Sunday, 10 December 2017

LABARIN BAWA DORUGU 5

LABARIN BAWA DORUGU: BAHAUSHEN DAYA FARA ZAGA TURAI

Kashi na biyar
Daga Sadiq Tukur Gwarzo

Dorugu yaci gaba da cewa "Yaronnan yace kaga baturen nan? Shine za'a bashi kai garesa". Nace a zuciya ta ni kuwa wanne laifi nayi da za'a baisheni ga bature? Yaron nan ya kara da cewa "idan kaga baturen nan ya zago, ka tafi cikin daji kada ka dawo sai da marece". Ni kuwa ban kula ba da abinda yake nufi ba.
Watarana Baturen nan ya zago, ga ubangijina yana nan, damu da sauran bayi duka mun taru kusa dasu. Sai ubangijina ya kirawo ni, Baturen nan ya dubi idona da harshena da hannuna, ya duba Kafata duka. Daya tabbatar ya ganeni, sai maigida da bature suka cikagaba da maganansu, nidai ban san abinda suke cewa ba. Daga nan sai bature yahau bisa doki, suka ce mini na bishi mu tafi. Nace musu "don me?" Sukace mini da hausa "ka tafi ka kawo itace daga cikin gidansa" nace musu "kuna fadin qaryane, na sani kun sayar sheni".
Nabi Baturen nan ko ince sabon ubangijina har muka shiga cikin birni, muka isa ga cikin gidansa, ya kaini ga matarsa. Matarsa ta ganeni, ya kira wata baiwarsa da take maganar hausa, yace mata "ki tambayeshi daga ina ya fito?" nace mata daga qasar hausa bayan data tambayeni. Baiwar nan ta kaini inda suke cin tuwo, sannan ta tambayeni labari na, nikuwa na fada mata shi duka, ashe tana tsammanin ni dantane saboda irin abinda ya sameni ne ya sameta, a yanzu haka yaranta sun fantsama a duniya suna bauta kamar yadda takeyi a gidan bature. A iya zamana a wannan gidan, babu abinda nake sai dai a aikemu da sauran bayi zuwa daji dauko ciyawa ko itace.
Sai dai watarana Bature ya tambayeni ko zanje wani gari mai suna Konu siyar da dokinsa? Nace masa "a'a, ni bawa ina zan iya tafiya sayar da doki? Ai sai a saidani ba doki ba". Ba'a jimaba sai wani bako ya zago gidan, sunan sa ibrahimu, yace da bature ko zai bari su tafi dani konu? Sai dai ni ban jinsu sosai, tunda banjin borno da yaren bature sosai.
Bature ya amince da haka, ibrahimu ya wuce gaba na bishi a baya. Ashe shima bara ne, wani bature ne ubangidansa, sunan sa Tebib. Da muka shiga gidan Tebib da dare, naga an shirya kayan tafiya duka. Muna zama a gidan naga wani dogon mutum ya fito, fuskarsa da hannunsa duka fari kamar takarda, da jar tagiya bisa kansa, gashi da tsawon gemu da farar riga, yana kallona duk sai na tsorata kaman zashi cinyeni. (Wannan farin mutumi ba kowa bane sai Dr Barth)
Akwai wani mutumi, sunan sa Yamadugana da borno, da hausa 'Muhammadu karami' kenan, yana yin hausa kamar ruwa, ya tambayeni ko inason tafiya konu dasu akan rakumin ubangijina? Sunce akwai dabino da yawa acan, suna tsammanin idan sunce haka zanyi dokin zuwa. Nace banson zuwa. Suka lallameni ala tilas muka tafi. Da gari ya waye Suka bani igiya inja rakuma, muka fita daga cikin gari muka shiga daji.
MUN TAFI YAKI
Da muka shiga daji sai sabon ubangijina Tebib yayi sha'awar yin farauta. Ina kallo yasa wani karfe mai tsawo acikin bindiga, muna tafiya sannu-sannu sai ya hango tsuntsuwa, sai kuwa ya harbota ta fado kasa. Ya kirani "barka, barka", nayi gudu na dauki tsuntsuwa amma na rasa karfen dayasa a cikin bindigar. Na dauka na kaiwa baransa ibrahim don ya dafa. Da aka dafa aka kawo masa, sukaci tare da wani kamarsa, sunan sa Abdulkarim, muka kwana a wani daji, da safe muka isa wani gari sunan sa 'Yawu'.
Muka kwana uku ko hudu daga nan. Yawu garine dake kusa da ruwa. Suna da kifi da yawa mai dadi kuwa, suna kama kifi da taru. Idan zasu shiga ruwa suna da gora manya-manya da sanda karama a tare dasu. Idan sun kama kifi babba saisu doke kansa da sandar. Anan muka zauna har mukayi abokai masu tafiya Konu.
Muka ketare gulbi tare dasu muka isa ga konu. Mutanen konu suka tarbemu, suka gaishemu, sannan suka koma gidajensu. Da marece yayi sarki ya aiko mana da nonon taguwa muka sha muka koshi muka ci dabino, muka baiwa dawaki sauran nonon da ciyawa suka ci.
Mutanen konu basu zama wuri daya, idan suka kwana anan anjima saisu tashi su tafi wani garin su shiga. Nonon taguwa ne abincinsu. Da muka zauna naji mutanen garin nason zuwa yaki da mutanen wani gari kusa da Tubo. Sunce tafiyan kwana daya ne daga konu. Sukayi shiri, basu dauki komai ba akan rakumansu, sai jakka wadda babu komai aciki.
Akwai kaya bisa garesu da lema da kuma abinci acikin kayan. Muka tafi tare da mutanen konu har dare yayi, amma bamu hura wuta ba don kada abokan adawa su gano wuta da dare. Da gari ya waye muka tashi, nahau bisa rakumi ina sukuwa tare da wani yaro har na gaji na sauko kasa, su kuma mutanen dake bisa dawaki suka shige zuwa fada suka barmu a baya.
A wannan yakin sun samo dukiya. Wadansu sun kama bayi, da shanu da awaki. Suka dawo garemu. Sannan muka nufi wani garin kuma. Da mukaje sai muka ga garin nada girma. Ubangijina da abokansa dani muka tsaya, sukuma suka karasa ga garin. Ga kuma mutanen garin duk sun firfito waje suna hango mu. Tsammanina sunji labarin fada zamuyi dasu. Sai mutanen konu da muke tare dasu suka ce musu bamu yin fada da garinku
Sai mutanen garin suka koma cikin garinsu, amma fa sunfi mutanen mu wayo. Su kuma mutanen mu sai suka dawo suka samemu mu shidda. Muka zauna yini guda duka anan. Tebib da Abdulkarim suka sha gahawarsu a karkashin inuwar kalgo, mukuwa mukaci dabino. Mutanen birnin nan kuwa sun boye matansu da 'ya'yansu da shanunsu da dukiyarsu duka a cikin rukuki, sai maza ne kurum acikin gari, kuma sukaki bacci suna jiran suji motsi...
A daren nan mutanen mu suka daura sirsi, kowa ya cika bindigarsa. Suka nufi garin don gwabza fada. Fada ya rincabe musu. Dushin bindiga yana wucewa kiu-kiu a haka har gari ya waye suna yin fada. Daga bisani mutanen garin nan na Tubo suka korasu, da muka gani suna gudu zuwa gurinmu, sai mukace mu gudu sun lorosu. Nahau bisa rakumi, Tebib ya bani karamin sunduki, rakumi na gudu sunduki na jana kasa, sai kuwa na fadi tare da sunduki, kana na tashi inayin gudu da kafa tare da sundukin. Muka hau bisa wani tudu, nan muka tsaya har sauran mutanen konu da muke tare suka karaso garemu, amma fa kayan mu munbarsu a baya.
Da mutanen Tubo suka zagaya inda muka ajiye kayanmu, sai suka kwashe dukiyar da muka bari duka, sun taras da wani mutumi kuma wanda yake tare damu, suka yanke masa gaba da mashi, suka dauke lemar mu. Haka muka zauna yini guda cikin rana. Yakin dana gani kenan.
#sadiqtukurgwarzo

No comments:

Post a Comment