Monday, 11 December 2017

TARIHIN KAFUWAR GARIN KABO

TARIHIN KAFUWAR GARIN KABO
Daga Sadiq Tukur Gwarzo
Marubuci Ibrahim Bala Gwarzo, ya ruwaito cewa asalin waɗanda suka fara zama a garin Kabo fulani ne jinsin Rahazawa, sunzo ne daga wani gari mai suna Korami ta kasar Borno.
Yaki ne silar tasowar su daga garin izuwa yankin kano, inda bisa sahalewar sarkin Kano na wannan lokaci yace ya sahale musu su zauna a kasar sa duk inda sukeso matsawar ba zasu kawo hargitsi ba.
Ance wani mai suna Muhammadu Nakiyare shine shugaban tawagar, sai mai musu jagora sunansa Ibrahim Allah-koro, sai sukayo yamma maso kudu da birnin kano suka sauka a wani wuri mai suna Kaci-kura, daga baya aka sauyawa wurin suna da Korami.
Bayan wani lokaci sai mutanen bisa haɗin guiwar Sarkin Baka Abubakar na Baskore, da Sarkin Ɓbaka Musa na 'Yandabino suka yiwa wannan masauki nasu ganuwa domin kuɓuta daga mahara.
Ance wani ɗan fulani daga cikinsu ne yana kiwo ya lura da wani wuri da tsuntsaye keta shawagi, inda da yabi sawunsu sai ya tarar da kududdufi ne da kuma dogayen bishiyoyi a wurin, hakan tasa ya shaidawa yanuwansa tare da komowa wurin da zama. Daga baya suka sanyawa sunan sabon wurin zamansu Kabo..

No comments:

Post a Comment