timbuktu, garin dana
jima banji labarin saba. Sarkin Borno yayi masa guzuri,
ya bashi rakuma, ya kuma aiko masa da masani ko ace
jagaba. Abdulkarim yace idan mun tafi kasar hausa,
idan mun hadu da ubana zai bayar dani gareshi...
(Tebib fa ba kowa bane sai Adolf Overweg masanin
taurari dan kasar jamus. Ya rasu ne a shekarar 1852, a
inda Dorugu ya labarta mana. Har yanzu kuma turawa
basu tabbatar da sunan cutar datayi sanadiyyar
rasuwar saba. Shikuwa Abdulkarim, bakowa bane sai Dr
Heinrich Barth shima ya fito ne daga jamus. Shine
kuma wanda ya dauki dorugu da abega zuwa ingila da
Jamus. Dukkansu sun canza suna ne domin samun
hadin kan al'ummar Afirka da suka shigo cikinsu).

No comments:
Post a Comment