MANYAN ABUBUWA MASU TABBATAR DA WANZUWAR UBANGIJI
SADIQ TUKUR GWARZO
Kamar yadda wasu masana ke faɗawa duniya, a yanzu lokaci yayi da za a fara yiwa al'umma baje kolin manyan hujjoji gami da misalai waɗanda ke nuni da wanzuwar sa Allah madaukakin sarki, babu buƙatar ka ce da mutum "kayi imani kurum", a maimakon haka, sai ka faɗa masa hujjoji, in yaso sai ya yi tunani da kwakwalwarsa.
Izuwa yanzu, duk duniya, babu wanda ya ke musun cewa mota da babur, wayoyin sadarwa da kwamfutoci sune sukayi kansu, amma da yawa daga cikin al'ummar duniya suna shakkun cewa akwai wani Sarki wanda ya ƙagi duniya, akwai mala'iku, akwai aljanna da wuta, sannan akwai rayuwa bayan mutuwa..
Ga wadansu daga cikin dubban abubuwan mamaki, wadanda suke tabbatar da wanzuwar Allah maɗaukaki.
1. DUNIYAR MU
Kasancewar Rana na ɗaya daga cikin taurari wadanda aka ƙiyasta adadinsu a sararin samaniya yakai biliyan sau biliyan, tana zagaye da duniyoyi guda tara ko kuma takwas, masu juyawa akan kansu, masu kuma zagaya ta. A ciki har da duniyar da muke rayuwa acikinta.
Da fari dai, yanayin duniyar kanta yana cike da mamaki, domin an tsara shine dai-dai da jikkunan mutane, akwai sanyi amma ba sanyi ƙarara ba, akwai zafi amma ba zafi na sosai ba. Wannan yanayin na ta kuwa shine dai-dai da yanayin da ɗan adam ke buƙata wajen cigaba da rayuwa, canzawar yanayin dai-dai yake da kawo ƙarshen wanzuwar sa. A misali, idan Rana zata matso daf da duniyar mu, ko kuma duniyar mu ta matsa kafada-da-kafada da Rana, da tabbas duk abinda ke cikin wannan duniyar sai ya ƙone ƙurmus, haka kuma idan da ace duniyar mu zata ƙara matsawa can nesa da inda take a yanzu, da tabbas komi na cikinta sai ya daskare.
Tun da ɗan adam ya soma rayuwa izuwa yau, babu wanda ya taɓa ji ko ya gani da idon sa irin wannan sauyawar ta faru, ba kamar abinda ke aukuwa ba ga jirgin sama ko sauran na'urorin da mutum ya ƙera wadanda suke yawan gamuwa da 'Technical errors' kuskuren masarrafai, wannan na nuni da cewa akwai wanda ya qadarto rayuwar mutanen dake wannan duniyar da ita kanta duniyar, yake kuma kula da kasancewar ta a inda take domin cigaba da wanzuwar halittun cikin ta. Kallon waɗannan abubuwa kadai ya isa mutum ya gamsu akwai Allah.
2. ƘWAƘWALWAR ƊAN ADAM
Shin kunsan ƙarfin aikin ƙwaƙwalwar ɗan Adam kuwa?
Itace fa ke shigar da duk wani bayani dake tattare damu da wanda yake zagaye damu. Misali, aikin ƙwaƙwalwa ne ta rarrabe maka abubuwa, kamar sunan su, girman su, matsayin su, kalolin su, manufar su, darajarsu da duk wani abu dake tattare dasu. Itace ke sanar da yanayi wanda ya hadar da sanyi, zafi ko matsakaici. Ita ke sanar da kai duk wani hali da kai kanka kake ciki. Itace ke gudanar da manyan ayyuka na cigaban rayuwar ka, kamar numfashi, isar da jini, isar da abinci, motsi, da sauransu.
Hasashen masana ya nuna cewa aduk daƙiƙa daya, ƙwaƙwalwa na tatsa da warwarar bayanai sama da miliyan daya. Gaga cikin su ne take rarrabe masu amfani da marasa amfani, sannan ta tsara yadda ya kamata a tafiyar dasu ba tare da ɓata lokaci ba duk acikin mafi ƙanƙantar lokaci. Wannan gagarumin abin mamaki dake tattare da ƙwaƙwalwa ya sa shakku a zukatan waɗanda basu gamsu da wanzuwar Allah ba, domin tambayar su akayi da cewa "Ta yaya za a ce Na'urar kwamfuta wadda ba ta taka kara ta karya ba wajen abin mamaki idan aka haɗa ta da ƙwaƙwalwar dan adam za a ce wani ne ya yi ta, amma kuma ita ƙwaƙwalwar za a ce itace ta yi kanta?"
3. TSARIN MAƊAUKAKIYAR DUNIYA (Universe)
Masana kimiyyar duniya duk sun haɗu akan cewa maɗaukakiyar duniya ta faro ne daga fashewar wani babban ƙwanso (Big Bang). Wannan kuma shine asalin duk wani abu wanzajje a duniya baki daya, shine asalin wanzuwar taurari da duniyoyin su da ma nisan dake tsakanin su, shine kuma asalin farawar lokaci.
Wani masani, Robert Jastrow yace "Wannan tarwatsewa itace mafarin duk wani abu da suka haɗar da taurari, duniyoyi, halittu masu rai da marasa rai. Ada can, madaukakiyar duniya tana cure ne a guri ɗaya, daga baya sai ta fashe, har yanzu kuma bamu san asalin abinda ya fasa ta ba"
Wani masanin kuma Steven Weinberg yace "a wannan lokacin da madaukakiyar duniya ta fashe, zafin da take ƙunshe dashi yakai misalin miliyon dubu dari a ma'aunin selshiyos, kuma duniyar cike take da haske".
Abin nufi dai, ada can babu rayuwa, babu duniyoyi da taurari, babu duhu, babu sanyi, lokaci kuma a tsaye yake cak. Fashewar madaukakiyar duniya shine ya samar da duk waɗannan abubuwa. Abin tambayar anan shine, menene ya wanzar da su alhalin a kimiyance mun san cewa tunanin motsi na farko da Newton ya kawo (Newton's first law of motion) ya tabbatar da cewa duk wani abu da babu shi, bazai taɓa wanzuwa ba har sai an wanzar dashi, haka kuma duk wani abu da yake wanzajje, zai cigaba da wanzuwa har lokacin da wani abu ya cire wanzuwar tashi?
4. RASHIN LAFIYA
Masanan kimiyyar dan Adam sun fara nuna gazawarsu a wasu fannoni na cututtuka masu damun ɗan Adam. Uba ga fannin likitoci wato Hippocrates, yayi imanin da cewa jiki yana da ikon warkar da kansa daga duk wata lalura, har yake cewa "magani yana taimakawa ne kurum wajen saurin warkar da lalura"
Eben Alexander ya tabbatar da wanzuwar Aljanna da kuma wanzuwar Allah a cikin littafinsa mai suna 'Proof to Heaven'. Shi dai Eben, ya kasance ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa, wanda kuma ya kamu da dogon suma har malikitoci suka fara cire rai da rayuwarsa, suka kuma fadawa iyalansa cewa "ko da dan uwanku zai rayu, tilas ne yayi fama da lalurar mutuwar ƙwaƙwalwa na tsawon rayuwarsa". Amma abin mamaki, daga baya sai ga shi ya warke, komai nasa ya dawo, sannan da kansa ya tabbatar da cewa ya tsinci kansa ne a wani yanayi kamar ba a wannan duniyar ba, tamkar dai tafiya yayi tsakanin duniya zuwa duniya, don haka ya gamsu da cewa akwai wata rayuwa bayan mutuwa.
Itama wata marar lafiya Maryam Ali wadda tasha fama da ciwon daji (cancer), cewa tayi "nayi imanin Allah ke warkar da duk wata lalura". Sannan ta ƙara da cewa "a lokacin da cutar kansa ta kamani, likitoci sunyi bakin iyawar su, har ma sun faɗawa iyaye na cewa babu tabbas na rayu, amma dana nemi taimakon ubangiji, sai gashi na warke, kuma ina rayuwa".
5. WANZUWA A FALSAFANCE
Wani farfesa daga cikin waɗanda basu gamsu da wanzuwar Allah ba ya taɓa shaidawa dalibansa hujjojinsa dake nuni da cewa komai ka gani a wannan duniyar, yanayi ne kurum yayi shi, babu wani abu mai suna Ubangiji, don haka babu tashin alƙiyama, aljanna da wuta duk ƙarya ce. A cewar sa "kawai ana tsoratar da al'umma ne domin a sanya su su bi wata hanya da za'a mulkesu anan duniya".
Manyan hujjojin nasa sune; ba a ganin Allah, ba'a taɓa shi, ba'a jinsa ko shaƙarsa, don haka tabbas babu shi.
Sai wani ɗalibin sa yace "indai don haka ne yasa farfesa yake ikirarin babu Allah, to yana da hujjar da zata ƙaryata hakan".
Shine fa farfesa cikin zumudi yace "yi maza kawo mana hujjar taka".
Sai Dalibi yace" a yanzu kenan zamu iya cewa farfesa bashi da hankali, domin ni dai bana ganin hankalinsa, bazan iya taɓa shi ba, ba kuma najin ƙamshin sa.. Idan kuwa har kowa ya amince farfesa yana da hankali, hankalin da kuma ba'a taɓashi, ba'a ganin sa, ba kuma a shaƙar sa ko sauraren sa, to banga dalilin da zaisa aƙi amincewa akwai Allah ba, domin duk tsarin daya ne". Tilas farfesa yayi turus, ƙaramin dalibi ya fishi hujja.
A ƙarshe, Bayanai na nan masu nuni da cewa ba lalle sai kana ganin abu wanzuwarsa take kasancewa ba, sannan a falsafance, an hadu akan cewa duk abinda kake iƙirarin babu shi, wannan iƙirarin naka yana tabbatar da wanzuwar sa ne.
Har masanan ke cewa "kome daka gani, yana da sila. Ada can babu duniya, kuma babu rayuwa har sai da sila ta samar da su, wanzuwar silar kuwa ita ke nuni da wanzuwar Allah".
Anan zan tsaya ba domin hujjoji da misalai sun ƙare ba. ALHAMDULLAH. AMANTU BILLAHI WA RUSULIHI.
Allah ya bamu dacewa amin.
No comments:
Post a Comment