RUBUTUN BOKO NA FARKO
Sai dai, abu ne mai matukar wuya a gane wanda yafara rubuta hausa da haruffan romawa (Rubutun Boko) kasancewar bauta da kasuwanci sun sanya hausawa shiga kasashen larabawa lokaci mai tsawo daya gabata, daga can kuma an tsallaka da wasu izuwa yankunan turai da sauran sassan duniya masu nisan gaske duk da zimmar yin bauta.
Kowa yasan anyi zamunna na cinikin bayi a baya, sannan shaharar masautar Borno ba karamar aba bace. Itace akace sarakunan ta sun shahara, har ma akace a wajajen karni na goma sha ɗaya suka fara hurɗa da larabawa, sannan kuma idan yakinsu ya motsa, mamaya suke kawowa dukkanin makwabtan kasashe, ciki kuwa harda kasar hausa. Ance tun zamani mai tsawo da suka gabata akwai hausawa masu yin bauta a Turabulus da makwabtan kasashe, waɗanda ake kyautata zaton daga borno aka kwashesu izuwa can. Tana iya kasancewa wani daga turawa ko girkawa ya taba jarraba amsar labaru daga wani bahaushe gami da rubutashi da romanci (boko) amma abin bai fito ga duniya har mun riske shi ba. Amma dai mafi daɗewar rubutun boko da aka samu shine wanda Marubuci Ibrahim Yaro Yahaya (Allah yajikansa da rahama) ya kawo a shafi na 74 na littafinsa mai suna 'Hausa A Rubuce..' inda yakecewa "Watakila za'ayi mamaki aji cewa a kasar Denmark ta turai aka fara samun an rubuta kalmomin hausa acikin rubutun boko tun a karni na goma shatakwas. Yadda abin yafaru shine a cikin shekarar 1772 sarkin Denmark ya tura wakilansa izuwa Arabiya don gudanar da bincike na kimiyya. Acikin wakilan harda wani mai suna B.G Neibuhr, wanda shine kadai ya tsira kuma har ya koma gida kasarsa. To a wannan shekarar sai wani balaraben Tunis yaje Denmark ziyara, sunan sa Abdurrahman, a tare dashi akwai wani bawansa Bahaushe. Sai sarkin Denmark yasa aka kira Niebuhr domin ya zama tafinta tsakanin sa da balaraben nan kasancewar shi Niebuhr ya koyi larabci a tafiyar da yayi izuwa Arabia. To a wannan gamin ne har abota ta-kullu tsakanin Niebuhr da Abdurrahman, har kuma Niebuhr yayi sha'awar koyon Barbarci da Hausa daga wannan Bawa. Anan ya dukufa yana koyo, ana faɗa masa kalmomi yana rubutawa.
Ga wasu kalmomi da aka samu Niebuhr ya rubuta a hausar boko kamar yadda yaji daga bakin wannan bawa bahaushe.
Dudsji. Dutse
Ghaui. Gari
Dsjenari. Zinari
Ghurasa. Gurasa
Crua. Ruwa
Sirki. Sarki
Schensali. Shaidani
Berni. Birni
Na baya daga wannan kuma shine rubuce-rubucen da baturen Mishan mai suna J.F Schon yayi da hausa a wuraren 1856 lokacin daya roki Dr. Barth ya bashi aron Yaransa biyu Dorugu da Abega don su taimaka masa wajen yin rubututtukan hausa.
A wancan lokacin ne Dorugu ya rinka faɗar labarun hausa, shikuma yana rubutawa, har aka samu cewa J. F Schon din ya rubuta litttattafai misalin Magana Hausa, Letafin Musa na fari, Labari Nagari, Dictionary of the Hausa da sauransu.
BUNKASAR RUBUTUN BOKO
Amma dai idan muka dawo maganar asalin soma rubuta hausa da boko irin wadda har yau muke amfani da ita, to zaifi kyau mu koma kan maganar mu ta sama cewa turawan mulkin mallaka ne suka assasa tare da tabbatar mana da ita.
Farfesa Mahdi Adamu ya tabbatar mana da hakan a shafi na 55 na littafinsa mai suna 'The Hausa factor In West African History'. Kuma ga kadan daga abinda yace :- Karatu da rubutu ta hanyar boko ya samu ga hausawa ne a farkon karni na 20. Saboda a shekarar 1900AD ne gwamnatin Ingila ta karɓe ragamar mulki daga hannun sarakunan hausawa, amma sai a 1903 sojojin Gwamna Lugga suka cinye Kano da Sakkwato a yaki, sannan suka buɗe makaranta ta farko a sokoto tare da malamai biyu watau Mr. Kurdan da mataimakinsa Malam Ibrahim, amma makarantar bata daɗe ba saboda iyaye sunki sanya 'ya'yansu don gudun kada acusa musu akidar kiristanci.
Farfesa ya nuna cawa rashin gamsuwar hausawa ga ilimin da turawa suke shirin basu daɗaɗɗen abune, kuma tun a wancan zamanin kalmar 'Boko' ta samo asali wadda acewarsa ma'anar ta da hausa shine kamar ace 'rufe kura da fatar akuya'.l (Watau ayi basaja wajen rufe wani abu da wani abu).
Tun kafin wannan ma, shi kanshi Lugga sai daya kalli Hausawa da yadda sukayi riko da addini tun a lokacin, sannan yayi amannar cewa bai yiwuwa ace za'a koyar dasu boko kamar yadda ake koyar dashi a kasarsu Ingila.
A wani zancrn kuma, cewa akayi tun sa'ar da Lugga yake yaki a kasar nan ya fara sanyawa ana rubuta hausa ta hanyar amfani da rubutun romawa (boko). Saboda kamar yadda muka faɗa tun a baya, Lugga ya fahimci tasiri da bunkasar yaren hausa a wannan yanki na arewa, amma kuma a wurinsa bai yiwuwa ya rubuta hausa da ajami kamar yadda ya samu hausawan lokacin sunayi. Dalilan yin hakan suna da yawa, daga ciki akwai fadin cewa idan za'a rubuta hausa da ajami, sai an koyi yare biyu maimakon ɗaya, watau sai an koyi hausa, sannan kuma an koyi larabci. Amma watakila babban dalilin yafi ga kiyayyar su ga larabawa ko kuma ace kiyayyarsu ga musulunci (kamar yadda babban dalilin kin jinin boko daga hausawa shine kiyayyarsu da kiristanci tunda watakila da ace musulmai ne suka kawo ilimin zamani kasar hausa da ba'ayi burtu da iyaye wajen su sanya 'ya'yansu ba).
Akwai wani abu ma da ba sai an ɓoye ba. Lugga ya faɗa cewa baya ganin rashin sanya musulmai a cikin sojojinsa a matsayin siyasa, amma a zahiri siyasar ne. Tunda dai kusan ɗaukacin Sojojin nasa ba musulmai bane, mutane ne gwarawa da sauran kabilu marasa addini wadanda suke adawa da musulunci, waɗanda kuma yawa-yawansu suna da matsala da musulmai tun a lokacin jihadi, don haka suna zucci-zuccin karya daulolin da musulmai suka kafa domin ɗaukar fansa.
A ɗaya ɓangaren kuma, akwai kwatankwacin wannan kiyayyar a zukatan hausawa, kuma tana daga manyan dalilan da yasa hausawa suka kyamaci ilimin boko. Tunda ilimin yazo ne daga waɗanda suke gani a matsayin makiyansu. Shiyasa sai da aka sha-burtu aka soma sanya yara a makarantun zamani a wancan lokacin, koda yake har izuwa yanzu (kusan shekaru 114 kenan) wasu daga cikin mu hausawa na kallon ilimin boko a matsayin haramtaccen abu kuma gurɓatacce.
Ai a zahirin yakin da turawa sukayi a zamanin mulkin mallaka da 'yan kasa akayi, domin mafi yawan dakarunsu 'yan kasa ne bakaken fata, tunda turawa ba yawa garesu ba a rundunonin, hasali ma wannan yanki namu kamar makabarta ya zamewa turawa saboda yawaitar cututtuka dake musu lahani a yankin.
Shi kuwa rubutun Ajami, turawa da waɗanda ba musulmai ba na ɗaukarsa a matsayin rubutu ne na Larabci kuma na musulunci, daman kuwa da tun da jimawa turawa da larabawa ba wata ɗasawa suke ta azo agani ba musamman ma saboda banbancin addini. Idan kuma ba haka ba, to zamu iya cewa baya daga cikin manufar turawa a zuwan su wannan yanki su inganta addinin Islama tunda a nasu ganin rubutun ajami na musulunci ne. Dalili kenan da ba zasu yadda suyi aiki da rubutun ajami ba ballantana har su inganta shi.
Don haka akace babbar sadarwar da sojojin Lugga sukafi fahimta daga gareshi shine rashin sonsa ga musulunci. A zahiri, ban jin an taɓa ruwaito wata kalma ta ɓatanci da Lugga yayiwa Islama, amma a baɗini, ayyukansa nason ganin ya haɓaka addinin sane tare da cika umarnin kasarsa. Shiyasa kuma sojojinsa sukafi kaunar kome za'a rubuta musu, a rubuta musu shi da yaren hausa, yaren da sukafi sha'awar yarawa sama da nasu, amma kuma cikin haruffan sabuwar wayewa da turawa kuma kiristocin mulkin mallaka suka kawo, watau romanci.
Bayan anci kano da sokoto da yaki, sai Gwamna Lugga ya sa akayi masa hasashen ɗaliban dake makarantun allo a wannan yanki, inda kintace yanuna cewa akwai misalin makarantun Allo da ake karantar da Addinin musulunci cikin rubutun arabi da ajami kusan dubu 25, sannan ɗaliban dake cikin makarantun sun tasamma dubu 250. Wannan tasa Lugga fahimtar Cewa akwai aiki ja agabansa, amma dai ance da taimakonsa aka kafa makarantar mishan a Bidda a cikin shekara ta 1904, inda aka fara koyawa wasu mutane ciki harda tsirarun musulmai rubutun hausar boko, gami da harshen turanci. Ance ana koyar da daliban ne cikin harsunan mu na gida, watau hausa da nufanci.
Gwamna Lugga ya sanar da Ingila yunkurin daya fara na juya rubutun ajami izuwa haruffan Rumawa (Boko) kamar yadda aka samu a kundin takardun dayasha turawa izuwa ingila (Annual Report, Northern Nigeria no. 476, 1903, 332-3)
NASARAR RUBUTUN BOKO KAN AJAMI

No comments:
Post a Comment