Sunday, 10 December 2017

TARIHIN ASALIN BAKIN MUTUM 2

Tarihi: Asalin bak'in mutum da mazaunin sa
     Kashi na biyu

Daga Sadiq Tukur Gwarzo

FANTSAMAR BAKIN MUTUM IZUWA SASSAN DUNIYA

Masanin ilimin akiyoloji Manfred Bietak yayi wani zuzzurfan bincike akan tsohuwar girka da kuma alak'ar ta da tsohuwar egypt. A binciken nasa, ya samu cewa tun a shekara ta 7000 kafin zuwan Annabi Isa A.S. wadansu mutane da suka tashi daga egypt suka riski kasar Girka, a cikin su kuwa harda bak'ak'ken fata.
   Masani Manfred Bietak yayi kokarin gabatar da tsoffin kere-kere na mutanen girka na farko, kamar misalin mutum-mutumi da tukwane don kafa hujja abisa haka.
   A ranar 3 ga watan maris na shekarar 2000 miladiyya ne masanin tarihi Runoko Rashidi ya gabatar da wata lakca mai jan hankali a Honolulun jihar Hawaii na Amurka mai taken 'Bakar fata a tsohuwa da sabuwar Indiya'. A ciki ne yake cewa " fuskar Indiya ta sauya ne a wuraren shekara ta 2000 kafin zuwan Annabi Isa A.S lokacin da wasu kabilun makiyaya da ake kira Aryan (Indo-Europeans) suka isa yankin tekun Indis da sauran yankunan 'Fertile' dake kudancin kasar ta indiya."
  Sai ya kara da cewa " amma kafin zuwan su, bak'ak'en fata sun riga sun isa yankin harma sun kafa biranen su".
   Marubuci Wayne Chandler ya kara haske tare da tabbatar da hakan a littafin sa daya rubuta mai suna 'African Presence in early Asia' bayan zuzzurfan binciken daya gabatar.
   Shine ma ya rubuta cewa "tsoffin birane masu suna 'Harappa' da 'Mohenjo-dare' ne manyan biranen da bak'ar fata Suka kafa tun a wancan lokaci. Wadannan birane sun mamaye yankin da arewacin India da Pakistan suke a yanzu.
    Kabilar Olmak (olmecs) sune tarihi ya zayyana a matsayin wadanda suka fara riskar yankin Mexico.
    Wasu masu bincike irinsu Ivan Van Sertima, Rashidi da Alexander Van Wuthanau sun gabatar da hujjoji masu nuni da cewar wadancan mutanen bak'ak'en fata ne da suka taso daga afirka.
   Daga hujjojin su, sunce akwai kamance-ceniya tsakanin mutanen na olmaks da kuma bak'ak'en fata mazauna yankin 'mende' dake yankin afirka.
   Sannan kuma sun k'ara da gabatar da wasu k'ok'on kawunan mutane da suka hak'o, wadanda aka sassaka da dutse tun lokaci mai tsawo daya wuce masu nuni da siffar mutanen a matsayin bakaken fata ne.
   Haka kuma sun kara nuni da da'irorin pyramid da aka samu mutanen sun giggina da turbaya. Kwatankwacin wadanda aka taras a tsohon yankin Merwa na bakaken fata.
   A wata muk'ala da aka wallafa a shekarar 2009 miladiyya mai taken 'Light worlds from the Dark continent; a collection of essays' wadda Nibs Ra da Manu Amun suka rubuta, an samu cewa tsohuwar gwamnatin mulki da tarihi ya fara ruwaitowa a kasar china, ta kafu ne bisa shugabancin Sarki Shang (Ko zuriyar sarki shang) a wuraren shekara ta 1500 zuwa shekara ta 1000 kafin zuwan Annabi Isa A.S.
   Muk'alar ta ruwaito cewar ana kiran 'Shang' da lak'abin 'Nakhi'. Kalmar 'Na' kuwa na nufin 'bak'i', yayin da kalmar 'Khi' ke nufin 'mutum' duk a harshen tsohon yaren kasar ta sin. (Nakhi na nufin bakin mutum kenan)
   A daular Mesopotamia ma kusan haka abin yake, domin kuwa Masani Henry Rawlinson (1810-1895) ya fada cewar ana yiwa wadanda suka kafa daular da lakabin 'sag-gig-ga', ma'ana 'masu bakaken kawuna'.
    John Baldwin shima mai bincike ne kuma marubuci, ya gaskata magabar Rowlinson a littafinsa mai suna 'Pre-Historic Nations' wanda aka wallafa a shekarar 1869. Ga abinda ya rubuta a shafi na 192 na littafin " Mutanen da suka fara riskar Babylonia d'aya suke da mazauna gabashin tekun Nilu (inda akace garin bakaken fata ya fara kafuwa).
   Haka kuma, Marubuci Chandra Chakaberty ya kara haske akan haka a shafi na 33 na littafinsa mai suna ' study in Hindu social polity' inda yace "..dogaro da mutum-mutumai da aka samu an sassaka a tsohuwar daular babylonia, muna iya cewa mazauna gurin asalin su bakaken fata ne, gajeru, masu zagayayyar fuska da yankakken hanci..".
  (A duba 'From Babylon to Timbuktu na Rudulph R. Windson don karin bayani)
 Sai dai kuma, menene gaskiyar labari akan asalin inda bak'ar fata suka fara zama tare da tarihin rarrabuwar k'abilun su?

No comments:

Post a Comment