TARIHIN ATTAJIRI NA DAYA A DUNIYA BILL GATES; KYAUTA BATA HANA ARZIQI.
Tare da Sadiq Tukur Gwarzo.
Cikakken sunan sa shine william Henry 'Bill Gates' III. An haifeshi a ranar 28 ga watan oktoba na shekarar 1955 a wani fari mai suna 'seatle' wanda yake qarqashin birnin washington DC dake qasar Amurka.
Mahaifin Bill Gates Lauya ne, mahaifiyar sa kuma malamar makaranta. Don haka tun yana qarami ya iya rubutu da karatu. A wannan lokacin kuma ya fara karatun jaridu, har sha'awar kafa kamfani ya shiga ransa.
Bill Gates yana dan shekaru 13 ya soma ido biyu da na'urar kwamfuta. Makarantar da yake karatu ce ta siyo ta. Dalibai na biyan kudi suyi amfani da ita na wani qayyadajjen lokaci. Bill Gates ma sai ya biya nasa kudin, aka bashi lokacin amfani da ita. Sai dai lokacin na qarewa, yayiwa kwamfutar wayo (daga nan ya fara hacking), akan dole ta bashi damar cigaba da amfanuwa da ita a kyauta. Amma da akai rashin sa'a makarantar ta gano haka, sai ta koreshi.
Abu nagaba shine, Bill Gates ya samu damar shiga jami'ar Harvard bayan ya ci maki sosai a jarrabawar share fage. Ance maki 1600 ne qurewa a jarabawar mai suna SAT, amma sai gashi Bill Gates ya ciyo maki 1590, watau goma kurum ya fadi. Alokacin bai ma san me zai karanta ba.. Wata rana yana karatun jarida sai ya hango tallar wani sabon kamfanin qere-qere. Nan take ya dauki lambar su ya kirasu. Yace yana musu tallar wata masarrafa (programme) idan zasu iya. Sai kuwa suka ce suna so. Alhali kuma bashi da masarrafar.
Daga nan sai Bill ya nemo abokinsa Paul domin su rubuta masarrafar. Haka suka rinqa amfani da kwamfutocin jami'ar Harvard ba dare ba rana, da kyar suka rubuta ta.
Da suka kammala, sai Bill ya sanyawa masarrafar suna BASIC, ya dauke ta ya nufi Mexico don karbo kudinta. Anan aka biyashi kudi Dala dubu uku, amma da sharadin yana da ikon qara siyar wa wasu. Sai dai ina son kusani, Bill gates bai kammala jami'ar Harvard ba, ba kuma don ya kasance daqiqi bane, sai dai kawai saboda karatun baya qayatar dashi, kwamfuta ita ke burgeshi.
Shekaru biyar bayan haka sai ga kamfanin IBM ya gurfana a gaban Bill, suna son ya rubuta musu masarrafa. Kasancewar 'basic' bai gamsar dasu ba, sai ya shiga cigiya, har ya samo 'DOS' a hannun wani. Ya biyashi kudin sa, shi kuma ya siyar musu dashi.
Daga nan sai Steve Jobs (wanda ya qirqiri kamfanin apple) yazo. Shima ya nemi Bill Gates ya qirqiro sabbin masarrafai irinsu 'MS word' wadanda suka fi nada. Daga baya dai gayyar tasu ta watse. Amma dai Bill ya saci dabarun Steve jobs, da sune kuma ya qirqiri masarrafar 'windows'.
Bill Gates ya shiga kogin tunani akan abubuwan daya kamata a sanyawa kwamfuta don amfanuwar mutum a gida da ofis. Duk ya tattara abubuwan ya cusa su a wata masarrafa. Sai ya sanya mata suna 'windows'.
Daga nan ya fara siyar da masarrafar a kasuwa. Ance Bill gates tun yana matashin sa a jami'ar Harvar yake shaidawa Furofesoshi malamansa cewa zai tsaya a gaban su yana matsayin babban attajiri a dai-dai sa'ar da zai cika shekaru talatin, sai dai burinsa na zamowa attajiri ya samu ne a lokacin daya cika shekaru talatin da daya.
Cinikayyar Masarrafar windows ne ya bashi damar zamowa attajiri. Da kadan da kadan ne ya zamo attajiri na daya a sahun attajiran duniya alkacin yana da misalin shekaru 39.
Daga nan kuma ya shiga kyautar da dukiyar sa baji ba gani. Ya kafa gidauniya mai suna 'Bill and Melinda foundation' wanda suke gudanarwa dashi da matarsa, da kuma amininsa attajiri Warren Buffet. Gidauniyar da take daukar nauyin karatun dalibai sama da 5000 duk shekara. Take gina manyan dakunan gwaji na kimiyya a makarantu. Take kuma biyan kudin bincike tare da bada kudin magani na manyan cututtuka da suka addabi duniya domin a rarrabasu kyauta.
A shekarar 2010, Bill Gates ya raba dukiyar sa biyu ya bayar da rabi da niyyar tallafawa marasa shi. Don haka sai aka daina jin duriyar sa a sahun attajirai. Amma abin mamakin shine, a wannan shekarar ta 2016, ninkin dukiyar daya bayar kyauta guda biyu ne ya koma gareshi. Kuma qididdiga ta nuna cewar yafi kowa arziki a duniya.
A yanzu haka Bill Gate ya sanya hannu a wata yarjejejiya cewa duk sa'ar daya mutu, a sadakar da kashi cassa'in da biyar na dukiyar sa. A baiwa iyalansa ragowar kaso biyar din dayayi saura. Har yake cewa yayi imanin wadannan kudin zasu ishi 'yan nasa guda uku rayuwa mai inganci, tunda ya basu ilimi mai kyau.
Wani lissafi da akayi, ya nuna cewar a duk daqiqa, kudin dake shiga aljihun Attajiri Bill Gates sun tasamma dala 250, a mintuna daya kuma dala 15000 ke shiga. Dai-dai kenan da naira dubu hamsin a duk Sakan din agogo, kuma naira miliyan uku a duk minti daya.
Manzon Allah (s.a.w) yayi gaskiya da yace kyauta ke kara arziki. Hadisi ya tabbatar da cewa a kullum akwai mala'ikan da yake roqon Allah Ta'ala yaninka dukiya ga dukkan mai kyauta ya kuma yi hani da dukkan mara yinta.
Allah yasa mu dace amin
Dg #SadiqTukurGwarzo

No comments:
Post a Comment